Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,301 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani matsayi daka taka a yau,nice silar zamantowa abinda kake a yanxu,amma sakayyar da zaka yimin kenan?,ka zabi wata akaina?" "Kin gama?" Ya furta a nutse yana saurarenta,jin batace komai ba yasa ya dora "Na farko ba wani bawa daya isa ya azurta wani bawa dukkaninmu muna cine cikin taskar ubangiji,abu na biyu banyi zabe ba hakan ban fifita ba,kece wadda kika zabarwa kanki haka,ko a yanxu kika yarda da abinda nazo dashi,kika amince da cewa qaddararmu ce gaba daya ina maraba da hakan,saboda haka zabi ya rage game shiga rijiya" daga haka ya datse kiran ya aje wayar gefanshi,yadda yake tsammanin zai damu ko zaiji ciwo saiyaga duka ba haka bane,abu daya cikin daruruwan daya sanya ya kasa baiwa nafisa koda digo daya cikin dari na so ko qauna a zuciyarsa kenan,bata da lafazin magana,bata da tarbiyya yiwa kai waigi a duk sanda rai ya baci,ya godewa Allah daya sanya ya maida dukkan kudaden da kamfani da kuma alhj abba ya bashi a wancan lokacin ya zabi yaci gashin kanshi ba tarema da yasan waye yayi silar zuwanshi wajen ba,saiya dauki coffensa a hankali ya soma kurba ba tare daya ji wata gagarumar damuwa ba. Kira ya sake shigowa wayar tashi,ya dauka itace dai sai yaga anty usaina,ya amsa wayar bayan sun gaisa ga gaya masa komai ya kammala kuma jibi ne zasu miqa lefan "Shikenam babu damuwa,Allah ya nuna mana,saidai na nafisa ki ajesu wajenki,zan shigo gobe zamuyi magana" "Allah ya nuna mana" ta amsa masa. Wayarsa ya dauka yana duba jerin numbers din dake cikin wayar,kaf wayar babu number dinta,ba abun mamaki bane don yasan dama da zaman hakan,rabonshi da number dinta ta rabi wayarshi cikin xamanin da yake amfani da waya keypad,wayar da har yanzu bai rabu da ita ba,hakanan baisan dalilin qin rabuwa da ita ba,saiya koma neman number wayar sulaiman,bugu uku ya daga,suka gaisa ya gaya masa ya kaiwa daada wayar,ya shaida masa yana kusa da ita,sabida haka ya miqa mata wayar,bayan sun gaisa cikin mutunta juna sun dan taba wasa irin na jika da kaka da suke lokaci zuwa lokaci,don jin anwar din take kamar jikanta na jini "Jibi xasu miqa kayan daada,na nemi number dinta ban samu ba,ko zaki nemi wani cikin gidan a shaida masa" "Karka damu,sule nada lambar zubaida,yanzu zansa ya kirata ya gaya mata" hira suka dan qra tabawa kadan yana tsokanarta sannan sukayi sallama. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kurban coffensa idanunsa saman tv da aka ragewa volume sosai,tunani nason fisgarsa yana jefashi wata duniya can,zamanin da dukkaninsu shida shahidan keda buri da fatan mallakar junansu,zamanin da kowannensu yake kwana ya kuma tashi da marari soyayya da begen dan uwanshi,a sannan dukkan mafarkinsu da fatansu ya ta'allaqa ne akan lokacin da zasu zama mallakin juna,lokacin da dukansu shida ita quruciyarsu ta ninka ta yanzj qwarai,bai mantawa wani lokaci daya je hira suna hirar qawar shahida da aka kaiwa lefe,ganin yadda yake nuna buri da fatan yiwa shahidan lefe mai yawa na kece sa'a yasa tace "Nifa yaa anwar,basai ka takura kanka ba,nifa ba wani lefe da zakamin,ni ba kaya nakeso ba..." "Me kikeso...?" Ya fada yana tsareta da ido cikin wani salon kallo da baisan yana mata ba saboda shagwabarta data tafi dashi,yasandai cewa sanda yake kallonta din soyayyarta da qaunarta na narkewa tana sake kwaranya cikin magudanan jininsa,kallon da yake mata ya sanyata jin kunya harta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya "Kai nakeso ni" "Na sani shahida,amma kullum burina shine na daga darajar shahida cikin mata,kullum burina shahida tafi kowacce mace a duniya,indai ina dashi dole shahidana ta fita daban,kita min addu'a shahida,idan