Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,312 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fita shahida!. Ki fita nace!" Kai ta kada cikin tashin hankali tanason taji qarshen zancan daya dauko,daga sanda ya ganta me?,ya ganta ne sanda suka tafi siyan syrup?,koko yana tsaye sanda matashin saurayin ya fiddo ta daga motar? "Ba inda zani...kome zaka yimin ba inda zani" bata ankara ba taji ya damqi hannunta,karon farko a tarihin rayuwarsu,bai barta ba saida sukaje soron qarshe bakin qofar gidan sannan ya turata wanda hakan yayi sanadiyyar da tayi taga taga ta kusa faduwa Allah yasa ta turje "Bana sonki shahida" kalmar data hadu da qarar rufe qofar gidan garam da yayi ta bada wata tsawa tsakiyar kanta data sanya komai nata ya tsaya cak na wucin gadi,da taimakon ambaton sunan Allah data soma yi ne ta samu nutsuwarta ta dawo. A hankali ta dinga takawa kamar wadda tasha wani abun,kalaman anwar suka soma amsa kuwwa cikin kunnuwanta,wani irin bushewar zuciya taji,dukkan wani tashin hankali ta nemeshi ta rasa,ba abinda takeji sai kalaman anwar a kunneta,bata ankara ba taji ana "Subhanallahi....sannu...amma bakiji ciwo ba ko?" Sai a sannan ta daga kanta tana duban mutanen dake magana kamar wata doluwa,ashe qatuwar kwalbatin da ake haqawa unguwar ta fada,da qyar da taimakon wasu 'yammata da sukazo wucewa ta samu ta fito sunata mata sannu,taci gaba datakawa ba tare data tsaya duba ciwon data ji ba,burinta kawai ta isa gida,burinta Allah yasa ace mafarki take. Bata tabbatar da cewa komai da gaske yake faruwa ba saida dare ya tsala,taji idanunta tarwai kaman yanzu ta tashi daga baccin wata uku,siya zuciyarta ta dinga yi irin wanda bata tajin irinsa ba,cikin qaramin lokaci qirjinta ya soma ciwo,numfashinta ya dinga fita da qyar,haka ta tsinci kanta har asuba ta risketa,sanda ummanta ke yunqurin tadata tayi sallah a lokacin taga halin da take ciki,basuyi wata wata ba suka wuce da ita asibiti. Gwajin farko likitan yaga jininta yayi mugun hawa,don dab yake da yakai dari biyu,dole suka soma mata allurar bacci kafin sauran treatment su biyo baya,ba qaramin tashin hankali abba da umman suka shiga ba,don duk ga zatonsu iya halin da suka tsundumata ne kawai yayi sanadiyyar faruwar haka,duk da cewa shi dinma ya taka tashi muhimmiyar rawar. Daga bangaren anwar tunda ya maida qofar gidan ya rufe da qyar ya kaishi daki ya zube saman kujerar falon qwalqwalwarsa na daukan zafi,yana maijin ciwo da zafin dukkan wani abu daya faru tun daga kwanaki uku da suka wuce kawo yau,ji yake kaman ya budi idanun yaga mafarki yake,yana jin bugu wanda yasan bazai wuce muhsin ba amma bazai iya tashi ba,bashi da sha'awar ma kowa ya rabeshi,daga bisani wayarshi ta dauki qara,ya qura mata idanu yana kallonta hartayi ta gana ta tsinke,sannan ya miqa hannunshi ya daukota,ba tare daya damu da duba mai kiran ba ya bude bayan wayar ya ciro layin wayar ya karyashi ya watsa tsakar gida sannan ya cilla wayar da batiranta gefe guda,a ranar yadda yaga rana haka yaga dare,dukkan laifukan kuma na wuyan shahida ita ta haifar da komai,haka ya dinga sintiri yana zarya,gaba daya duniyar jinta yake sama ta koma qasa. Da qyar da sudin goshi ya samu bacci yayi awon gaba dashi. Cikin watanni qalilan yaji gaba daya rayuwar ta juya masa baya,baya jin dadin komai,komai ya daina burgeshi,komai kuma ya tsaya masa cak,duk yadda yayi qoqarin moving forward ga aje komai hakan ya gagareshi,dalili na farko da yasa ya tattara dukkan abunda ya danganci shahida wanda idan ya ganshi zai iya tuna mishi da ita ya killace a muhalli daya,duk yadda yaso ga qonasu ko zubarwa hakanan ya kasa,abu na biyu ya aje aikin kamfanin da yake,domin kuwa duk sanda zai tafin saiya tuna