Chapter 18
Chapter 18
Mubina dake goge hawayenta ta fada,harararta shahida tayi amma hakan baisa ta fasa magana ba "Wanine mai mota yazo...umma tace taje ta sallameshi,shine yaya anwar ya ganshi ya tafi" "Ubanki mai shegiyar magana" umman ta fada tana kai mata duka "A'ah hadiza barta ta fada....kice kawai kin soma shanshano wani ne....ke shahida tashi ki tafi,kema zamu gamu dake" "Duk abinda kaga dama ka fada,tunda dai ba zuciyata ka shiga ka hangi haka ba shikenan na gode Allah" tun kan ta fice daga soron nasu ranta ya soma baci,saboda taji suna gab da kaurewa da halayyar tasu da suka saba,saitayi maza maza ta ficema don kada ta jiyo abinda wunin yau zai sa ta kasa walwala,sam bata iya daurewa duk sanda wani sabani ya hasu tafi kowa jin zafin abun,tqfi kowa shiga qunci,ta rasa me yasa dukkansu basu haquri da juna,kowa kaman jiran kowa yake,kamar wadanda aka sakawa hannu cikin mu'amalarsu. Ba dadewa ta isa gidan anty amina,ta taddata tana wanki ta saka mata hannu suka gama tare,tanata tambayarta anwar kwana biyu bai leqo ba batace komai ba,har sai da suka gama suka zauna dakinta suna ninke wasu kayan da suka soma bushewa "Anty....nifa zuwa nayi ki mana sasanci da anwar" "Sasanci kuma,me ya hadaku kenan?,yau kwana uku kuwa da zuwanshi ya gaidani"ana ya gobe abun zai faru kenan?,shahida ta raya a ranta,batasan ma yazo din ba,jininsu ya hadu da anty amina,gashi kuma ba wani nisa sosai tsakanin gidanta dana anty usaina,don har zumunci ma suke yanzu ta sanadinsu,tsaf ta kwashe komai ta gayawa anty aminan,a take tasa shahidan ta kirashi,saidai harta gama ringing bai daga ba "kin gani ko anty?"shahidan ta fada idanunta na cikowa da qwalla "Bari na kirashi da wayata" anty amina ta fada tana daukan wayarta,ringin biyu ya daga cikin girmamawa "Anty amina...da kanki?" Ya fara fada cikin girmamawa "To ya zanyi?,diyata ta dagamin hankali?"dariya ya danyi "Shahida ko?" "Ita mana" "Karki qona katinki anty bari nazo" "Da kuwa ka taimakeni karta fashemin gata nan ta cika fam" da haka sukayi sallama tana duban shahidan "Shima a muryarshi kadai ya isa kasan cewa yana cikin damuwa da kewarki,wanne irin so kukewa juna shahida?" Kunyace ta kamata saita soma sinne kai. Ba'ayi minti talatin ba cikakke d'aya daga cikin yaran anty amina suka shigo suna cewa ga uncle da yake haka suke kiranshi,anty amina ta saka hijabinta tace suce mishi ya shigo.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGππ½* ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1οΈβ£0οΈβ£ A nutse cikin sallama ya shigo ta daga kai a hankali ta kalleshi saboda ita kadai tasan yadda tayi missing dinshi,shi dinma idanunshi na bisa kanta ji yake kamar ya shekara dari bai ganta ba,amma duk da haka saiya gintse saboda tuno ganinta da yayi da wani,daya daga kujerun falon ya samu ya zauna suka gaisa da anty amina sannan ta soma tambayarsa "Wai me ya hadaka da shahida?,duk ka firgitamin diya?" "Ta firgitani dai anty...bakiga har rama nayi ba?" Murmushi anty aminan ta saki,yadda sukeson junan nasu na bata sha'awa,bai boye komai ba ya gaya mata sannan ya dora da cewa "Wallahi anty wani irin kishine dani,ina da matuqar kishi kan abinda nakeso,ranar dana ganta wallahi anty ban iya bacci ba" "To kayi haquri mr kishi....bari kaji me ya faru" ta shaida masa kamar yadda shahidan ta gaya mata,nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana jin kaman an sauke masa qaton dutse daga zuciyarsa,sai a sannan ya sami salama "A rude nake anty,shahida ba ruwanmu bace mu