Chapter 65
Chapter 65
ta sake umman tana dubanta sannan tace "Saikace qanqanuwar yarinya zaki tasani gaba kina kuka?,meye hakan?" Zamowa tayi daga saman kujerar da take kai tayin kneeldown a gaban umman ta kama hannayenta "Don girman Allah umma ki dakatar dasu,ke daya ce burina na qarshe,wallahi umma bana sonshi shima baya sona,ku aura min koma waye umma amma banda anwar?" Idanu ta saka tana kallonta,a iya saninta abinda ya faru tsakaninta da anwar ma laifi nata ne,iya abinda ta saninma baiyi zafin da zata rikice hakan ba harta rasa sukuni da walwala ba,Yayin da khadija wadda shigowarta kenan ta tsinci xancan ta dafe baki gami da zare ido cikin mamaki,har batasan sanda tayi subutar bakin cewa "Yaaya?,ya anwar ne fa?" Daga kai umma tayi tayi mata nuni data fice,haka ta fita cikin dimbin mamaki,ta zaci antyn tata zatayi farinciki da dawowar anwar rayuwarsu fiye da yadda su sukayi,amma ga sabanin hankalinta sai taga ba haka bane sam. A nutse umma ta zuba mata idanu,cikin sanyin murya wanda ke nuna har jikinta ma a sanyaye yake tace "Ashe so kike ki tona mana asiri shahida bayan lullubin sutura da Allah yayi mana?" Ta qarasa maganar wani abu na taba zuciyarta wanda ya bayyana har a muryarta "Shahida ashe baki qaunata?,ashe ba rufin asiri Allah yayi miki ba damu kanmu daya dawo miki da anwar?,meye a zuciyarki shahida?,bakison farincikina ashe da walwalata?"kai shahida ke girgizawa kuka na qwace mata "ba haka bane umma,umma bana sonshi kiyi haquri umma,wallahi banajin sonshi kwata kwata" "Shahida indai nice na haifeki ina....." "A'ah,karki qarasa don Allah umma" sukaji wata murya da sako kanta kenan dakin ta tsinci zancan shahida na qarshe da lafazin umman ta fada,dukkansu suka juya suna kallonta,anty usaina ce,ta qarso inda suke zaune,wajen shahida ta nufa kai tsaye ta kama hannayenta sannan ta zauna gab da ita,hankalin umma yadan tashi kadan don ba zataso shahida tacigaba da magana kan anwar ba,don tana da tabbacin batasan wace ita a wajenshi ba "Idan kika fadi haka kamar kin mata qarfa qarfa ne ai" tana kallon umman tayi maganar,wani sanyi shahida taji cikin ranta,tana fatan Allah yasa zuwan matar ya zame mata haske "Idan kuma tana da hujjarta fa wadda tafi taku qarfi?,ki barta aji hujjarta da dalilanta tukunna". Miqewa umma tayi " bata da wata hujja ko dalili usaina" "A'ah bari naji ta bakinta tukunna" "Koda kinji ta bakinta na riga na yanke matuqar nina haifeta ina bata umarnin auren anwar" daga haka umma ta fice daga dakin tana mamakin wauta da sakarcin da shahidan takeson tafkawa,kamar batasan meya wakana cikin rayuwarta a baya ba,bata taba tsammanin ma anwar zai sake waiwayar shahida yace zai aureta ba sabida abunda idanunshi suka gane masa a zahiri ba labarj,dama tazo mata tanason tayi wasa da ita?,koda taqi anwar din batajin zata samu kamar anwar din,mutumin da tun wancan lokacin ya samu karbuwa cikin kaf danginta na uwa da uba,badon komai ba sai kyawun halayyarsa da kyawawan dabi'un da Allah ya huwace masa. Maido dubanta kan shahida tayi bayan ficewar umma,suka hada idanu,hakanan shahidan taji gabanta ya fadi,ta dauke nata idanun tana matsar qwalla,cikin taushin murya ba tare data saki hannunta ba tace "Shahida....inason naji meye matsalarki dashi wannan din da umma tace saikin aura,indai naji dalilanki masu qarfi ne nayi alqawarin tsaya miki harsai an warware komai" shuru na 'yan sakanni ya ratsa tsakaninsu,batajin zata iya furtawa wani komai,yin hakan kamar ta dabawa cikinta wuqane,tana ji ceqa wani sirri ne agareta ga duk wanda baisan meye faru ba,a hankali ta motsa labbanta sannan tace "Kawai bana sonshi,shima kuma baya sona,hasalima mun rabu dashi a qalla shekara