Chapter 49
Chapter 49
mai neman attention dinsa,ya sakar masa murmushi sannan ya juya cikin wani irin sauri ya bude qofar office din ya fice. "Wash" shahida ta fada tana dafe kanta tare da duqawa kadan kaman mai ciwon ciki bayan fitar tashi "Subhanallah" nuradden ya fada da sauri yana nufota,da sauri ta daga masa hannu ta koma da baya ta zauna kan kujera,gabanta ya qaraso ya duqa yana tambayarta,ta nuna mishi kanta "Sannu,kiyi haquri don Allah,banzo nan da niyyar wani abu mara dadi ba,nazo ne muyi magana dake ta qarshe kuma ta fahimtar juna,bansa ya akayi duka hakan ta faru ba" "Ba komai,gida nakeson tafiya" "Muje na kaiki" ya fada cikin nuna kulawa yana miqewa,da gaske kan nata ke mata ciwlo sosai,saboda haka taja wayar office din,ta bada uzurin barin office dinta ba tare da lokacin tashi yayi ba. Cikin girmamawa rayyan ya tarbeshi,ya bashi hannu suka gaisa sannan yaja masa kujera ya zauna "Yallabai kai da kanka?,a maimakon kayi tafiyarka kawai saika tsaya bada excuse?" Murmushi anwar ya saki yana shafa kanshi dake masa ciwo "Doka ce bai kamata ace mune muke karyata ba" "Kasan yanzu tsarin ya canza,account dinka idan ya zamana kudi na yawan shiga da fita suna saka ido akanshi saboda yadda barayin gwamnati ke bude account kala kala suna aje kudaden al'umma da suka diba,qasarmu saidai addu'a kawai" "Wallahi yallabai,abubuwan kullum qara dagulewa suke,saidai fatan dacewa" hira suka shiga yi data shafesu,wanda bai jima ba sukayi sallama dash ya fito. A reception ya tadda nafisa yana kai kawo,tana ganinshi ta qaraso inda yake "Inata neman inda ka shiga...."bai amsata ba ya ciro waya da aljihunsa yayi kira yana buqatar qarin mota guda daya,sai daya kammala sannan ya dubeta "Zasu zo su daukeki,ni xan wuce inda da baqi,ki tafi da duka kayan da kika zaba babu matsala" Da ido ta bishi sanda yake takawa don ficewa daga katafaren wajen,tana mamakin sauyawarshi lokaci guda,iyaka tunaninta ka gaza ganowa,tilas ta samu waje ta zauna,lokaci lokaci tana duba lokaci gami da bin jama'ar dake kai kawo a wajen da kallo. Gefanta ta kalla kamar wadda aka baiwa umarni,take idanunta suka sauka a kanta tana takowa a hankali cikin nutsuwa nuradden na binta a baya,cak ta miqe tsaye tana ci gaba da kallonta har zuwa sanda ta fice daga ginin gaba daya,duk data ganta da wani amma sam hankalinta da zuciyarta sun kasa kwanciya,yanayin anwar daya sauya lokaci daya shi ya fado mata a rai,ko ita ya gani?,gabanta ya sake faduwa hankalinta ya tashi,itakam ta shiga uku,bata qaunar duk wani abu da zai hada anwar da shahida koda na bacin raine bare na mutunci,lallai tana buqatar qarin bayani,hakan ya sanya ta taka har zuwa reception "Sannu malam" ta fadi tana duban daya daga cikin receptionist din "Yauwa,kina da buqatar taimako ne?" Ya fada yana karantarta a nutse ganin kaman hankalinta bai jikinta,yaga kuma da wanda sukazo din tun dazun "Eh...don Allah tambaya gareni"kai ya gyada "yi tambayarki" duban hanyar da shahida tabi ta wuce tayi kaman har yanzu tana wajen sannan ta maida dubanta gareshi "Don Allah malam wannan matar data fita yanzun nan ita da wani,ma'aikaciyarku ce?" Shima qofar ya kalla sannan ya kalleta "Eh" yace yana gyada kai "Yauwa,don Allah ina take?,sannan tana da aure ne ko tayi aure?" "Kiyi haquri madam,gaskiya bama bada imformation haka kai tsaye game da duk wani ma'aikacin wannan kamfanin,idan kana buqatar ganinsa ne ka iya samunshi a nan"gyara tsaiwarta tayi,tana son sanin wani abu game da rayuwar shahidan,zataso qwarai ace a shekarun nan tayi aure kodon tabar mata anwar din ta samu nutsuwa ita kanta,ta daina