Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,301 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi shigar ne?,batason dukkan wani abu da zai mata kyau a yanzu har yaja hankalin wani zuwa gareta,ta saka hannu ta soma cire lullubin laffayar dake kanta anty zubaida ta turo qofar ta shigo,wanda hakan ya tarwatsa abinda tayi niya "Me kike haka?,yau lafiyanku kuwa shahida?"koda ta boyewa antyn yadda take qare mata kallo tasan saita fahimceta,jin tayi shuru saita girgiza kai tana tabe baki " damuwa dai damuwa dai?,ina zakikai damuwa shahida?,wannan kuma da kike niyyar cireta fa?,don ta miki kyau?"dole yadda anty zubaidan tayi maganar ya baka daroya,saita murmusa tana maida lullubin gami da zarar jakarta "Ina kwana anty?" "Lafiya lau ni zan fita inason idan ya saukeni saiya wuce dake makarantar basai ya sake dawowa ya dauki wani ba" "Tohm anty" tare suka fito daga dakin shahida ta wuce saman dining ta soma tsakurar abinci,anty zubaida kuma ta koma dakinta don dauko mayafi da jakarta. Sam abincin ji take bazai ciwu ba,don haka ta hada tea kawai tasha anty zubaidan na fitowa suke fice tare. Sun dan sake bata lokaci a hanya saboda cunkoson ababen hawa da suja tarar a hanya wanda shahidan ta rasa na meye,titi ne da yake da wuya ka samu cunkuso akanshi,ita kanta data dubi agogonta sai da taga makarar tayi yawa,da qyar suka samu hanya suka wuce,ta sauke ajiyar zuciya sanda suka isa bakin katafaren ginin makarantar noor international academy "Yau ina tunanin zamu iya kaiwa biyu,saboda yaune hutu,idan mun tashi zan maka waya in sanar maka" "To babu matsala" ya fada yana tashin adaidaitan,tana tsaye kaman wadda aka dasa har adaidaitan data sauketan tabar gurin,sannan ta soma takawa a hankali kaman mai sanda zuwa cikin makarantar,haka kawai taji zuciyarta tayi mata nauyi,qafafunta kuwa kaman an sare su,bugun zuciyarta na daduwa duk sanda ta qara wani taku guda da zai kusantar da ita da cikin makarantar. Harabar makarantar fetal,sai ababen hawan wasu daga cikin malamai da kuma wasu baqin motoci guda uku da take kyautata zaton na baqonsu ne,shuru makarantar take,hakan ke nuna mata cewa duk an tafi zuwa hall din da za'a gudanar da taron da kuma hutun dalibai,ta dan tsaya tana shawarar ta soma kaiwa huda maganinta tasha kota bari sai sun hadu a dakin taron? "Malama shahida ya akayi haka?" Taji muryar kausar wadda ta fito daga can wani sashe wanda zai sadaka da dakin taron,murmushin yaqe shahida tabi kausar dashi saboda yadda takejin jikinta ba qwari haka kawai "An sallami kowanne aji saura naki,yau tsarin na daban ne,inviglating ya yiwa kowanne aji saiya gama dubaka sannan sai ku wuce kai da dalibanka dakin taron" murya qasa qasa tace "Yana naki ajin yanzu ku kawai ake jira a soma,kiyi sauri ki riskeshi donma yana da kirki,nima amakare na iso amma ina bashi uzuri ya karba" kai kawai shahida ta kada mata sannan ta soma takawa zuwa sashen azuzuwa. Bayanshi take iya hangowa saboda qofa da ya baiwa baya,tsaye yake gaban blackboard sanye da suits ash da suka zauna das a jikinsa,fuskanshi na kallon 'yan ajin da alama wani abu yake saurara daga garesu. Sautin fitar murmushinsa shi ya soma dukan kunnenta,bisa alama wani cikin daliban ya fadi abinda ya bashi dariya "To shikenan...next question....who is the best teacher in dis school?" "Anty rahama...aunty rahama!" Suka hada baki dukkansu suna fada,abinda ya sake sashi dariya qwarai,irin dariyar daya jima baiyi irinta ba,baisan wanne irinso yaran kewa malamar tasu ba,komai anty rahama anty rahama,wai wace anty rahama nan "Auntyyy" wasu daga cikin yaran da suka hango tsaiwarta bakin ajin suka fada cikin shauqi da nuna qauna tamkar sunji tambayar da yakewa kanshi,duban yaran yayi sannan a hankali ya waiwaya yana son yaga wace. Shahida....shahida ce dai tsaye cikin shigar