Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,289 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Allah ki shuru" ajiyar zuciya dukkansu suka sauke wanda su kansu basu san ta fito sarari ba saida suka hada ido da juna suka tabbatar anwar din yaji sai kuma sukaji kunya,hakan shi ya tabbatarwa da anwar suma zancan na ransu,basason tararsa ko tauyeshi ko tilastashi kan abinda bashi da niyya ko ra'ayi. Wannan abun daya faru sai ya zama kamar wani lasisi nafisa ta samu na nuwa anwar soyayya ko a gaban waye,wanda hakan ya sanya babu shiri ya qara qaimi wajen gyaran gidansa,don yana ganin matyqar yaci gaba da zama a gidansu akwai matsala,don nafisan kaman ta soma fitsare sawayenta,duk da yadda hajiya bilkisu ke taka mata burki amma sam bataji,hudubar mima gani take itace dai dai don itace dai dai da ra'ayinta. Ta dage sosai wajen farauto zuciyarsa,da yake Allah shike sanya soyayya cikin zukatan bayinsa duk irin kulawa da kyautatawar da take masa bai taba jin wani abu mai kama da qaunarta ba cikin zuciyarsa,yana mata kallon qanwa tana kuma da qima a idanunsa darajar mahaifanta da yadda suke sonshi. Shekara biyu cur rayuwar anwar ta sauya,kai baka ce shine wannan anwar din ba,kamanni yanayin rayuwa da komai nashi,saida zuciyar nan na nan,zuciyar dai itace babu wani abu daya sauyata,a sannan alhj abba ya shirya bikin yaye wasu daga ma'aikatansa wanda su suka buqaci haka don suci gashin kansu,ciki harda anwar wanda tun dacan dama bai sha'awar zama qarqashin wani,yafison duk wahala yaci gashin kansa,a lokacin da alhj abba ya yayesu ya danqawa kowanne kudin sallama,saidai kudin anwar yafi na kowa yawa,ya zauna da alhj abban ya gaya masa zai amsa ya qara cikin kudadensa,amma in sha Allahu zai dawo da dukka kudin da aka bashi,aljh abba yace sam wannan kudin kyautane kawai saboda bauta da wahalar da suka yiwa kamfani, a nutse anwar ya fahimtar dashi manufarsa,shidai yace yaje kawai ya kafa kanshi din. Komai na rayuwa wato yana da lokacinsa,hakanan rabon kwado bai hawa sama,anwar ya tsaya tsayin daka,babu dare ba rana,babu lokacin bacci bana hutu sai daya tabbatar ya kafu,ya fidda kudin alhj abba ya maida masa,shi kansa alhj abban yayi mamakin yadda anwar din yayi kafuwar da aqalla kayi shekara goma sha bakayi irinta ba,saidai yasan komai yassarewace ta ubangiji,shi kansa anwar yasan cewa qarfin addu'ar iyaye tsayawa kai da fata kan gaskiya da riqe Allah da yayi shi ya kaishi fa wannan matakin,tuni ya tamfatsawa anty usaina gida,saidai a sanda yace ta zabi unguwa saita zabi unguwarsu shahida,farkon layinsu wasu gidaje da suka tashi suka saida,daya tambayeta dalili tace ba ruwansa,ba yadda ya iya haka yayi mata yadda tace tana so,saidai har aka kammala ginin bai taba taka qafarshi unguwar ba,data koma kuma sai zuwan ya zame masa dan zani shima,sai daya sanya aka sake fasa qofa ta bayan layinsu yake shiga ta nan. Ganin lokaci yana ja anwar yaqi soma maganar aurensu babban burin daya rage mata a duniya yasa ta soma masa shagube,qwarai ya fahimta saidai har yanzu baiji nutsuwar zama da nafisa a matsayin matar aurensa ba,duk da ya sani tunda ya furta dole ya cika amma har yanzu zuciyarsa taqi karban hakan,abinda yaketa yaqi akai kenan,ita kuma tasan cewa iyayenta ba zasu taba yi masa batun ba,mutum daya ce nan duniya zata ce yayi ya zame masa dole yayi anty husaina,dalili kenan da yasa ta wanki qafa bisa shawarar mima taje mata da batun,wanda a yanzu haka akan qadamin da suke kai kenan yanzu haka(idan baku manta ba a baya kunji inda anty usainan ke masa maganar kar suji kunya kan nafisan). Ta bangaren shahida ma kwanaki watanni zuwa shekaru sun soma tafiya,tuni ta kammala degree dinta wanda ta samu