talakawa,hankalina a tashe yake kada wani ya qwace min ita"dariya ya baiwa anty amina sosai har sai data dara "karka damu anwar,shahida taka ce in sha Allah,yo shahida muka bata wani bakaiba ai inajin fiya fiya zata sha ta mutum" sosai anty amina ta baiwa shahidan kunya,har sai data diba a guje ta shige dakin anty aminan,shima ya miqe ya fice yana dariya. A dakin ta taddata ta dubeta "To laila majnun,saikije ku sameshi tunda na kashe case din,saiki kula a gaba" "Na gode anty amina ta" "Eh kyace haka mana tunda na dawo miki da hasken rayuwarki ko?" Dariya ta tuntsire dashi sannan ta miqe ta zura hijabinta ta fice. Yana tsaye a soron gidan amma qofar fita yake kallo,tadan tsaya kadan a bayanshi,a jikinsa yaji tana wajen saiya juyo a hankali idanunsa zube fes a kanta,takowa yayi har sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sannan ya tsaya,a hankali cikin wata murya dake cike da mayen so yace "Nayi kewar wannan kyakkyawar fuskar,wannan ruhin ya hana ruhina samun barci bare ya samu salama,na cika da fargabar cewa na rasa hasken idaniyata,ashe abun duka ba haka bane" sosai kalamanshi suka sanyaya mata rai cikin daqiqu kadan,tayi qas da kanta tana fidda murmushi "A'ah dago kanki sosai don na samu qwarin gwiwar fada miki albishir din danaso yi miki tun rannan mai mota ya korani" "Don Allah ka daina zancan mai motar nan honey haba" "Na daina" ya fada yana murmushi "Na samu aikin kamfani Allah ya taimakeki...wani maqocinmu ne ya sama min,kwana goma sha biyar zan dinga aikin kwana,kwana goma sha biyar aikin wuni,zasu dinga biyana albashi duk wata dubu sha biyar" sosai fuskarta ta washe da fara'a tana jin farinciki na ratsata,tana jin burinsu ya soma daukar hanyar cika,rasa inda tsoma ranta zatayi har sai daya tsaya yana kallonta cikin mamaki,sun jima a soron gidan anty aminan kafin ya sanyata ta tattaro kayanta tazo su wuce gida,napep ya tsaida musu har qofar gida,sanda suka sauka ta zaro kudi zata biya ya harareta ya ciro daga aljihunsa ya biya,dariya kawai tayi,ko yaya idan yana da kudi ko iyakarsu kenan jikinsa baya yarda tayi masa hidima da kudinta,nan ma sun dan jima kafin suyi sallama ta wuce gida shima ya wuce. Cikin taimakon Allah ya soma zuwa aikinsa,saidai babban qalubalen daya soma fuskanta shine na rashin kudin mota,tafiya ce mai nisa tsakanin unguwarsu zuwa kamfanin haka yake niqar gari ya tafi,duk da cewa ya saba tun sanda yana makaranta amma tafiyar bata kai ta makaranta nisa ba,sai kuma abincin da zaici shima saiya dawo zai jiqa kwakinsa yasha musamman idan aikin dare yayi zai dawo da safe,duka wannan bai dameshi ba tunda yasan cewa komao lokacine,hakanan bai yarda shahida ko anty usaina sun sani ba saboda baiga dalilin da yana namiji zai dinga daura nauyi wa mata ba,a haka ya cinye watanshi guda,saidai kafin cikar watan ya fada yayi baqi,hakan ya sanya shahida ta sanya ayar tambaya a kanshi. Ranar daya amso albashinsa yazo da daddare,duka ya zube mata albashin nasa yana dubanta "Me zanyi dashi honey?" Ta fada bayan ta gama saka musu albarka "Inason ki dauki iya abinda ranki yayi miki,a matsayin albashin mijinki na farko" kai ta girgiza tasan ko tace masa a'ah cewa zaiyi bata isa ba saiya dauka,saboda haka tasan maganinsa. Da fari ta ware wasu kudaden tace wannan kudin kayan abinci da zai siyo ya dinga dafawa yana tafiya dashi kamfani,ta sake ware wasu tace ya sake dinka kaya kala guda duk wata zai dinka kala daya,ta sake ware wasu tace ya riqe ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96