Chapter 46
Chapter 46
ta hada ruwa mai dumi sosai tayi wanka hade da alwala sannan ta dawo daki ta shirya cikin wasu kaya masu dan kauri,sai datayi sallar magariba sannan ta sake fitowa. Yanzun ma a zaune ta samesu,saidai da alama faruqu da haidar sunje masallaci sun dawo,anty zubaidan ma wannan karon da hijabi jikinta,huda dake duqe gaban socket ta dago tana cewa "Yauwa anty,yaa nuradden ne ya kiraki" "Uhmmm" ta amsa tana dubanta,saita ciro wayar ta kawo mata ta karba tana dubawa,Allah ya taimaketa ba abinda tayi ruwa bai tabata "Na gode hudallahi" shahida na murmushi ta fada. Saida sukaci abinci sannan ta duba dinkunan,sunyi masifar kyau ko ba'a fada ba tasan zasu zauna mata a jiki,saita yanke kawai ta barsu saida bikin da zasuyi,ta ninke kayan ta kwashesu ta haura sama dasu,don yau da wuri takeson kwanciya har yanzu kuma yayyafi ake,saboda gobe sammakon fita zatayi akwai ayyuka da yawa. Tana shirin jan abun rufa kiran nura ya shigo wayarta,ido ta lumshe sannan ta waresu,ba yadda ta iya haka ta daga "Ranki ya dade....yau an manta dani kwata kwata ko?,koda yake dama idan ban nemeki ba saidai na shekara ina jajenki" "Ba haka bane...ayyuka ne yau sai hamdala" "Ina fatan dai basu gajiyarmin dake ba?"ajiyar zuciya ta sauke "Gajiya kam akwaita,don yanzu ma shirin kwanciya bacci nake" "Da wuri haka?,da qorafi nakira nayi,amma tunda haka ne kiyu baccinki dakyau,ki gayan yaushe zanzo mu hadu?" Kanta ta juya daya sashen,ta danyi nazari kadan "Kasan yanayin aikin nawa,wunin office ne,idan na dawo kuma na gaji bacci kawai nake buqata" tsaf ya gama ramfota,haduwar tasu ne bataso,ita kuma takurawa da zancan aure da yake a 'yan kwanakin da yadda yake marairaice mata ya sanya bata fiya son haduwar tasu dashi ba,sakata yake kawai a corner "Duka ba damuwa bace,ni idan anmin izini saina riskeki har office din lokacin break mu tattauna abinda zamu tattauna din,karki damu bazan jima ba zan tafi,daga nan har zuwa next week ina jiranki" numfashi ta sauke,ya gama kamata kenan iya wuya,amma itama bari ta qure haqurinsa "Saidai nan da sati daya rana ita yau" "Allah ya kaimu" ya amsa hakan bisa ga mamakinta,da haka sukayi sallama ta kwanta tunani fal ranta,tana mamakin yadda nuradden yake iya shanye duk wani hali nata,bata taba kamashi da rashin yi mata uzuri ko hanzari ba,tanajin nuran na hawa wani mataki fiye da wanda yake kai a baya,ya kamata ta sake bashi wata damar ko yaya take,da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita. *BAYAN SATI DAYA* Turare ta dauka ta fesa abu na qarshe cikin shirin fitarta office,ta kalli kanta sosai ta tabbatar komai yayi mata,shiga mai kyau da tsari,riga da skert na swiss atampha wanda suka mata cas da mayafi yalwatacce wanda ta dorashi saman daurin dankwalinta data dan turoshi gaban goshi,hannunta agogo ne kaman yadda tafi son sakashi fiye da awarwaro,wuyanta sarqa ce da dan kunnayensu masu azabar kyau qirar kamfaninsu,wanda gwaji ne akayisu aka bawa masu manyan matsayi a kamfanin,takalmanta ta jawo rufaffe na mata wanda ya dace da shigarta,tana zuge jakarta da zata fita da ita taji shigowar saqo a wayarta,saita dakata da abinda take ga zatonta mudassir ne daya daga cikin abokan aikinta wanda yace zai tura mata wasu bayanai kan lissafin da suke tayi na wasu siyayya da wani kamfani yayi na sarqoqi,ga sabanin tunaninta saita tarad da nuradden ne _Da fatan wannan kyakkyawar halittar ta tashi lafiya cikin amincin ubangiji,yau sati guda cif cif,Allah yasa banyi azarbabi da yawa ba_ Kyawawan idanunta masu kyau da haske ta juya gabanta yadan fadi,sam ta manta da zancansu wanda yace ya bata sati guda,saita sauke numfashi data tuna