gamasu da qananun shekarun da kowa ya kalleta sai yayi mamaki,hakanan ta dora da masters shima Allah ya taimaketa ta kammalashi cike da nasara mai tarin yawa,a sanda sakamakonta ya fito uncle hisham yaso ta amshi tayin lacturing da jami'o'i suka yi mata tace sam bata ra'ayi,ya tura takardunta kamfanoni da dama ta samu aiki daga wajensu nanma tace ba zatayi ba ciki harda kamfaninsu,ba yadda ya iya hakanan ya qyaleta. Sanda tazo masa da zancan koyarwa a *NOOR INTERNATIONAL* sai daya cire gilashinsa ya kalleta don ya tabbatar da wasa take koda gaske,hakanan taji kawai bata da burin daya wuce itama yaran talaka su amfana da karatu ilimi da baiwar da Allah ya bata,ba haka yaso ba sam,saboda tayi karatu kai kyai wanda ya dace ta tsaya ta moreshi tayi amfani dashi ta hanyar yin aiki a gurbi da kuma bigiren daya dace,hanatayi kai tsaye yace maida kai baya ne,ta nace ta dage wansa ya sanyashi dole ya amince,amma bisa wasu sharudan. Duk sanda suka mata wani abu da bai gamsheshi ba to ba shakka ta gama koyarwa a makatantar,kai tsaye ta amince don bata ga ma abinda zai gamota dasu ba bare wani abun ya faru,kan wannan sharadin ta soma koyarwa cikin makarantar,ta kuma samu karbuwa daga wajen dalibai har malamai,zama cikin makarantar kuma yayi mata,hakanan yana mata dadi qwarai. Wannan shine labarin taurarinmu guda biyu da abinda ya zama sanadiyyar rabuwarsu ba tare dakowannensu yasan cewa MAQARQASHIYA CE ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Zaman bitar rayuwarsu ita da anwar din data tsaya yi daren jiya ba qaramin taba zuciya ruhi da kuma gangar jikinta yayi ba,tayi kuka irin wanda ta jima ta jefashi kwandon shara tare da yiwa kanta alqawarin ta daina har abada,dalilin daya sanyata makara kenan bata kwanta da wuri ba,hakan ya sanyata bata tashi farkawa ba sai qarfe bakwai na safe,ko sallar asuba ta qwace mata kenan,cikin hanzari ta sauko daga saman gadonta duk da yadda jikinta yake a matuqar mace,hakanan ya mata nauyi tun daga gangar jikinta zuwa kanta. Tana idar da sallar da ake binta tana cikin yin azkar dinta na safiya huda tayi knocking ta turo qofar,ta shirya tsaf cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm dinta,kai kace yau ne zata soma zuwa makarantar,fuskarta qunshe fal da walwala da farinciki,saidai tana ganin alamun shahidan bata shirya ba ta turo baki kaman zatayi kuka "Anty...bakishirya ba,yaune fa?" Murmushi ta saki tana qarashe salatin annbi guda goma da takeyi ta shafa sannan tace "Banajin dadine yau huda" "Amman zaki ko?" Ta tambayeta da sauri cikin fargabar kada tace ba zata samu zuwan ba "Zanje huda...amma inajin zamu makara da yawa fa" qafa ta soma bubbugawa shahidan ta gane me take nufi "Kinga...ki shirya a soma kaiki,idan yaso in ya dawo daga kaiki ni saiya kaini,saimu hadu a hall din hakan yayi?" Kaita kada tana murmushi "Bari naje naci abinci to" ta fadi tana juyawa a guje ta fita a dakin,sai data bacewa ganinta sannan ta dauke kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya,tanajin inama ace itace hudan,quruciya abu ne mai dadi,baka da matsala baka da damuwa,dukka ka tsere musu. A nutse ta cire kayanta ta shige bandaki ta tara ruwan dumi ta soma wanka,saboda yanayin jikin nata da batajin dadinsa yasa komai nata ma cikin nawaa take yinsa,hakan ya sanya ta kashe kusan awa guda a wanka da shiryawa. Ta jima gaban mudubi tana kallon fuskarta kaman yadda ta saba koda yaushe,dukda idanunta sun dan sauya saboda kukan da tayi daren jiya amma sai taga fuskarta tayi wasai,farar affaya mai taushi data nade jikinta ta amsheta qwarai,akwai adon golden jikinta,hakanan taji kaman ta cireta,me yasa ma

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});