Chapter 5
Chapter 5
ya fuskanci kamar bata cikin ainihin nutsuwarta,kai kawai ta iya gyadawa "Kiyi haquri idan na takurakin,na kasa jurewa ne,na kira wayarki yafi sau nawa bakya picking,naje gida nemanki na bada saqo amma banga respond ba" ya fada yana tsagaitawa da maganar don ya bata damar cewa wani abu,duk da bashi da yaqinin zata amsa din,tsahon zamanshi da shahida duk daba wani dogon lokaci can suka dauka ba,zai iya qayyade adadin kalmomin bakinta daya ji,ko dama can tun asalin shahida mutum ce mai qaranta magana qwarai,bata da yawan surutu,tafi ganewa zaman shuru da kad'aita. Ason ranshi ta shiga gaban motarshi ta zauna suyi hira sosai da ita,saidai yasan hakan bamai yiwuwa bane,ko a yanzu daya zo yayi shahadar quda ne kawai,don bai tsammaci fitowar tata ba "Ko zamu qarasa can ki samu ki xauna karki qosa da tsaiwar" yayi qarfin halin fada yana nuna wani dakali dake qofar gidan nasu gab da qofar shiga zaurensu,a nutse ta daga jigatattun idanunta ta kalli bigiren da yake nunawar,kasancewar akwai wadatar hasken wutar lantarki taga wajen sosai,idanunta ta lumshe wani abu na takore mata wuya,kallon wajen a koda yaushe yakan tuna mata dashi,abinda bata da muradi ko kadan,kai ta girgiza cikin qarfin hali tace "Nan ma ya isa,don ina saurine zan wuce gida dare yana yi" cikin zumudin da yake yunqurin boyewa ya muskuta kad'an "To idan babu damuwa me zai hana ki shigo saina saukeki?" Hannunta saman wuyanta kamar wadda ke taba yanayin zafin jikinta,duk da tana jin kamar zazzabin ne ke shirin kamata tace "Babu buqatar hakan.....zan iya komawa ciki?" Kafin yakai ga bata amsa tuni har ta soma tattaki,kasa cewa komai yayi yana kallonta harta shige cikin gidan. Sit din driver ya koma ya zauna cikin matuqar kasala da mutuwar jiki,zazzafar ajiyar zuciya ya saki gami da furzo iska mai zafi daga bakinsa,kallon kansa ya shiga yi a madubi,haryau bai gano wani naqasu tattare dashi ba ko makusa daya sanya shahida ta kasa sakewa dashi,iya kyau Allah ya baiwa noraddeen kyau,kudi aji da nasaba,baisan wacce hanya zaya bi ya shawo kan shahida ba,da yana da masaniya kan hanyar da babu shakka yabi ko don ya mallaketa zuciyarsa ta huta da abinda take ji,sai daya kusa a qalla mintuna goma kafin ya iya miqa hannu yaja murfin motar ya rufe ya tadata yabar layin. Bakwai taso barin gidan,amma ba ita ta tafi ba sai qarfe tara,sai data tabbatar ta kwantarwa da ummantata hankali duk da tata duniyar a rude take,haka ta shirya tayi sallama da qannenta ta wuce gida. πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ Sannu a hankali yake takowa cikin gidan saman shinfidadden marbles daya malale ilahirin gidan,hannunshi d'aya soke a aljihun wandonsa yayin da daya yake riqe da wayarshi da yake amsa kiran daya shigo masa,ya jima tsaye tsakiyar qawataccen falon yana amsa wayar kafin daga bisani yayi sallama da wanda suke wayar ya soma qoqarin shiga akwatin tura saqonni. "Ka iso kenan?" Cewar wata farar mace data fito daga daya daga cikin qofofin dake jere a falon,shekarunta na haihuwa a qalla zasu doshi arba'in da biyar,tana sanye da atamfa wadda tayi matuqar yi mata kyau,a kallon farko idan kayi mata zaka ga kama ta zahiri tsakaninta da anwar,saidai banbancin launin fata,wanda shi tashi fatar choculet colour ce wato wankan tarwada mai kyau,yayin da tata fatar ta kasance fara ce duk da ba irin farin nan can can ba,anty usaina kenan 'yar uwa daya tak data ragewa anwar a duniya,kanshi ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar yana amsa mata da eh,lokaci guda kuma shima yana yiwa kanshi gurin xama kan daya daga cikin kujerun. Second goma ya qara ya aje wayar