Chapter 33
Chapter 33
wata rana da abbanta ya gayyatoshi cin abincin dare gidan. Abban da mamanta sun kammala sun bar wajen saura nafisan da tunda taji labarin zuwanshi ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta tsara kwalliya ta a mutu,sannan ta aro duk wani salo da tasan zai iya tafiya da d'a namiji,saidai kuma har ya kusa gamawa bataga ya nuna wani abu game da ita ya burgeshi ba,hakan ya sanya tayi gyaran murya "Anwar....idan ba zaka damu ba don Allah...ina da magana dakai" "Uhmm...babu damuwa ina jinki" shuru tayi na wasu mintuna sannan ta daga kanta tana dubanshi sosai "Tun ranar da Allah yasa na soma ganinka anwar Allah ya dasa min qaunarka...na rasa ta yadda zan furta maka bansa ya zan gaya maka ka gane ba,wani irin soyayyarka nakejin har cikin jinina,anwar ina fata da roqon ka soni koda rabin yadda nake sonka ne" tunda ta soma maganar ya zuba mata idanu yana jin wani abu da baisan meye ba yana taso masa,ko kusa ko alama baison yaji wannan kalmar daga bakin kowacce diya mace gani yake duk yaudara ce,ba gaskiya bane qarya ce,yatsunsa ya dinga bugawa a saman teburin kadan kadan har ita sai data tsargu da kallon da yake matan ta soma kame kamen abunyi,da qyar ya iya hada abun fada "Nafisa" ya kira sunanta a kausashe,daga kanta tayi ta dubeshi sosai jin yadda sunan nata ya fito bilhaqqi daga zuciyarsa "Inason daga yau wannan tunanin yabar qwaqwalwarki,wannan kalmar ta fita daga bakinki,ina ganin qimarki data mahaifanki,kada ki jawo abinda bazai mana kyau da dadi ba ni dake gaba daya"daga haka ya miqe ya dauki maqullan motarshi ya wuce ya barta a wajen,kuka ta saki sosai,bata taba tunanin lamarin zaizo da haka ba,tayi tsammanin yadda yake nuna kulawa a gareta kaman qanwarshi zata samu soyayyarshi ta sauqi,haka ta miqe ta shiga bedroom dinta cikin tashin hankali ta dauki wayarta ta kira mima ta zayyane mata komai "Nafisa kenan,dama ke kina tunanin samun kanshi da wuri ne,to kinyi kuskure idan ma zaki zage damtse kiyi kaman kinayi to" ta jima tana juya zantukan miman a kwanyarta,inda daga qarshe ta zage damtsen kaman yadda ta bata shawara,saidai gogan ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,yadda ya saba mu'amala da ita haka yake babu abinda ya canza,naci kuwa babu kalar wanda batayi masa ba,inda daga qarshe ma ta matsawa dadynta ya bata gurbin aiki a kamfanin,ya bata din saidai tace matsayin secretary din anwar takeso,babu musu ya bata kasancewarta diya mace diya tilo dake gareshi,anwar din bashi da bakin cewa don me?,haka ya amsheta saidai kusan ba wani aikin kirki take ba,cikin qaramin lokaci kowa ya fahimci yadda nafisan ke bala'in so da qaunar anwar din,wannan labarin shi yakai har kunnen umminta,take ta saka abban nafisan ya karbe gurbin aikin daya bata aka maida shi da wani,fada ta dinga ma nafisan kan wautar da take nunawa na nunawa namiji irin wannan zallar son bayan shi baisan tana yi ba,kuka ta dinga duk da ta bata tausayi amma sam bata nuna ba,don tana sone idan anwar zasiso nafisan ya sota don karan kanshi,ya kuma sota da datajarta ba tare data zubda qimartata ba wajen neman soyayyarshi ba a matsayinta na diya mace. Wannan karbe aikin ya bata ran nafisa matuqa,tana ganin kaman ummin nata bata sonta ne,banda haka meye aibu a nunuwa anwar soyayya da take,hakan ya sanya ta sake maida akalar shawararta dai wajen mima,inda ta bata wasu shawarwari da take ganin anwar din bai isa ya tsallakesu ba dole ya furta mata soyayya da kuma kula koda ba haka bane har zuciyarshi. Cikin sa'a kuwa a lokacin aka maka wani gagrumin ruwan sama daya sanya gidan anwar rushewa,dama yana dab da