cewa bai taba zuwa kamfanin nasu ba,asalima bata taba gaya masa inda yake ba,hakan na nuna baisan office dinta ba,bazai kuma iya zuwa ba har sai ta bashi adress,tuna hakan ya mata dadi,don idan yazo din bata jin zaya samu amsar da yake da muradi,saboda haka ya kashe wayarta ta jefa a jaka tana murmushin nasara,ta duqa ta qarasa saka takalminta ta dago tana rataya jakarta huda ta shigo cikin shirin makaranta itama,gaida shahidan tayi ta gaya mata sun fito "Muje hudallah...wannan makaranta anaji da ita" dariya ta saki "Sosaima anty,kinga randa me makarantarmu yazo,ya bamu labarin wahalar da yayi saboda karatu,yace mu dake muyi karatu sosai muma donmu zama irinshi" yatsine fuska shahida tayi saboda yadda zancan ya tuna mata da ranar "Allah ya kiyaye" shahidan tayi subul da bakan fada wanda yasa buda ta juyi da sauri "Allah ya kiyaye kuma anty?,yana da kirki fa,sannan yana da karatu,ya iya turanci da larabci,gashi kyakkyawa,shiyyasa ranar banji dadi ba da kika koma gida baki ganshi ba.....kinsan me?,uncle fa muke ce masa,yace duka mu yayanmu ne..." "Hudaa....a'ah" shahida ta fada tana kallonta,itama sai ta saka ido kawai tana kallon shahidan "Oya muje karki sa muyi late dukanmu" dariya ta saki tana tafiya sauri sauri "Mu yanzu ai ba'a dukan late comers,uncle ya hana" goshinta ta dafe da tafin hannunta,wato dai hudan ba zata daina mata zancan mutumin nan ba. Tana mamakin yadda suke ganin kirkinsa haka da yawa,basu san cewa macijin sari ka noqe bane shi?. Agurguje kuma a tsaye ta hada tea dan kadan ta kurba,duk yadda anty zubaida tayi kan ta tsaya tayi break sosai cewa tayi sauri take yau suna da aiki da yawa,haka ta fice bayan ta musu sallama,aka dauki huda itama ta shiga tata adaidaitan suka wuce. A cikin company ya ajeta kaman yadda suka saba ya juya ya fice ita kuma ta shige zuwa cikin ainihin kamfanin,a sashen kula da baqi na musamman zata wuce cikin hanzari tajuyi muryar mudassir "Kin kusa makara fa" waiwayowa tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta dubeshi "Wallahi,amma na gode Allah da ban makara ba,ina fatan komai ya zama ready" kafadarshi ya daga yana dubanta,yana da muradin shahidan sosai tana burgeshi,komai nata abun sha'awa ne amma kame kai da jan ajinta yasa ta masa wani irin kwarjini daya sanyashi ya kasa kwatanta mata bare ya furta "Eh tuni ma" ya qarashe maganar yana miqa mata daya daga cikin file biyun dake hannunshi,hannu ta saka tana buda shafukan farko tana dubawa sama sama,daga kai tayi sai suka hada ido yana kallonta,hakan ya sanyata dan tsare gida "Ka sameni a office dina muyi acan inaga zaifi" ta juya abinta ta isa bakin elevator da xata kaita zuwa bakin ofishinta. Da sallama ta shiga duk da cewa ya sani babu kowa ciki,a nutse ta qarewa office din kallo,ko ina tsaf yake yana fidda sassanyar qamshin da ita ta yiwa kanta zabin kalar freshner din da takeso wadda ta banbanta data kowa,wadda ke mata shara din ta qwarai sosai,sannan kuma tasan aikinta,hakan yasa takejin dadin aikin da take mata,tasan ra'ayinta da tsarinta,jakar hannunta da file din ta dora saman teburinta sannan ta taka a hankali ta isa bakin windows din office din ta bude kowanne,iska mai dadi da sanyaya rai ta soma kunno kai,irin iskar damina mai taushi da sanyi,tana son irin wannan iskar,sabida banu iska mai dadinta,fresh ce daga indallahi,sai data tabbatar ta gauraye office din sannan ta rufe windows din,ta sauke labulayen ta kunna AC,hakan ya qarawa office din wani dadi da yanayi na musamman. Tana zama mudassir ya shigo,yaja kujera ya zauna yana qarewa office din kallo sanda take kiciniyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96