kamala ta lafaya,jakarta rataye a kafadarta idanunta saye da farin gilashin daya zamto yana taimaka mata wajen gani,sakamakon matsalar idanu da taso gamuwa dashi tun shekarun baya saboda yawaita kukan da take,wani irin abu yaji yana zagayawa saman kanshi,tsigar jikinsa gaba daya ta zuba,zuciyarsa ta kasu kashi biyu,kowanne sashe na zuciyar tasa da abinda take ayyanawa. Gaba daya jin jikinta tayi tamkar an zare dukkan wata laka data yi saura,,nutsuwa tayi qaura daga jikinta a take,idanunta cikin nashi a hankali taga yana juye mata daga anwar data sani zuwa wani mutum daban,matashin saurayi mai kyau kwarjini kamala da haiba,matashin saurayi daya jiqu da hutu da naira,matashin saurayi mai cikar zati,tsayayyen namiji wanda tambarin ilimi nutsuwa da wata qasaita ta daban ta bayyana muraran kan fuskarshi,dukkan wani abu daya gani tattare da ita shekarun baya suka soma dawowa idanunshi daya bayan daya,hotunan da idan ya tuno dasu suke hanashi bacci duk dare,ganinta cikin halin maye,jinin zubda ciki na gangarowa daga qafafunta,yaci gaba da kallonta yana takowa inda take tsaye cak,sai yaga kaman a sannan ne abinda ke jikin hotunan ke faruwa,take cikin 'yan sakannin da bai wuce ka qirgasu da yatsunta biyu zuwa hudu ba idanunsa ya sauya launi,jijiyar kanshi ta motsa ta tashi,sai daya zo dab da ita sannan yace "Kina nufin a haka zaki baiwa yaran mutane tarbiyya?,a haka kike koyar da yaran jama'a?,na tambayeki ma me kike koya musu?,uhmmm gayamin,?,yadda zasu....." Sai kuma ya kasa qarasawa ya kaiwa iska wafta da hannunshi sannan ya dunquleshi tsam kaman zai tatse dukkan jinin dake cikin hannun nashi gaba daya,dai dai sanda shugaba kula da dukka sashen makarantar ya iso ganin shuru har yanzu bai iso ba,cikin girmamawa ya rusuna "Sir....." "Dakata!" Ya tsaidashi cikin tsawa "Dama irin wadan nan malaman kuke baiwa yara su koyar?" Cikin mamaki ya dubi shahida da yake nuna masa,wadda take tsaye qam a wajen kaman an dasata idanunta kan anwar,tana jin wani fushi na ratsata amma tana ta qoqarin hana hakan tasiri "Sir.....kodai wani akasi aka samu,amma malama shahida na daya daga cikin malaman da kaf makarantar nan babu kamarsu a kowanne sashe" "Sauraramin" ya kuma dakatar dashi wannan karon har yana daga mishi hannu,ya maida idanunsa cikin nata "Indai wannan ce malamar da babu kamarta tabbas bakusan abinda kuke ba,babu abinda ta iya!,bata iya komai ba!,daga yau na koreta!,na koreta cikin malaman makarantar nan.....kar qafarki ta sake tako mana makaranta,you are fired!" Dukkan wani qwarin gwiwa da taso tattarowa ya tarwatse da kalmarshi na qarshe saboda yadda sautin ya fito ya bada amsa kuwwa cikin ajin,qoqarin tattaro abinda zata fada take saidai bakinta ya gaza fidda sautin saboda karayar da zuciyarta tayi,idanunta suka hada qwalla fal suna shirin ga gangarowa,saiya sake saka idanunsa cikin nata cikin wani qwarin gwiwa da yake ji yace "Uhmm...kina da wani abun cewa ne?....say it....say it mana!" Ya kuma fada cikin hargagi yana dan dukan qirjinsa da yatsunshi gaba daya,jakar dake kafadarta ce ta sulmiyo saboda yadda jikinta ya soma rawa,gaba daya kayan ciki suka tarwatse a wajen ciki harda kwalaben magungunan huda,a kansu idanunsa suka soma sauka,wani tashin hankali da baisan na meye ba ya rufto masa,saiya daga kai da sauri yana kallonta,sam ko daya bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa ta tattare kayayyakinta ko ta dauki jakar,hakan yasa ta juya da sauri ta soma takawa,fatanta da burinta kawai shine tabar makarantar,tabar wajen,tabar inuwar da anwar yake tsaye a cikinta,burinta shine ta nesanta dashi kawai,ta daina ganinsa ta kuma daina jin sautinsa "Ki dawo ki debi wannan kayan zatar naki" maimakon dawowar kamar yadda ya buqata saita qara sauri

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});