soma aikinsa ne,dalili kenan daya sanya alhj abba ya sake nemanshi ya dawo gidanshi da zama har zuwa sanda zai kammala gyara nashin,tofa,abun nema ya samu wajen nafisa,nan ta zage damtse ta shiga shigewa anwar din haiqan,har abunma yana wuce gona da iri,don takan iya zamanta bangarenshi da sunan tayashi hira har tara ko goma na dare,duk wadda kuwa akayi katari cikin yammatan dake damunshi da kira ta kira nafisan ta samu nasarar dauka hara zata dauka ranar suyi kace kace da sunan matarshi ce,hakan ya sanya ya qaranta dawowa gida da wuri,ya qirqirarma kanshi guraren zuwa saiya daida daici sanda tayi bacci,wani bin ya dace wani bin kuma ya taddata dai tana zaman jiranshi. Ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa tamkar cin qwan makauniya yasanyata amfani da shawarar mima,inda ta kwanta ciwo sosai suka hada baki da wani likita aka kaita can,ya dubata ya kuma ce lallai tana cikin damuwa ne,kuma tilas a sama mata abinda takeso idan ba haka ba za'a iya rasata. Randa ta farfado daga suman qaryarta anwar na dakin shida alhj abba da mahaifiyar nafisan,a sannan yana gefan daya gadon da babu kowa a kai yana charting da wani abokin kasuwanci da suka fara shirin saka hannun jari shi da shi su tashi nasu kamfanin,sunanshi ta soma kira wanda yaja hankalin dukkaninsu,saiya daga kai yana dubanta bayan ya amsa,ta wani lumshe idanu kaman gaske tana kallonshi,nauyin idanun alhj abba da mahifiyarta ya sanyashi barin abinda yake ya taso zuwa kusa da ita,sai ummanta tabar kujerar da take kai wanda ke gaban gadon ta masa nuni daya zauna ba musu ya zauna. Ba kunya ta kama hannunshi cikin dabara ya zame,saita saki kukan qarya "Don Allah anwar kace kana sona kaji" mummunar faduwar gaba ce ta sameshi yayi shuru yana jin yadda qirjinsa ke bugawa "Ina sonki" yayi qundun balar fada saboda ganin yadda take kuka gaban iyayenta "Zaka aureni?" Ta sake jefa masa tambayar data kusan sa jininsa hawa a take,tanason daureshi ne wato da jijiyoyin jikinsa. *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saita tuntubi wadan nan numbers* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe kyauta ne!*👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣8️⃣ Kanshi yaji yayi masa nauyi kaman an dora masa dutse,kafin ya ankara nafisa ta saki kuka tana roqonshi,dukkansu ya tabbatar hankulansu da kunnuwansu na wajen,haka yake,don dukansu fata yace ya amince,don sun yarda da hankali da nutsuwar anwar,sun tabbatar idan ya auri diyarsu ta fada hannun dako bayan ransu basa kokwanto ko shakka,saidai ta bangarin mamanta magiyar da take ta taba ranta ta kuma bata takaici "Meye haka kikeyi ne?,baki da hankali?" Cewar mamarta data matso kusa da gadon a fusace,ta rasa meye matsalar diyartata,kullum kwanan duniya cikin dorata hanya da gyara mata kurakurenta take amma a banza wai an tsikari kakkausa,cikin sauri anwar ya dakatar da maman,ko mutuwa ma tana kunyar idanun mahaifi,hakanan kara da alkunya ma wani abu ne,kuma shi alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,nafisa diyarsu ce kuma fadinma suna sonta bata baki ne,saidai su wasu irin mutane ne masu kunya kara da kawaici,wanda soyayyar dansu bata hanasu ganin gaskiya "Qyaleta mama" hakan shi ya tsaida hajiya ta koma da baya tana sauke numfashi,duban nafisan yayi sosai sannan yace "To kuma meye na kukan?,ya isa kiyi shuru kinga ba cikakkiyar lafiya ce dake ba" "Indai kanason shuru na saika yarda kanasona zaka aureni ya anwar" alhj abba ne ya soma takawa don barin dakin ganin rashin kunyar nafisan na qara gaba "Zan aureki in sha
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96