Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,312 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

anty,ko waye aka yi masa haka anty ba'a kyauta masa ba,ta yaya za'a badani kamar an gaji dani,yanzu an siya min mutunci kenan?,kina gani fa shi wanda akace an bawa din bansan ko waye ba,uwa uba yau kwanaki nawa shi dinma bai nemeni ba,qafa da qafa kiran waya ko text,me kike tunanin sun jawomin kenan anty?" Ta qarashe maganar da sigar tambaya idanunta kan anty wanda gab suke da ziraro da qwallar dake cikinsu,kai anty zubaida ke kadawa,ita kanta abun bai mata ba amma uncle hisham ya dakatar da ita kan babu ruwanta,duk wata hanya da zata bi tasha cikin uncle din ya gaya mata na ko waye donta gayawa shahidan ta samu dan relief ya tosheta "Haka zaki haquri shahida,qaddara ta riga fata,amma sai nake ganin idan da laifinsu kema da naki laifin,kinyi wasa da damarki qwarai,shekara nawa nuradden na bibiyarshi ki bashi dama kikaqi,idan da ace kin bashi dama da tuni yanzu wani zancan ake ba wannan ba,nidai bani da wani abunyi bani kuma data cewa saidai ince kiyi haquri kiyita addu'a kawai,nima kuna zan tayaki" kai kawai ta kada,ta bude baki zata ce wani abu wayarta ta sake kadawa karo na barkatai,tare idanunsu yakai kan wayar,nuradden ne,sai anty zubaida ta kalli shahidan "Babu hujja ko alfanun boye masa komai,kawai ya kamata ace ya sani ni a ganina" tana kaiwa nan ta miqe don ficewa ta bawa shahidan damar amsa wayar. ******* ****** ********* A hankali ya miqe daga gaban qaramin akwatin mai lambobin sirri yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,duk sanda ya budeshi koda wani abu zai ciro daga ciki saiya tayar masa da wawakeken mikin dake danqare a zuciyarsa,cikin nutsuwa wadda ta cakudu da kasala ya isa gaban akwatinshi ya jefa abinda ya dauko daga ciki ya rufe zip din akwatin sannan ya saukeshi daga saman gadon ya soma janshi har zuwa falonshi. Saman dining ya isa ya zauna a nutse ya soma duba abinda aka dafa din,rabin hankalinsa nakan wayarshi da haka ya zuba abincin ya soma ci,knocikin din da akayi shi yaja hankalinsa,saiya dan daga kanshi yana duban qofar,kafin yace komai aka turo aka shigo,nafisa ce,sanye cikin doguwar riga ta atamfa da madaidaicin mayafi,idanunta bisa kanshi yayin daya dauke nashi idanun ya maida kan abincinsa,hakan yasa tayi hanzarin tunawa da batayi sallama ba,saita dan koma da baya tayi sallamar sannan taci gaba da takowa cikin falon a hankali tana nazarin falon,falon ya jima yana burgeta,duk da wannan shine ganinta dashi na uku,saboda haidar din bai lamunci ta dinga zuwa masa gida ba bayan shi kadaine cikin gidan. Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa "Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa "Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta "Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar "Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi "Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya" *ga mai buqatar sabon littafina da zan fara bayan alqawarin Allah,sai yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,da zarar sunan ya fito akwai rubutun SUBSCRIBE da jan rubutu,ki danna shi sau daya zai koma black,saikiyi screenshot ki turo zuwa number dake qasa,za'a saki a group din in sha Allah* 07038670166 *Ziyarci tasharmu ta youtube don samun qawatattun litattafan hausa,masu qunshe da zallar soyayya darasin rayuwa da kuma nishadi* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *Alqawarin Allah* 2️⃣8️⃣ Bata tsaya ba har sai data isa dining din,fuskarwa a washe take kallonshi,ta dora jakarta saman teburin tana kallon abincin da yake ci,saita zari spoon ta saka cikin farantin nashi tana cewa "Goodmorning boss" idanunshi ya daga yana janyewa daga cin abincin yana cewa "Morning...me kika fito yi yanzu?" Zama tayi saman kujerar dake daura da ita,ta langabe wuya tana kallonshi bayan ta aje cokalin hannunta "Rakiya mana dear....uhmm....ji nake kaman na bika wlh,kaika janyo mana kaga da tuni tare zamuyi tafiyarmu babu me tuhumarmu" saiya yagi tissue yana goge bakinsa,ya cilla dan qaramin dust bin dake gefanshi yana miqewa daga saman kujerar "Amma dai kinsan akwai wadanda zamu fita tare,kuma duka maza ne,bai kuma kamata ki shiga cikinsu ba ko?" Itama tashi tayi tana daukar jakarta,cikin hanzari harta cimmasa tasha gabanshi "Amma dear,tafiyar wata biyu fa banan kusa bane,ni a wajena ba laifi bane don nayi maka rakiya". Bai amsata ba saida ya ciro wayarshi ya amsa kiran dake shigowa sannan ya maidata ya daga kai ya zuba mata idanunsa da kullum kwanan duniya ke sanya nafisar sake dilmiya cikin so da qaunarshi,kallonsa kawai yakansa taji wani sanyi da sassauci cikin ruhinta,taji tamkar an mata rahama "Waye ya kawoki?"wuya ta noqe tana jefa masa wani kallo da take fata ko yaya yayi tasiri a zuciyarsa "da kaina na taho"hannu ya miqa mata,ta kalleshi tana son qarin bayani "Bani muqullin motar"ba musu ta zuge jakar tata ta dauko muqullin ta miqa masa,saiya sakashi a aljihunsa sannan yace mata muje. Tana gaba yana bayanta,a hankali yakai idanunshi kanta,saiya lumshe idanu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake mata rakiya zuwa gida,lokacin da take sadakar shinkafa da wake,ya tuna randa ta zura da gudu tabar mishi botikinta saboda ya furta mata kalaman soyayya,murmushi ya sube masa cikin qiftawa da bismillah kuma murmushin ya bace bat,bacin rai ya maye gurbinsa,ya hadiyi wani abu mai tauri yana girgiza kai,hotunanta ita da saurayin suna yawo a idanunshi,fuskar saurayin daya ajeta a mota har yau taqi barin idanunshi,ya dunqule hannunsa daya yana jin wani abu mai dumi na zagaya jikinsa,har kwanan gobe takaicin dukan da baiwa saurayin yake ba,amma yaci alwashi...yaci alwashin dashi kadai ya barwa kansa sani...... Inda yaje aje motocinsa ya nufa,ta bishi a baya,ya bude daya daga cikin motocin ya mata alama da hannu kan ta shiga,wani dadi ya kamata,yau din taga kamar wani dama dama yake da ita,ta rabeshi ta shiga ta zauna,maimakon shima ya shiga sai taga ya maida murfin motar ya rufe,ya duqa bakin window din idanunshi cikin nata,wanda hakan ya sake narkar da ita ya kashe mata jiki,qamshinsa ya cika mata hanci,kamanninsa suka fito sosai,cikin daddan muryarshi yace "ga driver nan zai kaiki gida,karki sake irin wannan fitar da sassafe haka,zamuyi waya kafin na tashi,motarki kuma zansa a kawo miki ita,sai Allah yayimin dawowa?" Kai kawai ta gyada,ta kasa cewa komai saboda gaba daya jikinta a mace yake dakyau da kwarjinsa,baya yaja ya miqawa drivern muqullin,yana tsaye har suka fice daga gidan,ya saki ajiyar zuciya yana duba agogon hannunsa,da yana da yadda zaiyi ya ragewa nafisa sonshi ko yadda ta damu dashi da yayi,sam baiso ta zura kanta da yawa kamar yadda yayi,shi a ganinsa wannan shine babban kuskure ko gangancin da mutum zaiyi a soyayya. ***** ****** ******** A hankali take takowa zuwa qofar gidan nasu,sanye da dogon hijabi har qasa mai hannu,kallo daya

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});