na tashi zan miki lefe irin wanda kowacce mace xatayi burinsa" idanunta ta zaro tana kallonshi "Ya anwar?,ranar kuwa zanyi bacci?,ya anwar dina yayimin kaya irin haka ranar kowacce mace saidai ta biyo bayana" "Qwarai kuwa,wannan dan qaramin bakinkin ya iya furta kalmomi masu zaqi da tsayawa a rai" dariya sukayi a tare tana kife fuskarta akan cinyarta. Yana kawowa nan wani qaramin murmushi da bai shirya ba ya subuce saman fuskarsa,saiya aje cup din,lokaci guda wani abu yayi kutse cikin farincikin daya tsinci kasa,ya soma juyawa zuwa bacin rai,da sauri ya soma furta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,saiya miqe ya dauki cup dinsa ya haura sama inda bedroom dinsa yake dashi. ***** ******* ********* "Ina kwana anty" shahida ta fada sanda take sanya kanta cikin kitchen tana daura agogon hannunta,anty zubaida ta amsa hankalinta na wajen siyayyar da akayi mata tana dubawa,sai data gama daura agogon sannan ta daga kai,turus tayi yadda taga kitchen din ga kacame da kayyaki "Anty,wadan nan kayan kuma fa?" Ajiye dan qaramin botikin butter din data duba tayi "Kayan aikin abincin masu kawo lefe ne" wani mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,duk wani dan kuzari data samu ta sauko dashi yau ya soma yin nashi waje,saita dan dafe kujerar dake kusa da ita "Lefe kuma?" Kai anty zubaida ta kada tana karantarta "Eh,jiya da dare daada ta gayamin" sai kawai ta kada kai tana qoqarin hadiye wani abu,ba tare data ce komai ba ta juya ta fice a kitchen din,ko abincin break dake saman tebur bata saurara ba ta fice daga gidan,ta samu mai adaidatanta na jiranta ta shiga ta zauna yaja suka bar gidan. Ko data isa office rufe kanta kawai tayi ba tare data bar kowa ya shigo ba,ta rasa shin kuka zatayi ko kuwa,idan tayi kuka babu mai sauraren kukanta,idan bore zata ci gaba dayi wanda zatayiwa borenma bata ganshi ba,wannan wanne irin cin zaline anwar ya shiryawa rayuwarta?,me yasa zai bibiyi rayuwarta da irin wannan sakamakon na daban,tunda bai ra'ayinta ya barta tayi rayuwarta cikin salama,irin rayuwar da zata samu nutsuwa mana,saiya shigo don ya rusata?,ya rusa dukkan walwala da farincikin data jima tana tattalinsu da rainonsu?. Kusan haka ta wuni cikin kamfanin babu cikakkiyar madafa ko mafita,don haka suna tashi ta yanke shawarar zuwa gida,donkarta koma ma ta tadda su anty zubaida na aikin kayan masu kawo lefe,lefen da takeji kamar ta cinnawa mai lefen da lefan kanshi wuta.*AA* 3️⃣2️⃣ Sallama tayi a tsakar gidansu,khadija dake qofar kitchen tana tankadewa umma dake cikin kitchen garin tuwo ta amsa,a matuqar kasalance kamar wadda tayi aikin shekara ta tsaya da qofar kitchen din tana gaida umman,ta waiwayo ta dubeta sannan ta amsa tana karantar yanayinta,khadija na gaidata ta amsa mata tana shigewa falonsu,jakarta ta aje waje daya sannan ta cire mayafinta ta dora akai,ta samu daya daga cikin kujerun falon ta kwanta tana sauke numfashi a hsnkali,saita tashi ta sake qaro gudun fankar dake sama tana juyawa ta sake dawowa ta kwanta a riginginen dai,haka kawai zuciyarta tayi wani rauni,hawaye ya soma bin kumatunta yana zirarowa gefan fuskarta,ta dinga shareshi akai akai,duk sanda ta tuna anwar zata aura sai taji zuciyarta ta quntata,a ganinta bata dace dashi ba,bata cancanci mutum kamarsa ba,tunda a baya ya iya guje mata a gaba babu abinda zai hanashi aikata hakan,bugu da qarima gaba daya auren manufa zaiyi da ita,yayi ne don kawai ya rusa walwalarta ya rabata da nuradden. Umman ta dan jima tana kallonta ba tare data sani ba kafin tatako zuwa cikin falon,ta samu kujera daya ta zauna sai a sannan shahidan ta ganta,miqewa tayi daga kwanciyar kuka na balle mata sosai,baki

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});