Chapter 11
Chapter 11
ya sanyashi kada kanshi yana ci gaba da jifanta da murmushi "Eh zuciyarki nakeso" cikin mintina qalilan kwanyarta ta hakaito mata abinda yake nufi,wata iriyar kunya da nauyi suka kamata,ta rasa tudun dafaww,saboda haka saita juya gudu gudu sauri sauri ta shige gida,yana tsaya mana amma ina ba zata iya ba,bata taba zaton a shekarunta sha biyar akwai saurayin da zai gaya mata wai yana sonta ba,kalmar tayi mata nauyi da yawa. Murmushin jin dadi ya saki,ya zauna dakalin dake daura da gidansu,abinka da d'an makaranta ba'a rabashi da takarda,sai ya ciro qaramar jotter din dake aljihun wandonshi wanda ya gama duba wani karatu da ita yayi rubutu da basu wuce layi goma ba ya jefa cikin botikin,ya kira yaro ya bashi botikin shi kuma ya wuce. *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGππ½* ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGππ½* ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 0οΈβ£7οΈβ£ Saida umma ta dinga qwala mata kira kan ta fito ta wanke kwanukan ta dauki abincinta taci kada lokacin islamiyya ya wuce sannan ta taso daga rub da cikin da tayi saman katifarta,ta harhada kwanukan ta kada ruwan kumfa ta soma sabesu,tanayi tana tunanin kalmar daya furta mata,ashe kalma ce mai nauyu da dadi haka,lokaci lokaci ta dinga sakin murmushi ita daya,harta zubawa botikin ruwa ta zubda ruwan sai taga takardar,ta tsame hannunta cikin kumfar ta dauki takardar sannan ta bude. Soma fahimta da tayi takardar meye yasa tayi sauri ta shige dakinta,ta samu kebantaccen waje ta budeta inda zata sha iska ta bushe sosai sannan ta dawo taci gaba da wanke wankenta. Kafin ta kammala shirin islamiyyarta saiga qawarta zunnurah ta iso cikin unifoarm din islamiyya "Yauwa,dama banason cin abincin nan ni kadai,don Allah bari na dauko ki tayani" cewar shahida tana nufar kitchen ta fito da kwanon abincinta ta aje a qasa ta zauna dirshan "Sauko malama muci" "Ke nifa a qoshe nake wallahi ba abincin da zan iya ci" "Ni zakima wulaqanci ko?,zaki sake cewa naci abinci a gidanku" tq fada tana saka hannu tayi bismillah ta soma ci zunnurah na mata dariya,wai ita zata cewa tana cin abincin gidansu,matar da nata abincin ma sai ya huce bata ci ba,hira suke jifa jifa shahida nacin abincin tana kuma duba lokaci kada a fito saga sallah a shiga aji basu tafi ba,saidai rabi da rabin hankalinta nakan takardarta dake shan iska "Yauwa shahida....wai waye wanda yake rakoki ne kullum daga wajen sadaka" tsaida lomar da zata saka a bakinta tayi tana duban zunnuran "Au har kin samu labari kema?" Harara ta watsa mata "Uwar labari na samu,waye baya ganinku a tare wai kwana hudu kenan,tunda ansan baki kula kowa...." "K'nnnn...nima ban sanshi ba wallahi zunnurah,acan nake ganinsa" dariya zunnurah ta saki "Qawata nasan halinki sarai,duk yadda akai wannan din na dabanne tunda har kika kasa gwada masa halinki" murmushi ta saka,ita kanta tasan na daban dinne nasai zunnurah ta fada ba,tun kallon farko taji yakai mata ko ina,ganin farko taji wani qaqqarfan lamari dangane dashi,takan iya raba dare tana tunaninsa,kowanne second nata da tunaninsa take rayuwa "Amma fa kinsan shaik hafiz zai shiga wani hali?" Dagowa tayi tana duban zunnurah kafin ta galla mata harara "Kamar yaya?,sonshi nake?,ko ce miki yayi yana sona" nan ta zauna tsaf ta kwashe mata yadda dukkan dalibai suka lura da soyayyar da yake mata,baki ta tabe tana miqewa daga gaban kwanon,don ita dai tasan ko doguwar magana bata hadata dashi