Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,305 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba,tana zaune suka shige kitchen din kuwa itadai tana cikin baqinta suna hirarsu. Qarfe biyar suka kammala lafiyayyen abinci,hasina ta bude sabbin warmers din shahida ta zuba komai ta tsarashi saman table,sannan suka gyare kitchen da gidanma duka suka soma haramar tafiya. Ta rasa me zata basu,saita tuna salary dinta na watan nan da company ya biyata duk da batakai qarshen watan ba biyu ta raba ta saka rabi cikin jakarta,jakar ta bude ta dauko musu ta hada musu da snacks na gararta,kamar kada su tafi haka taji,hakanan ta rakosu har farfajiyar gidan,daidai sanda wasu baqin katsinan suka shigo cikin motar gidan anty usaina bisa jagorancin sa'ida,suka gaisa dasu hasina su suka wuce su kuma suka shigo ciki. Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa da juna,taja sa'ida kitchen ta hada mata kayan abinci tace takai musu,idan takai ta dawo ta dauki ruwa da drinks,sanda ta dawo shahida na ta gama shirya cups din da komai sa'ida ta qaraso tana murmushi ta dubi shahida "Anty,baki tambayi uncle ba,yana gidanmu wajen ummi,kinsan me yacemin?" Kai shahida ta kada tanadan murmushi badon hirar ta mata ba,kawai sa'idan na burgeta hakanan "Wai idan munje mu duba masa ke,ko kunyar ummi dake wajen fa baiji na anty,wai ki bashi abun dadi nakai masa" wato sai zaiwa siyasa kenan saboda yaga anty usaina a wajen?,lallai kam to su zuba,saita saki dan murmushin yaqe don kada yarinyar ta gane "Nikam inajin kunyar ummi,qyaleshi zai dawo gidan ai" daga haka yarinyar ta dauki ruwa da lemo,ita kuma shahida ta dauki kofuna suka fito. Ba laifi sun dan taba hira dasu suma,babu ruwansu kaman anty usaina,hakanan suna da girmama mutum kuma suna d sauqin kai. Gab da za'a kira magriba don har sun soma daura alwala motar anwar ta shigo gidan,shahida na tsaye tana shimfida musu manyan abun sallah ya shigo,donsunqi shiga dakin data ce su shiga suyi sallar a can,idanunshi akanta,karo na farko a rayuwarsa daya soma ganinta a haka gayarta,ba hijabi babu mayafi,cikin riga da skert na atamfa da suka xauna mata das a jikinta,suka fidda shape dinta sosai,wani kishinta yaji ya sake kamashi sosai fiye da baya,saiya dauke kansa yana son hana bacin ranshi tasiri,duk sanda zai ganta hotunannna dawo masa,abun ya zame masa kamar jarraba,bai taba zaton yana da halittar kishi ba haka,bai tama tsammanin yana kishin wata halitta a bayan qasa kamar yadda yake kishin shahidan ba,a yanzun da take cikin gidanshi sai yake jin yayi wani abu daya dace,yake jin hankalinsa yafi kwanciya da samun nutsuwa a hakan koda ba zaman dadi bane akan tana waje ba tare dayasan me take yi kuma aina take ba,tare dawa take,duka yanzu ya samu aminci game da wannan. Ita ta soma yi masa sannanu da zuwa,yadan tsaya suka sake gaisawa dasu,yace bari ya shiga ya daura alwala kada a kira sallah,daya daga cikinsu data ke zaton qanwar babansa ce tace "Ai muma muna idar da sallahr xamu wuce don zamu koma mu shirya kayanmu gobe sai ta dikko dakin kara" murmushi ya saki "Dakin kaara ko dakin kara?" Dariya suka saki ta maida masa amsa da alama akwai dan wasa haka a tsakaninsu "Oho kai ka sani,koma dai dakin meye ta maka komai,tunda gashi sun baka mata da nan kanon suka kasa baka saida kayi kamun qafa damu,kai din kanka su suka samar dakai" "Gaskiya ne,kin gama magana" ya fada yana dariya dariya gami da gyada kai "Kafin ku wuce na fito in sha Allah" "Toh babu damuwa" ta amsashi,saiya juya da dan sassarfa ya soma hayewa saman. Tsaiwa tayi ta rasa abunyi,duk saita tsargu taga kaman kowa idanunshi a kanta yake