Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta miqe ko gabanta bata gani ta shige dakin. Wani irin tashin hankali ta tsinci kanta ciki,saitakejin kaman da wasa daadan ke mata zata dawo tace tsokanarta take,saidai har akayi magariba su faruqu suka dawo shuru daadan bata bi ta kanta ba,sanda suka dawo suma suka leqo dakin da take,dukkansu tambayarta suke me ya sameta da suka sameta a kwance,saidai ba wanda ta baiwa amsa,tana jiyo muryar daada daga falo tana cewa su fito suzo ita ta basu amsa,haka suka juya suka fita,faga haka basu sake dawowa dakin ba suma. Har qarfe goma na dare tana kwance ita daya cikin dakin cikin wani yanayi,nuradden ya jirata yafi a qirga ta kasa dagawa saboda tashin hankalin da take ji cikin zuciyarta,saida goma ta gota daadan ta shigo dakin da kanta ta taddata,ta aje kwanon abincin hannunta sannan ta samu gefan gadon da shahidan ke kai ta zauna "Tashi ki dauki abincinki kici" shuru tayi mata kaman bata ji me take cewa ba,ta sani sarai taji din,tsohon halinta keson motsawa saboda an mata zancan an bada ita "Saboda an hadaki da miji nagari za'a miki aure shine kika yiwa abinci yajin aiki?,kusan ni natsaya tsayin daka kan maganarnan saboda ganin nagartar da yaron yake dashi,sannan kuma ina da yaqinin cewa bamuyi miki zaben tumun dare ba,uwa uba nasan ko ba dade koba jima sai kinyi dariya kin godemin da irin mijin dana zaba miki" tana ganin daadan tazo gabar da zatayi magana saboda haka ta miqe ta zauna sosai tana gyara rigarta data sabule "Duk naji dada na fahimceki,amma daada ina ake irin wannan auren?,ban sanshi ba bansan waye ba,bance ina sonshi ba bani na aikoshi ba kawai sai a daukeni a bashi ni?,ta yaya za'a karbi sadakina abawa wani aurena ban sani ba?" "Saboda mun isa dake" lallabawa take ta samu a kwanceta daga tarkon da aka sakata,sabida haka tayi qasa da murya "Na sani daada,amma don Allah ina roqon alfarma ku maida masa kudinsa,nuradden ya jima yana tare dani,ya dade yana bibiyata,sannan kuma shima yana da dukkan nagartar da za'a iya baiwa mutum aure saboda ita" "Duk nagartarsa bazai kama qafar wannan ba" mamaki duka ya cika shahidan,wai waye wannan da daada ta kafe kai da fata taketa faman yabo da kodashi haka?,taqi ji taqi gani saboda shi?,ko wani cikin 'yan uwanta nanan dake qwaqwar sonta dai daadan ta baiwa ita? "Taya kika sani?,bafa sanin nuran kikayi ba?" "Eh ban sanshi ba kuma bana son na sanshi,bazamu zama qananun mutane ba magana an riga da an gamata,ki sauko ki dauki abincinki kici" daga haka daadan ta miqe tayi ficewarta,alamar dake nuna cewa ba qaramin abu bane zai saukar da ita daga kan bakanta ba. Ajiyar zuciya ta saki cikin tashin hankali idanunta na tara sababbin hawaye,ta zurafafa tunaninta tana neman dukkan hanyoyi da take ganin zati ba don sauke daada daga qudurinta,tunaninta yakai ya kawo,babu wata qofa guda daya,tunda kowa kusan da umarninta yake aiki,mafita daya ce ta dage da nacin roqonta kawai kafin nan da ranar lahadi ko Allah zaisa ta janye tun maganar batayi qarfi ta watsu a dangi ba. Ba irin tunanin da bata kawo ranta ba kafin bacci yayi awon gaba da ita. Koda ta idar da sallahr asuba wani baccin ne ya sake kwasheta,saboda rashin samun isashshen bacci da batayi na daren jiya. Cikin baccin taji kamar muryar huda na tashinta,ta bude idanunta da qyar wadanda sukayi nauyi ta zubesu kan huda "Anty shahida,kizo inji kawu ummaru" tuni ta nemi sauran baccin idanunta ta rasa shi,saita zauna dangwargwar saman gadon tana duban shahida "Yaushe yazo" "Bai jima da zuwa ba,muna cikin cin abincin safe" "Kice masa ganinan" ta fada cikin fargaba,miqewa tayi ta dauki hijabinta dake saman jakarta ta zura,ta tsaya gaban mudubi ta kalli fuskarta gabanta na faduwa,tasan halin kawu ummarun sarai,yafi kowa zafi cikin kawun nan nata,Tana dage labulen tana addu'ar Allah yasa koma da meye yazo ya zamana mai sauqi ne. Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa,shuru yadan biyo baya kafin daga bisani ya ciro kudade daga aljihunsa ya zube kusa da ita "Nasan tuni daada tayi miki bayanin cewa mun karbi kudin aure da sadakinki,to gasu,inaso nayi magana da mahaifiyarki kan meye ya dace ayi da kudin" da sauri ta dago kai tana duban kawun idanunta ya cika taf da qwalla sannan ta sauke qasa,ya karanci me takeson cewa,don tuni daada ta gaya masa "Rahama,karki wani ce zaki damu,yaron ya cancanta,banda haka babu abinda zai saka mu bashi ke,muma muna sonki fa" cikin muryar kuka tace "Kawu,wallahi bansanshi ba,bani bace na turoshi,akwai wanda muka riga mukayi alqawarin aure dashi,harma yana shirin zuwa gaidaku" murmushi kawun yayi "Rahama,indai cancanta take sa a baiwa mutum aure wannan yaron ya cancanta,matar mutum kabarinsa,Allah baiyi shi wancan din shine mijinki ba,saboda haka kiyi addu'a kawai,Allah yasa hakan shine alkhairi a gareki" kai ta sadda kawai qwalla na silalo mata,tana jin kawun harya gama maganganunshi yayi sallama dasu yayi gaba,miqewa tayi kawai ta fita daga falon zuwa tsakar gida ta wuce bandaki,ta tara ruwa tayi wanka sannan ta sake zuwa ta wuce daada zuwa daki. Cikin minti talatin ta gama shirinta gami da hada kayanta tsaf,daidai lokacin daada ta leqo dakin tana mata magana ta fito ta karya,saita ganta saqale da jaka tana shirin fitowa,binta tayi da kallo "Ke kuma meye hakan?" "Gidan zan wuce,tunda nazo na karbi saqon naki" baki ta tabe tana dubanta "Allah ya raka taki gona,dadin abundai bake kadaice jikata ba,kuma su bayau zasu tafi ba,saikin dawo" duban daadan tayi,zuciyarta na mata zafi matuqa idan ta tuna abinda suka mata,yanzu kamar ita da hankalinta da wayonta da komai amma ace an baiwa wani ita?,waninma da batasan waye ba?,tsabar qarfa qarfa kota bakinta ba'a jiba aka amsa harda sadakinsa?,ranar daurin aure kawai suke jira kenan?,saita juya da kayanta ta koma cikin daki ta zube gefan katifa,tana jin wayarta na rurin shigowar kiran nuradden amma bata da qarfin gwiwar dauka. Dole ta haqura da tafiyar sabida wani zazzafan zazzabi daya saukar mata wunin guda,ba ita ta samu sassauci ba sai washegari da safe,kafin sallar azahar ta sake shirin tafiya,wannan karo daadar bata hanasu ba,suka shirya tsaf suka wuce,saidai tafiyar bata musu dadi ba kamar yadda tayi musu a zuwansu,saboda gaba daya hankalin shahida bai kansu,sosai ta shiga tunani mai zurfi ita daya,har suka qaraci surutansu suka haqura. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kwana biyu da dawowarta tana gaban system dinta tana tura saqon daukar uzurin ba zata samu damar komawa office bakin aikinta ba anty zubaida ta shigo dakin,saita samu gefan shahidan ta zauna sanda ta gama tura saqon ta soma kashe system din,cikin qaramin lokaci gaba daya shahidan ta sauya ta wani sukurkuce kamar wadda akace an daura auren nata,ta sauya gaba daya ta auri zaman daki,duk wata hira da walwala data dawo da.ita cikin gidan yanzu ta janyeta,kamar wadda ke shirin komawa 'yar gidan jiya,anty zubaida batace da ita komai ba saidata gama ta ture computer din gefe sannan ta kira sunan shahidan,daga kai tayi tana dubanta "Yanzu shahida daga maganar karbar kudin aurenki saiki ki tsangwami kanki haka?,kina neman maida kanki 'yar gidan jiya?" Kamar mai jira sai kuwa ta soma hadiyar zuciya,idanunta suka soma yaji tare da tara qwalla,ta bude bakinta tana jin wani abu ya tokare mata wuya cikin muryar kuka tace "Haba

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});