mishi da ita,abinda sam ko kusa ko alama baida buqatarsa. Ta bangaren shahida kuwa sanda ta farka kalamansa ne abu na farko da suka soma dawo mata aka,ji ta dinga yi kaman zatayi hauka,ta ina zata iya rayuwar da babu anwar,yadda ta koma din ya sake daga hankalin abba da umma,yayin da tarin damuwa da nadamar abinda suka aikata ya sanya ciwo ya shigi abban,ya dinga fama dashi shi kadai yana cinsa kadan kadan. Abubuwa sai suka taru suka yiwa umman yawa,ga shahida har yau bata gane kanta,ga abbansu ciwo nason kayar dashi,sannu sannu lamuran suka ci gaba da kwabe mata da tafi mata a haka,har zuwa rana mafi muni da tashin hankali a garesu,ranar da ciwo ya yiwa abbansu shahidan farat daya aka tadda gawarsa cikin daki,fadin irin tashin hankalin da suka tsinci kansu ma bata baki ne,shahida kam tunda ta suma bata farfado ba sai datayi kwana biyar,wata iriyar dakiya ta dinga shiganta,ta yadda tabbas wani tashin hankalin baida misali,yadda take jin kanta da rayuwarta ta zama wata mara gane komai,zaqi ko d'aci,baqinciki ko farinciki,murmushi ko kuka,ta koma kamar mutum mutumi,tana jin tamkar ita ta kashe mahaifinta,tana jin alhakin mutuwarsa na bisa wuyanta,abinda ta aikata ba shakka shi ya kashe mata mahaifi,awannan halin anty zubaida ta cimmasu,don dukkan abinda ya farun ya faru ne basa qasar ita da uncle hisham. Kuka umma ta zauna tayi sosai a gabanta,tana fatan ta samu wasu shawarwarin da zasu kawo silar warwarewar matsalarta,bata boyewa anty zubaidan komai ba,labarin dukkan abinda ya biyo bayan yayi masifar girgizata,tana qaunat shahida har cikin ranta,tasan kuma Allah ne ya sallada wannan qaunar a tsakaninsu "Ba shakka kun tafka kura kurai arayuwarku duk da cewa shi tashi ta riga data wuce kaman yadda kika shaidan yabar wasiyyar neman afuwa a gareku gaba daya saidai muyita masa addu'ar samun dacewa,cece kuce ko fada gaban 'ya'ya babu abinda baya haifarwa ku kunga irin naku sakamakon dayazo dashi,daga ciki yana haifar da qiyayyar uwa kota uba,saboda kan yara zai rarrabu,kowa da wanda yake goyawa baya,daga haka zakiga an samu jam'iyyu daban daban,wanda kowanne yaja tinga ne yana taya gwaninsa nashi fadan,walau yana taya uwa ko uba,wannan sai yasa hatta a tsakaninsu 'yan uwan junan ma basa jituwa saboda wani baya ra'ayin bangaren da wani yake,bugu da qari idan da namiji gareku kai uba kana koya mishi ko ya tara iyali haka zai mu'amalanci iyalinsa?,ke uwa kuma kin koyawa diyarki haka akewa miji,illoli ne masu tarin yawa da qalubake kala daban daban,yanzun kunyi silar jefa diyarku ga tafarkin shaye shaye sabida tashin hankalin da take shiga sanda kuke yaqar juna harta gwammace ta zama ko yaushe out of sense yadda ba zatasan meke faruwa cikin ahalinta ba..."dan shuru anty zubaida tayi abun na mata ciwo "Yanzu bazanyi kaffara ba cewa kun korarwa diyarku manemi...saboda halin data fada ya isa kunnenshi...wala'alla abaya yana mata kallon managarciya yanzu ya sameta kan wannan turbar,kowanne namiji burinsa shine zabawa yaransa uwa ta gari kun bata wannan kyakkyawar shaidar daga kan shahida...inajin ciwo...inajin ciwon abinda ya samu shahida...amma nayi alqawari bazan bar rayuwarta ta gurgunta ba" daga haka ta miqe zuwa dakin shahida cikin bacin rai amma kafin ta shiga sai tayi qoqarin dai daita yanayinta sannan ta daga labulen a hankali ta saka kai cikin dakin da babu kowa ciki sai shahidan qwal ita kadai.*Zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata ki tuntubi wannan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣6️⃣ Daga kai tayi ta dubi anty zubaidan maimakon yadda ta saba yi mata a baya duk sanda ta ganta,takan tashu cikin farinciki tana

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});