Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba. Shi dinma gaba daya saiya daina ganin 'yammatan dake kai kawo a wajen,ita kadai take gani cikin dinkin ankon da ya amshi fatarta fiye da zato,kowa idonsa cikin na dan uwanshi a haka ta qaraso,baice mata komai na sai gaban motar daya bude mata ta shige,shima ya bude sit din driver ya zauna bayan kubra 'yar anty umma ta shiga gidan baya ya tada motar. Saitake jinsu yau kaman rana ta musamman ce a wajensu,wani farinciki taji yana ratsata,ta samu kanta da addu'ar Allah ya shiga lamarinsu ya buda ma anwar din,motar tayi masa kyau qwarai da gaske kaman tashi "Wani abokina ne ya dage lallai lallai yau sai na amsheta na dana,tun tana sabuwa yamin tayi ban taba danawa ba,kinga kuma bai kamata naqi ba karya dauka wani abun ne na daban kuma" kai ta gyada yayin daya dinga satar kallonta lokaci zuwa lokaci,har bintu ta fahimta ta d'an masa tsiya,kunya ta sanya shahida daukan wani plate data gani ta saka jikin redion motar,tadan qaro volume sanda taji batajin me yake fita daga cd din,waqa ce ta hamisu breaker waqar jarumar mata,sautin waqar ya ratsa motar,kidanta ya fita sosai ta speakers din motar ya karade ko ina,har ta saka hannu zata kashe anwar ya daga mata hannu alamar ta barshi,shuru ya ratsa motar saidai gaba dayansu waqar na ratsasu ne,ji suke kaman su suke rerawa junansu,shurun yaci gaba da yi musu jagora har zuwa inda za'a gabatar da bikin. Sai daya rakata har ciki yayi mata mazauni,ya kuma gaya mata bai yadda da shiga rawa ba sannan ya fito ya dawo cikin motar ya zauna,wanda ya faka ne a bakin titi,sai yabar murfin motar a bude iska na shigowa qafarsa daya a waje. Awa guda da fara gabatar da bikin yana zaune yasa sauraren redio "Yauwa ga wani can....salamu alaikum" yaji an ambata,kanshi ya dago yana dubanta sannan ya amsa,matashiyar budurwa ce wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da d'aya,sanye cikin doguwar riga da siririn mayafi,fuskarta saye da tafkeken glass,gabanta ne yayi mummunar faduwa saboda cika mata idanu da kwarjini da yayi mata,uwa uba kyau data jima bata ganshi tattare da wani d'a namiji ba,da qyar ta tattaro miyan bakinta tace "Don Allah bawan Allah ko zaka taimaka ka duba mana motarmu?" Tayi maganar tana qare masa kallo ta cikin glass dinta,sai daya kashe redion sannan yace "Me ya sameta?"yarfar da hannu tayi cikin yauqi "toh wlh ban sani ba,ina cikin driving ta soma slow sai kuma ta tsaya gaba daya" dan jim yayi kafin ya jinjina kai ya fito daga motar ya rufeta sannan yayi gaba zuwa inda motar tata take. Tsahon wani lokaci yana qoqarin ganin ya gyara saita tashi saita sake mutuwa,saboda haka ya dago yana goge hannunsa da tsumma "Gaskiya dole sai bakanike yazo"ya fadiwa nafisa dake gefe tsaye suna qare masa kallo ita da qawarta mima "Ya salam...bari na kirashi Allah yasa yana kusa" ta ciro tsadaddar wayarta ta soma nemanshi,cikin sa'a yace yana kusa ta bashi adress din inda motar take "Idan ba damuwa ko zamu dan zauna cikin motarka kafin ya iso saboda zama a wajen ba dadi" nafisa ta fada sanda anwar ke komawa zuwa cikin tashi motar,tsayawa yayi ya waiwayo,kaman yace a'ah sai yaga mata ne bai kamata ya barsu tsaye ba,tunda motar tasu ba zasu iya zama cikinta ba,shi kuwa diya mace ako ina take yana da kishi da qoqarin kare mutunci da martabarta bakin gwargwado koda bai santa ba "Ba damuwa" ya fada yana sake yin gaba,idanu suka hada da mima ta kashe