Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 89

Chapter 89

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,309 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don sake kwantar mata da hankali da amintar mata tunaninta,saidai ya manta sa'idan bata mantuwa,ta kammala zubawa shahida komai ta miqe tana duban anty usaina "Na gama ummi" "Shikenan,idan kin sauka ki shiga kitchen ki tafasa min maganin nan,ki samu botiki mai murfi ki xuba a ciki kidan sabashi yasha iska kafin na sauko shi xansha" "Tohm" tajuya ta dubi shahida "Anty kici sosai don Allah ki cinye duka" murmushi kawai tayi tana dubanta,sosai yarinyar take sonta da burgeta. Inda shahidan ke zaune ya sauko,ya zauna sosai a gabanta,farantin dake tsakiyarsu ne kawai ya raba tsakaninsu,idanunsu suka shiga cikin na jina,kowanne ya zare nashi idon daga cikin na dan uwanshi yana jin yarrr cikin jikinsa saboda kusancin da sukayi da juna yayi yawa,saiya sanya hannu ya dauki kofin gabanta yana cewa "Tunda niba wanda yayimin tayi bari nayiwa kaina" "A'ah..ban yarda da wannan juyin mallakar ba,aje mata,kaidin baqo ne da bazaka dauka da kanka ba?" Murmushi ya saki yana tsaida kofin da yayi nufin kaiwa bakinsa "To ai anty itama ba zata sha ba idan bansha ba" ya qarshe maganar yana waiwayawa ya dubi shahidan yana kashe mata ido,sadda kanta qasa tayi saboda wani abu dataji ya saukar mata saman zuciyarta mau nauyi,yakai bakinsa ya kurba lemon ya miqa mata suna magana da anty usaina,qin amsa tayi har ya gama maganar ya juyo yana dubanta "Karbi mana,kosai na baki da kaina?" Harara ta cilla masa a fakaice ta saka hannu takarba ganin yana kai kofin bakinta,ya xuba mata ido sanda takai kofin nata bakin,tana sane ta juya daga wajen daya sha ta sauya gurbi,murmushin mugunta ya saki ya waiwaya wajen anty usaina yana tambayarta "Me yarinyarnan tazoyi gidan nan?,na ganta sanda muke shigowa" "Nafisa?....waitaji banji dadiba shine tazo dubani,amma tazomin da wata magana da nace saikazo naji ta bakinka tukunna" ta fada tana dan dubam shahida,batason yin maganar a gabanta,amma kuma tana ganin yin maganar a gabantan kamar xai bada wani alfanu game da kawo gyara kan yanayin mu'amalarsu da anwar,don har yanzu bata gamsu da yanayin zaman nasu ba,tana ganin yadda suke abu kaman baqin juna "Tace na baka haquri akan kuskuren datayi a baya,tana son idan da hali ka dawo ka....." Daga kai anty usaina tayi tana duban shahida wadda ta miqe tsaye "A'ah,ki zamanki shahida mana?"murmushi tadan saki,don tunda aka ambaci sunan nafisa zuciyarta ta gaya mata ba kowa bace illa wannan wadda suka gani dai sanda zasu fita,fuskar da anwar ya aiko mata da ita cikin envalope din data baiwa suna da baqin saqo,hotunan da har yau ta kasa rabuwa dasu dukda yadda suke qona ruhi da zuciyarta duk sanda ta tuna dasu,ko kuma duk lokacin data kallo gefan da suke aje "Zan saukane wajensu sa'ida" "To shikenan,nima ganinan zuwa,ai bamu gama hirar ba" "Toh anty" ta fada ta juya tana fice daga dakin,anty usaina ta bita da kallo farinciki na ratsa zuciyarta,tanason karanto wani abu game da shahidan,saita maida dubanta ga anwar,wannan karon shiya soma magana "Don Allah anty karki shiga maganar nan,an riga da an wuce wajen tuni,na godewa Allah da bani na soma gudunta ba bare aga butulcina,ta ruga data gayamin manufarta tun rannan,kuma kullum kwanan duniya saita aikomin da saqo kan hakan" ajiyar zuciya anty usaina ta saki,itakam a duniya yanzu ba abinda ya rage mata illa taga kan shahida da anwar din ya hadu kawai,ta tabbatar idan hakan ta faru babu kuma sauran wata matsala "Shikenan Allah ya zaba abinda yafi alkhairi,nikam yanzu bani da burin daya wuce naga kanku ya hadu yadda ya kamata kaida shahida,yarinyar tana da nagarta anwar,kayi qoqarin gyara zamanku,gashi kuna qoqarin cinye wata na biyu amma a