bare kuma wani abu daban can,fita tayi ta wanke hannunta ta dawo tana ware gogaggen hijabinta "Qawata baki da mutunci fa,shaik ke kanki kinsan yammatan makaranta rububinsa suke,kuma kema kanki qaryarki kice baki san yana sonki ba,maimakon kiyi murna sainaga ke ko a jikinki labarin bai faranta miki ba ko d'aya" "Don Allah zunnurah ki qyaleni da zancansa,sai....." Maganar tata ta katse jin sallamar fiddausi,yarinyar da tsakanin gidansu shahida da nasu gidan layi biyu ne,tun zuwanta islamiyyarsu shahida takeson qawance da ita,tun shahidan na janyewa harta saki jiki da ita,saboda ta lura yarinyar itama nada hankali,yawan shuru shuru da rashin son hayaniya. Tuni zunnurah ta hade rai,hakanan a duniya taji sam fiddausi bata yi mata ba,ko kadan jininsu ya kasa haduwa,shahida ta rasa dalili,tun tana sharewa har tazo tanawa zunnurah fadan ta daina haka,wulaqanta dan adam babu kyau,yarinyar na sonsu hakanan bata da wata matsala meye abun sha mata qamshi da take "Hakanan wallahi nidai naji batayimin ba" amsar da zunnurah ta baiwa shahida kenan. A tsakar gida fiddausi ta duqa ta gaida umma cikin ladabi,ta amsa ba tare data tsaya ta mata wani cikakken kallo ba taci gaba da sabgoginta(babban kuskure na biyu da ummanta ta sake tafkawa bayan fada da miji gaban 'ya'ya),fiddausi ta shige dakin shahida,cikin fara'a suka gaisa ita da shahida,yayin da xunnurah ta kauda kai ta amsawa fiddausin sama sama,dif zunnurah tayi sai shahidan da fiddausi dake hira sama sama,har shahida ta gama shiryawa suka fice daga gidan. Suna gab da shiga gate din makarantar xunnurah ta kamo hannun shahida tayi baya da ita,duk sai suka tsaya ta hade gira tace da fiddausi "Me kike jira?,magana zamuyi da ita" sum sum fiddausi ta juya ta wuce ciki "Wai me yasa kikeson koyon halin daba naki ba zunnurah me fiddausi tayi miki?" "Shahida,ba haka kawai naji banson yarinyar nan ba,an bani labari fiddausi tana taba shaye shaye..." Rufe bakinta shahida tayi da hannu tana kallon zunnurah gami da zaro ido "Haba zunnurah,haba,zato fa ance zunubi ne,ya zaki jefeta da wannan mummunan kalmar don kawai tana son mu'amala damu?" "Da gaske nake miki shahida,daga bakin namiji na samu wannan labarin,kinsan kuwa su basu fiye munafunci kosa ido ba bare kice,sannan kuma idan zaki lura da kyau zaki ga yanayin fiddausi ba irin namu bane,yawan bacci da kasala kawai alamune na mutum yana taba shaye shaye,zaman kadaici rashin so magana da yawa" zame hannunta shahida tayi daga na zunnurah,don sosai taji babu dadi ta kuma ji ranta ya baci "Duk abinda kika fada zunnurah baki da tabbaci a kanshi,karki fadi abinda zaki jawo a tsaidaki a miki hisabi ran gobe qiyama,ni fiddausi ta gayamin bata da cikakkiyar lafiya,tana da sicklier shi yasa take yawan bacci" kada kai zunnurah tayi "Shikenan shahida tunda baki yadda dani ba,kinfi kowa amma sanin halina,nidai ina baki shawara kibi a hankali,don bazanso abinda zai cutar dake ba" "Babu abinda zai faru in sha Allahu" daga wannan suka rankaya suka shige cikin makarantar. Washegari da wuri taje wajen bada sadaka ba kamar yadda ta saba zuwa ba,hakanan takejin wani nauyi da kunya tunda ta karanta kalaman da yarubuta mata jikin takarda,niyyarta tayi da wuri ta koma gida ba tare daya sameta ba,saidai abinda bata sani ba tuni ya rugata ma zuwa,saboda gaba daya ya rasa nutsuwarshi Allah Allah yake gari ya waye yamma tayi yaje ya ganta,bai taba tsintar kansa cikin irin wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96