yanason yaga ya zatayi,duk da cewa ba haka bane kowa sabgar gabanshi yake "Jeki mana shahida?,mu ai ba baqi bane karki damu" anty aminan dake shirin tada sallah ta fada,saita miqe cikin jin kunya ta soma takawa a hankali ta isa inda hasina ta shirya kayan abinci,ta dauki jug data hada lemo ya fara qanqara shi yasa ta fito dashi,tasan wai kafin lokacin cin abincin ya huce yadda za'a iya sha,ta dauki cup daya cikin mutuwar jiki ta nufi saman ta soma taka step din,xataso ta sanya koda mayafine,amma batason tayi wani abu da zai bar alamun tambaya game da ita akan baqin,fatanta daya Allah yasa taje ta taras dashi a bandaki,shine kawai zatayi saukowarta ba tare dashi yasan taje ba,hakanan suma ba tare da sunsan cewa bata je din ba. Qaramar varender mai kyau itace zaka soma taddawa bayan ka gama tsallake matattakalar benen zuwa qarshenta,wadda aka qawata da tiles da kuma shukes shuke na roba wanda idan ba tabawa kayi na zaka rantse da Allah rayayyu ne na gaske,cikin qananun kwandunansu masu ado suma,sai qofar glass wanda ta mamaye gabanka,daka tura zaka tadda wani ni'imataccen falo,wanda iskar dake kaiwa da kawowa ma daban take,komai na falon farine sol idan ka debe kayan kallon dake ciki,don hatta da frames masu sunayen Allah dake jikim bango farare ne,qofofine guda uku a saman kowacce tana dan nesa da 'yar uwarta. Bata gama wannan nazarin ba taji motsi daga gefanta,ta juya saita ganshi tsaye yana cire agogon hannunshi wanda dorashi da yayi saman teburin gilashin ya bada sautin daya jayo hankalinta,ya dan dosana gefan kujerar ya cire takalmanshi hadi sa safar gaba daya ya hadesu waje daya,safar agogon takalmin da muqullin motarsa,sau daya ya daga kai ya kalleta,saiya dauke ya taka zuwa inda ya aje remote na ac ya dauka ya soma rage sanyin da take kwararowa sannan ya ajeshi. Takawa yayi kaman zai shigeta ya wuce bedroom,sai kuma ya dakata saitinta,sunyi kusanci da yawa,tanason jan baya amma batason nuna masa tsiawarsa ta wani dameta kota dadata da qasa,idamunshi cikin nata ya sanya hannu ya dauki jug din ya daga cup daya ya zaunar dashi saman tray din dake riqe a hannunta tunda ta shigo,ya tsiyaya lemon a ciki ya aje jug din sannan ya dauko cup din yakai bakinsa,har ya gama shanyewa idanunsa na kanta,yayin da ita kuma taqi duban sashen da yake,sai daya shanye tas sannan ya aje cup din ya wuceta,sai daya dora hannunshi saman handle din sannan yace "Baiyi dadi bama" ya tura qofar zai shige,sarai ta jishi,haushi ya cikata,takaici ya qumeta "Dama badon kai na kawo ba,albarkacin wasu kaci,idan ka isa kuma ka amayomin da abina mana,aiba matse bakinka akayi akace sai kasha ba dama" fasa shiga dakin yayi,yayi taku uki da baya sannan ta juyo gaba daya,cikin takun nan nasa dai ya iskota,kaman xai hadeta cikin jikinsa har yanzu idanunsa na narke cikin nata yace "Zan amayoshi,amma nima ba zakimin asarar ruwan jikina ba,saidai idan zaki shanye amanne tas" ba shiri ta ware duka idanunta tsakiyar nashi ta watsa masa harara "Allah ya kiyaye ya sawwaqe,in sha amanka ni shahida?" Kafe juna sukayi da idanu,fuskarta na nuna bacin ranta muraran,yayin da nashi yanayin ya kasa nunawa,bacin rai ko walwala?,yaci gaba da duban qwayar idanunta,yana tuna wani lokaci can baya da ya taba zuwa mata yana zazzabi,kwananshi uku baida lafiya amma yaqi yarda ta sani don karta tashi hankalinta,duk da haka ta fahinta,ta kuma nuna rashin jin dadinta na yadda ya boye mata,tace da shine da baida zaune saiya tabbatar ta samu lpy donme ita zai boye mata?,da qyar ya lallasheta kan ya samu sauqi aisuna tsaka da fira yaji bazai

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});