mata ido gami da sakin murmushi suka bi bayansa. Ya tsammaci duka baya zasu shiga,sai yaga mima ce kawai ta shiga bayan,nafisa ta shiga kujera mai zaman banza,sai data zauna sosai sannan ta waiwayo ta dubeshi tana murmushi "Suna na nafisa....kaifa?" "Muhammad anwar" ya bata amsa a taqaice,idanu ta lumshe "Nice name...sunan ya dace da maishi" saiya waiwayo ya dubeta kafin ya dauke kai,murmushi ta sake saki "Dan wanne anguwa ne kai?,Allah yasa ban matsanta maka ba da tambaya" kai ya jinjina sannan ya gaya mata unguwar da yake "Kai ai bamu da nisa sosai" itama tasu unguwar ta fada masa,kusan duk unguwannin nasu maqotan juna ne,shuru ne ya sake ratsa tsakani yayin data lula duniyar tunanin yadda zata sha kan anwar,don ba zata cuci kanta ba kallon farko taji anwar yayi mata,infact ma zata iya cewa ta kamu da sonshi ne kai tsaye. Isowar mechanic din shi ya katse duk wani tunaninta,hanya daya ta rage mata saboda haka ta miqa mishi wayarta "Idan ba zaka damu ba ka sakamin numberka mana,saboda nayi maka godiya" kai ya girgiza "Basai kinmin godiyar komai ba" kai ta langabe "Ya zama dole na gode maka,saboda alkhairi kayi min" baison jan zancan saboda ya gaji da surutunta,saboda haka ya amshi wayar daidai sanda shahida ke takowa zuwa inda motar take,tana iya hango komai saboda akwai haske cikin motar,mummunar faduwar gaba ta samu,saidai ta kasa hana kanta qarasawa wajen,saitaci gaba da takawa harta isa bakin motar,daidai sanda ya gama saka mata number din ta amsa tana murmushi tace "Na gode,sai gani na gaba" ja baya shahida tayi a hankali sanda nafisa ke fitowa daga gaban motar,idanunsu suka hadu dana juna,kallon kallon suka yiwa juna kafin nafisan tayi gaba mima ta rufa mata baya,binsu shahida tayi da kallo har suka bacewa ganinta cikin duhuwar wajen sannan ta dawo da dubanta ga anwar wanda sai sannan ya lura da tsaiwarta a wajen.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣1️⃣ "Wacece?,me takeyi a nan wajen?" Ta tambaya tana daga tsaye ba tare data shigo cikin motar ba "Motarsu ce ta lalace nayi qoqarin gyara musu,bata ma gyarun ba sai data kira bakinikensu" "Shine tazo kusa da kai ta zauna?,har kana amsar wayarta tana jifanka da murmushi?" "Shigo tukunna sai muyi maganar" ya fadi yana bude mata murfin motar sosai,kaita girgixa sai kawai ta juya tabar wajen idanunta cike fal da qwalla,cikin hanzari ya fito don ya cimmata saidai ina tuni ta kutsa cikin mutane ta bace masa bat,haka ya qaraci nemanta bai ganta ba,dole ya dawo gaban motar ya dinga jera mata kira amma bata daga ba. A hankali wajen ya soma yoyewa,ya sake shiga ya dubata amma kome kama da ita bai gani ba bare ita "Ya salam shahida....ya salam" ya dinga furtawa a jejjere sanda yake tuqa motar zuwa hanyar gidansu amaryan,ba qaramin tashi hankalinsa yayi ba,bai samu 'yar nutsuwa ba sai daya isa gidan yasa aka shiga aka binciko masa aka tabbatar masa ta dawo gidan nan sannan ya saki ajiyar zuciya,nan kuma ya shiga jera aiken kiranta,saidai mirsis taqi zuwa,ganin dare ya soma yi ya sanyashi haqura kan tilas yaja motar yabar unguwar,bai je gida ba sai daya soma kaiwa abokinsa matar,yace daya barta ma sai sun gama bikin don tafiya ma zaiyi ta sati guda,murmushi ya saki wanda kusan na yaqe ne,donshi kusan sam baiji dadin hawa motar ba,yana ganin kaman itace silar faruwar komai,inda ace a motar haya suka tafi shikenan nafisa ba

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});