gefanshi sannan ya dago yana gaidata,ta amsa tana tambayarsa yanayin aikin da iyalin gidan alhj sambo,ya amsa mata da duk lafiya kowa yake "Ina duka yaran?,suna makaranta ko?" "Eh ai yau tun bakwai suka wuce,saboda anata shirye shiryen zuwanka,duk sai murna suke suce malaman sun shirya abubuwa da yawa" murmushi kawai ya saki,donshi karan kansa yakanji dadi a duk sanda ya tsinci kansa cikin daya daga cikin makarantun daya gina da kansu yaran al'umma kuma ke amfana da hakan,goshinsa yadan shafa kadan sannan yace "Naji kince nazo anty,Allah yasa dai lafiya" zamanta ta dan gyara sannan tace "Lafiya lau,kan maganarka ce da nafisa.....naji kayi shuru,yarinyar ta qagu,kuma nima ina kuma tsoron halayyarku ta maza,musamman kai da ludayinka ke kan dawo,kada ya zamana wani abu da zai sauya ra'ayinka ya gitta,ina tsoron faruwar hakan kodan halaccin mahaifinta a gareka" shuru ya ratsa na wani dan lokaci kafin daga bisani yace "Kawai dai ta kasa sama ranta nutsuwa ne,kishinta yayi yawa,kinfi kowa sanin halayyata anty,so banga abun d'aga hankali ba,komai na rayuwa idan aka bishi da tsari saiyafi bada ma'ana,ina sane kuma sauran wasu 'yan lokuta kadan akai gabar data dace nayi magana" kai take jinjinawa,tunba yauba tafi kowa sanin halin qannin nata,idan yace yes wuya ko rintsi basa sauyashi,hakanan idan yace no to ya bari kenan har abada,bata taba ganin abinda yace A'ah ba daga baya kuma yazo yayi accepting dinsa "Shikenan,zan mata bayani,Allah ya dafa mana" bai amsa ba ya shigar da wata tambayar "Zuwa tayi ta sameki?" Ya tambayi anty usaina yana dubanta,tasan halayyarshi tasan meye baiso da wanda yakeso saboda haka ta kada kai "Wannan ba abinda ya shafeka bane.....ga abun kari can ko zaka karya kafin ka wuce,tunda baka aje mai maka ba" siririn murmushi ya saki kawai yana shafa kansa,sannan ya miqe suka jera da antin zuwa dining suna hirarsu ta zumunci. "Har yau baku manta baya ba,gargajiyarku tana tare daku" anwar ya fada yana kallom coolers din abincin dake saman dining din,duk da baisan meye a ciki ba amma ya sani cima ce irinta bahaushe ba kayan ciye ciye na bature ba,murmushi anty usaina tayi "Laifin abbansu,yace manta baua butulci ne" murmushi kawai yayi yana kada kai,ko shi dinma ya fada ne kawai don ya tsokaneta,amma bashi da cima data wuce irin tasu wadda aka gada kaka da kakanni,sam ciye ciye zamani ba kasafai suke burgeshi ba,yakan ci lokaci zuwa lokaci amma ba komai da komai ba. Tunda ta fara zuba abincin hankalinsa yaji yayi matuqar tashi,duk lokaci haka duk a inda yaga wannan cimar saiya tuna da ita,cimar da a baya bashi da sama da ita musamman da safe,cimar da take burgeshi a baya,take rubuce cikin kundin abubuwan daya fiso,kunun gyada ne lafiyayye da yasha madara,sai qosai lafiyayye shima daya ji attaruhu da albasa ya bugu yayi luhu luhu kamar an saka masa qwai. Tsam ya miqe ba tare daya ce da anty usaina komai ba ya soma sauka daga wajen "A'ah,ina kuma zaka?" Ta tsaida abinda take ta bishi da kallo bayan ta tambayeshi "Na qoshi anty zan wuce office ne na tuna ana jirana" maida kanta tayi tana duban kunu da qosan dake gabanta,saita sake daga kai tana dubansa sanda yake daukar wayarshi daya aje a hannun kujera dazu,ko bai waiwayo ba,ko baice mata komai ba ta fuskanci me ya faru cikin 'yan sakannin,cikin hanzari ta aje plate ta sauko,ta cimmasa sanda yake niyyar bude qofar falon don ya fice ta dakatar dashi "Anya ko anwar anya?,har yanzu dai babu wani da zai sauya?,abun har yakai tsananin haka a zuciyarka?,anya ko wannan butulci ne kayi mata ko adalci?" Take idanunsa suka kada cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96