Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 83

Chapter 83

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,308 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

targade saboda tsabar son jiki shine zata hau sama ta nade?,oh ni habiba,yaran yanzu saidai abarsu,kamar wadda ta karye" "Yi haquri daada karki rudamin mata,kin manta ke mai laifi ce dama?" Ya fada cikin tsokana,da ido ta bishi baki sake "Iyeeee....au wato harka soma bin bayan matarka?" Murmushi ya saki sosai sannan yace "Yi haquri daadarmu,so so ne amma aisonkai yafi ko?" Kasa amsashi tayi,cikin zuciyarta tanajin sanyi da dadi na yadda ta fuskanci.yana kulawa da jikarta,ta cika da fata da addu'ar Allah yasa itama haka take masa kada ta basu kunya,kada kuma ta watsa musu qasa a ido,mubina yasa ta shiga kitchen ta hada musu abin motsa baki,sai dayaga ta shirya musu komai sannan ya zqri muqulli don zuwa ya sama musu abinci "Ku hau saman daada ku sameta kafin na dawo" "Kaga nifa ba zama zanyi ba,mai motar daya kawomu ma yana qofar gida yana jira in fito ya maidani,don yau ni kam kwanan garinmu zanyi" qememe taqi barinshi ya fita,tace saidai yahau sama ya sauko mata da shahida "Kiyi haquri daada ki hau,ba zata iya saukowa ba" "Ita sabon qashima taqi saukowa bare ni tsohon qashi za'ace nayi tattaki nahau,tunda goya mata baya kake tayita narkewa kaga tafiyarmu" daqyar ya lallaba daadan tahau saman,inda mubina da khadija sukayi xamansu nan falon suna kallo. Har yanzu tana zaune saman abun sallah a haka daada ta shigo,sai taji dadin zuwan daadan,tana ganin tazo a daidai,ita ta qulla komai saboda haka dole ta yiwa anwar magana ya barta ta koma bakin aikinta,ba yabi ba fallasa ta gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,bawani sauyi data gani tattare da shahidan na mace me aure,saita tabe baki,zata fara magana shahidan ta rigata cikin sautin wanda keson fashewa da kuka "Daada ki masa magana ya barni na koma aikina,kinga tun asali da aikina ya ganni,sannan kuma baice min bazanyi ba sai jiya da nake gaya masa zan koma yace waina gama aiki,daxun nan kan ku shigo ya dauki wayata ya ballamin layina waina daina amfani dashi" rashin sani yafi dare duhu,wani kallo daadan ke mata akaikaice,sai data gama tsaf sannan tace "Yo ai ni banga wani abun azo a gani dakika tabuka ba daxai nuna kinsan ma kina da aure,daga ke harshi banga wani sauyi tattare daku ba" "Kai anwaru" ta kira sunanshi tana zare ido,ya amsa mata ta masa nuni da kusa da shahida "Xauna nan" ba musu ya zauna yana qunshe dariya,daada sarkin rigimammu,da alama akwai magana a bakinta "Tunda kuka tare ta taba maka kwanan turaka?" Ta jeho masa tambayar kanta tsaye,take qwaqwalwarsa ta gaya masa abinda take nufi,kunya ta rugo ta rarumeshi,bai taba tunanin tambayar da zata masa kenan ba,cikin hanzari yace "Daada ai.... "Aime?,idan baka da amsa to bari na amsa maka,bata taba ba,kalli qafafunta da wuyanta,idan tace ma eh to qarya take,oh la'ilaha illallahu muhammadarasulillahi sallallahu alaihi wasallam" ta debo salati tana tafa hannuwa _afwa masu karatu,kunsan yadda sabgogi ke kutso kai cikin rayuwa_🙏🏽 *Alqawarin Allah* 39 "Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba haka taci gaba da takawa. A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye "Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama "Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?" "Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby "Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci "Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa "Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta. Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa. Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata. Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta. Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});