shida kenan,ba wanda keda muradin wani" shuru anty usaina tayi tana nazarin kalamanta,ba shakka akwai wani abu,amma dukkansu amsa kusan guda ce,jiya jiya ta titsiye anwar din kan meye sanadin rabuwarsu da shahida amma ya kasa bata amsa daya qwaqwqwara,kowannensu bayason fallasa asirin dan uwanshi,hakan na nufin akwai ragowar wani abu da yayi saura game da zukatansu qarqashin zukatansu kenan koda su basusan da hakan ba? "Amma shahida....ya akayi kikasan baya sonki?,kuma dama an taba rabuwa hakanan babu wani dalili?"tambayar taso kaita maqura saboda rashin amsa "Miji da mata ma kan iya rabuwa haka kawai ya saketa badon ta masa komai ba,saidon qarewar wa'adin zamansu da Allah ya qaddara musu" saitayi shuru tana hadiyar zuciya tana neman amsa ta biyu da zata bata wadda zata gamsar da ita,da qyar ta iya hada abun fadi bayan anty usainan tace "Uhmmm,ya akayi kikasan baya sonki?" "Duk wani abu na nuna kulawa ko xiyara da zai nuna saurayi yana son budurwa babu shi tattare dashi,sau daya ya taba zuwa wajena,shima bamuyi ganawar dadi dashi ba,ta yaya zance yana sona?" Ta qarasa maganar badon abinda ta fada ya dameta koya dadata da qasa ba,a'ah,ta fada ne kawai donta riqeshi hujjar da anty usaina zata taimaka mata ta rana wannan auren da take kallonsa a matsayin qarfen qafa mai wuyar kwantuwa a gareta. Lallai ya zama dole ta shiga alaqar shahida da anwar,tana fata nan gaba dukkansu suyi dariya,tana fatan ko meye silar shiga tsakaninsu nan gaba ya zama tarihi,rayuwarsu ta koma kamar yadda take a baya "Naji dadi da kika kasance yarinya mai biyayya wa iyayenta,ina mai miki kyakkyawan fatan ba zaki toxarta ba in sha Allahu,biyayyarki zata kai miki da ixinin ubangiji" da wannan kalaman sukayi sallama,ta fice daga gidan bayan ta samu umma ta roqeta kan karta gaya mata dangantakarta da anwar,donta tabbatar hakan zai baiwa shahidan kunya. Tun a kan hanya ta soma gwada number anwar din,saidai bata sami wayarshi ba akashe take,da alama yana muhimmin wani abune,dole ta katse kiran ta isa gida,saidai lokaci lokaci tana gwada number tashi ko xata dace ta shiga. Tana idar da sallar magariba ta soma shirin barin gidan,umma ta dubeta "Amma da kin dan jinkirta tafiyar tukunna,saboda garin a dinke yake da hadari ga iska ta soma kadawa" "Idan ya sauko bansan ranar da zai dauke ba,anty zubaida kuma zataji shurun yayi yawa,don ban gaya mata ma ina nan ba" "Shikenan,Allah yayi miki albarka,yasa albarka a rayuwarku" "Ameen" ta amsa tana maida qwallar dakeson fitowa,haka ta baro gidan tana tafiya kamar wadda batason taka qasa,wanda bai sani ba sai ya zaci salo ne ko tana sane,amma ba komai bane sai tsabar damuwa dake cinta a rai,tana jin yadda hadarin ya taso sosai sanda takai tsakiyar layin nasu,iska ta dinga kadawa tana ratsa jikinta,saidai sam bata damu ba,bata damu da ruwan ya sauko ya daketa ba,hakanan bata damu data koma gida donta samu mafaka ba. Daidai lokacin da motarsa ke tsaye qofar gidan anty usaina wadda ta buqaci ganinsa a yau basai gobe ba,yana zaune cikin motar baikai ga yiwa mai gadi horn ba bare ya bude masa,ya tsaya ne amsa waya,dukka gilasansa a rufe suke ruf kamar yadda al'adarsa take yawanci idan yana cikin mota,bugu da qari kuma ma sabida iskar dayaga ta taso sosai,wanda yasan ba za'a rasa qura ba cikinta,gefansa ya kalla kamar wanda aka fisgi hankalinsa,sai yaga kaman itace ta wuce,yaci gaba da amsa wayar yana kallon bayanta,tabbas ita dince,amma me take har war haka duhun magariba ya mamaye gari bata koma gida ba,idanunsa suka ci gaba da kallonta har lokacin data dan bada tazara daga inda yake,yana shirin janye idanunsa yaga yayyafi ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96