fargaba kullum dare game da ita ko dawowarta rayuwarsu "Kaga ba wani abu bane,childhood friend dina ce,na jima ina nemanta ban samu ganinta ba sai yau,kuma nayi qoqarin na tareta muyi magana amma ta kubcemin bansan ina tayi ba" "Kiyi haquri doka ce ta kamfani" ba yadda batayi ba amma bata samu komai akanta ba,hakanan ta juya a sanyaye tana jaddadawa ranta dole ta sake nemo mima,tana shirin zama driban da anwar ya turo ya qaraso yayi mata magana kan ta taso su wuce,haka ta fita daga kamfanin jiki babu qwari tana danasanin rakiyar data roqi anwar yayi mata. *12:45 pm* Idanunsa qyar bisa rubutun dake kan screen din computer dinsa,ya gama tsara duk wata yarjejeniya ta kwangilar da zasu amsa,amma ya kasa fahimtar meye gyara meye daidai cikin rubutun bare ya tura,dogon tsaki yaja wanda kana ji kasan akwai abinda ke tafasa zuciya da tunzurashi,maimakon ya tura sai kawai yayi serving dinsa a draft,ya rufe cumputer da qarfi har screen din ya bada qass da alamu ya masa lahani. Miqewa yayi yakai ya kawo sau biyu tsakiyar dakin nashi,sannan ya sake juyawa ya isa bakin window din daki,ya zuge labulen gami da budesu gaba daya,iska mai sanyi irin ya daren daya soma nisa,darenma na damina ta soma shigowa,ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana kallon sama da yau tayi fresh da taurari tare da fatan zafin da yake ji cikin zuciyarsa zai samu ya ragu,runtse idanunsa yayi karo na barkatai _ina tunanin kana cikin masu sonta ko,to ka makaro,don kuwa shahida tawace,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunya ce da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi ko iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirarin ko gigin cewa yana sonta_ Kalaman nuradden suka dawo masa fes kamar ma a sannan yake furta masa su,kalaman da yau wuni sur su suka dinga qona mishi rai,suka hanashi dukkan wani sukuni da walwala,baya tunanin tsahon rayuwarsa bayan labarin mutuwar mahaifansa akwai kalaman da wani ya gaya masa da suka hanashi sukuni irin wannan,bai tabajin anci mutuncinsa ko anci masa fuska ba kamar haka "Shashasha,zaka ganne koni waye,zaka ganne qarfina isata da kuma izzata"ya fada afili zuciyarsa na yanke masa shawarar abinda ya kamata yayi. _please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,ni da kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai_ Girgiza kansa sosai yayi zuwa hagu da dama,kalaman shahida na sake amsa kuwwa cikin kunnensa,ware idanunsa yayi murmushi ya subuce masa shi kadai "Zaki fahimci cewa nidin ba qaramin dalili bane keda shashashan masoyinki"ya furta sanda yake qoqarin rufe windows din dakin jin yayyafi ya soma sauka,yanajin bai kamata ya qyale nuradden ya furta masa wadan nan kalaman ba ya kuma ci bulus,bai kamata ya qyale shahida taci gaba da rayuwarta yadda taga dama ba,yadda ta tsaida duk wani aiki na zuciyarsa ya kamata itama tata zuciyar ta tsaya,bai kamata ace zuciyarta taci gaba da aikin da har xata karbi wani a matsayin masoyi ba bayan ta quntata tashi,ta kuma barta a rufe ruf,ta sanyata ganin baqi da baiken soyayya. A nutse ya hada abincinsa yaci sosai,don ya gama yankewa kanshi shawara,kuma shawarar ta karbu dari bisa dari cikin ransa,hakanan yaji duk wani nauyi dake qirjinsa ya sauka,walwalarshi ta soma dawowa,hakan kuma yana jin bai rasa nasaba da nunawa nuradden kurensa da illar lafazin da yayi a gareshi da zaiyi. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kofin kunun hannunshi ya aje yana duban anty usaina "katsina zan wuce,ko kina da wani saqo wajensu inna?" Cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96