karatuna banga hadin kan da nake buqata ba,ajiyar zuciya ya saki yana dan kashingida kadan,cikin zuciyarsa yana fadin antyn ba zata gane ba,shi kadai yasan me yakeji kullum kwanan duniya,a raye yake amma zuciyarsa matatta ce,ya gaza gano dalilin daya sanya shahidan aikata dukkan abinda ta aikata a rayuwarta,meye sila?,meya janyo haka?. Shahida na qasa suna hirarsu dasu sa'ida anty usaina ta koro anwar qasan takuma ce ya turo mata shahidan,sanda taje kusan karatun xama da miji tayi mata sosai ba kunya ko nauyi tsakaninsu "Shahida...kiyi haquri da yadda rayuwar aurenku taxo muku ahagunce kuma a kaikace,farinciki gamida walwalar gida a hannun matar gida take,tana da ikon maida gidanta aljannar duniya ko kuma akasin haka,duk yadda namiji keda taurin kai,taurin zuciya da kuma kafiya abune mai sauqi matarsa ta canzashi matuqar tayi karatu mai yawa akanshi da halayyarshi,kiyi haquri kiyi qoqarin canza gidanki,ki zama mace sosai,kiyi amfani da hikima da basirarki,kaf dinmu makusantanki dana anwar ba wanda yake fata ko burin rabuwarki dashi,kinga kenan babu ranar da zaku rabun,tome zayasa abinda babu ranar yankewarsa maimakon ka gyarashi kaji dadinsa ka amfaneshi saika zabi dawwama cikin karkatacciyar rayuwa maras dadi?,duk lokacin da rayuwar auratayya ta kacame ta lalace babu wanda yafi cutuwa a ciki,yafi quntata,yafi zama cikin wahala baqinciki da bacin rai irin MACE,namiji nada tarin hanyoyin da zai debewa kansa kewa ya ragewa kansa baqinciki da bacin rai,ba kamar ke mace ba da taki damar qwaya dayace wannan mijin da kike aure,kome anwar ya miki,duk da bansan girman cutarwar da yayi miki ba abaya,ina mai qasaqantar da kaina da roqa masa alfarmar ki yafe masa,ki tashi tsaye ki gyara gidanki,ki masa kyautatawar da girmanta zaisa yayi nadama yayi danasani,ya kuma ji kunyar aikata miki dukkan abinda ya aikata mikin,ita mace tana da wannan power,zuciyar namiji a wajenta ba komai bace horewa ce ta ubangiji,nasan zaki iya din ina kyautata miki wannan zaton,ina roqar alfarma zakiyimin shahida?"cikin jin kunya da nauyi gamida gasgata kalaman anty usaina ta gyada kai "Xan miki anty,zanyi in sha Allahu" ajiyar zuciya ta saki tana lumshe idanu "Na gode qwarai,amma kafin sannan,ki nutsu ki mu'amalanceshi ta yanayi da sigar da yake mu'amalantarki gudun kadda kisha wahala,ina fatan kin fahimceni?" Kai ta gyada mata alamun ta gane,hakan ya yiwa anty usaina dadi sosai,da kanta ta bude cupboard dinta ta ciro mata wasu rigunan bacci masu shegen kyau da sulbi guda shida,ta hada mata da turarukan bedroom suma guda hudu masu kyau da tsada,ta amsa tayi mata godiya sosai,saita danyi jim,anty usainam ta fuskanci akwai maganar da takesonyi,saboda haka tace da ita ta fada kada taji nauyi ko kunya "Anty aron sa'ida zaki bani don Allah tayimin ko sati guda ne" baki anty usaina ta bude "Keda zaki shiga yaqarmin tunanin dan uwa na hadaki da sa'ida ta hana ruwa gudu?" Kunya ta sata sadda kai tana dariya "Shikenan,amma ba zata wuce kwana uku ba" "Don Allah anty ki barta tayi sati" daqyar ta yadda da hakan,sa'ida murna kaman me ta hada kayanta ta bisu. *11:30 pm* Doguwar rigar bacci ce a jikinta mai sulbi wadda takai har qasa da dogon hannu,sai baby hijab data sanya wanda iyakarsa saman kafadunta,duk motsin datayi qamshi ne yake tashi harta iso matatattakalar qarshe wadda daga ita sai qaramar baranda da zata sadaka da falon samanshi,cak ta tsaya tana ajiyar numfashi,shida kanshi ya mata magana kafin su shigo gidan kanta taho samanshi saboda sa'ida kada ta karanci yanayin zamansu,baiso anty usaina ta fahimci komai,baisan yayi sara bane kan gaba,ta riga data gama shirinta dukda ciwo da takeji a qirjinta da nauyin alqawarin data dauka,anya zata iya saukewa?,takewa kanta wannan tambayar,duk sanda

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});