Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 81

Chapter 81

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,301 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai daya diba wani yayi guzuri ya haura sama dashi. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Bayan ta idar da sallar asuba bata koma ba ta soma gyara dakinta,sannan ta fito falo,ga zatonta zata dauki fulasan abincin kamar yadda ta saba kowanne lokaci amma saita tarar anci fiye da rabin abincin,harara kwanukan abincin tayi kaman su suka mata laifi "Dan rainin hankali,nina kwana ina baqinciki,shi kuma ashe zuwa yayi ya cika cikinsa,bacin raina dadi ma kenan yake masa,bai taba cin abincina ba sai yau daya fuskanci a bacin rai nake kenan,aikuwa bazan yadda ba nima" da wannan tunanin ta gama komai na gidan,ta kuma shirya abincin safe ta jera yadda ta saba sannan ta shiga wanka. Tara saura ta gama komai,ta shirya tsaf cikin laffaya data nade jikinta fes da ita,qafarta sanye take da takalmi me tsinin dunduniya,ba qaramin kyau tayi ba,kana kallonta kasan sabuwar amarya ce. Tana tsaue bakin dining tana break don ko zama batasonyi bare ta makara taji takun takalmi da alama ana saukowa ne daga sama,tasan shine don haka taqi daga kanta bare ta dubeshi,daga saman step din ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,tana nufin fita kenan zatayi da gaske?,a ina shahida ta sauyo hali ta koyi musu da kafiya?,bari ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta,dole ya nuna mata shine mijin itace matar,zata ga qarfin qwanji yau kuwa idan batayi wasa ba. Bai qara taku daya ba yana tsaye yana kallonta harta gama,ta ciro paper daga jakarta tayi rubutu ta ninke ta aje anan sannan ta tattara jakarta ta zuge ta riqe a hannunta ta soma takawa don ficewa. *Alqawarin Allah* 39 "Karki kuskura ki fita" ya fada yana daga tsayen yana dubanta,kamarma bada ita yake ba haka taci gaba da takawa. A nutse ya gama saukowa sannan ya saka hanzari irin na ingarman namiji,kafin kace meye wannan ya cimmata,yasa hannu ya maida murfin qofat falon ya rufe idanunshi cikin nata ya bata umarni kai tsaye "Wuce ki koma ciki" dubansa tayi itama "Kaman yaya?,bayan na gaya maka tun jiya aiko?" "Ki koma ciki kawai nace" saita dubeshi na tsahon minti daya,ta karanci da gaske yake,ita kuma na zata yarda yaga lagonta ba bare yaci gaba da sanyata yin abinda batayi niyya ba kuma bata shirya ba,saita sake dora hannunta kan handle din qofar da niyyar budewa,caraf ya riqe hannun nata,tana shirin masa tsiwar ya saketa bata ankara ba taji an sureta gaba daya daga ita hat jakar hannun tata,ya juya ya soma taka matakalar da zata sadashi da sama,sosai ta soma qoqarin zillewa ranta na quna na yadda ya maidata kaman wata karmami,ya dagata ba komai bane a wajensa kamar ba mutum ba?,sai kace wata 'yar baby "Meye haka ne?,ka saukeni don Allah bana son irin haka,ka saukeni,ka saukeni bana so" abinda ta dinga fada kenan tana qoqarin qwacewa daga daga hannunsa,baiko bi ta kanta ba hakanan bai fasa hawa saman ba har sai daya dangane da bedroom dinsa sannan ya cillata saman lallausan gadonshi yana maida numfashi,fuskarshi a daure,ranshi a matuqar bace wanda ko ba'a gaya maka ba zaka fuskanci haka ta idanunsa da suka soma sauya kala,nunata yayi da yatsa cikin bambami dake nuna ranshi ya baci "Na fuskanci cewa sassauci na yana neman kawo raini a tsakaninmu,barinki kiyi yadda kikeso yasa kikejin kece mijin nine matar ko?,to daga yau komai zai sauya,zaki gane wane shugaba tsakanin ni da ke" daga haka ya maida muqullin dakin ya rufesu shida ita gaba daya,cikin hanzari take saukowa daga saman gadon nashi tana cewa "Ka budemin qofa,ya zaka rufeni anan,wai me yasa ka fiya son kanka ne da yawa?,me yasa kake zalunt...." Maganar tata ce ta katse sakamakon yadda ta sauko qafafunta qasa da hanzari da cogenta,sai akayi rashin sa'a qafar tata ta turgude da tsinin takalminta,maimakon ta qarasa maganar da take saita buge da sakin qara,ta koma tayi zaman dole bakin gadon tana duba qafarta. Towel din dayake daukowa ya rataya a wuyanshi sannan ya waiwayo yaga me ya sakata yin qarar,idanunsa ya sauka a qafarta da take dafe da ita,a hankali ya qarasa ya duqa gabanta,ya saka hannu zai taba qafar ta janyeta baya da sauri tana ci gaba da dafe wajen,ya gane me take nufi,tana nufin batason ya taba nata qafa kenan,saboda haka ya qyaleta ya juya abinshi yayi shigewarsa wankansa. Azabar data dinga ji cikin qafar ya tabbatar mata mawuyacine idan ba targade tayi ba,batasan ya zatayi da qafar taya ba,hakanan ita daua cikin dakin ta dinga dafe qafar tana jin zugi na ratsata. Sai daya kwashe awa guda cur sannan ya fito,a shiryensa kaman ba shine ya shiga wanka da towel da jallabiya ba,ya isa gaban mudubi ya dauki turarukansa ya fesa,ta cikin madubin yaje dan kallonta yadda ta soma hada gumi,tuni harta cire yafen lafayar jikinta,idanunsa ya sauka kan lallausar t.shirt din dake jikinta fara sol mai dogon hannu da rufaffen wuya,wadda ta lafe sosai a jikinta ta fidda shape din albarkatun qirjinta,saiya dauke idanunsa daga kanta da sauri,ya gama fesa turarensa ya taje kansa sannan ya juya ya sake takawa inda take ya tsugunna gabanta karo na biyu,zata sake janye qafar yayi caraf ya riqeta sosai,ta saki ihun azaba sanda ya gama zare takalmin ya soma mammatsata,take ya gane targade ne,ya kuma gamo wajen,sai daya faki numfashinta ya kama wajen sosai wanda babu shiri ta qwalla wata irin qara tana qoqarin tureshi,saidai ko gezau baiyi na yaci gaba da gyara wajen,tun tana masa masifa tana jin girman kan ta roqeshi ya qyaleta harta soma roqon nashi tana hadashi da Allah,ta hada gumi jagaf kafin ya gama,yana sakinta ta saki ajiyar zuciya,sai kuka ya qwace mata,dama zuciyar na akusa,gani take kaman yana sane ya taba ciwon da yawa yayine kawai saboda mugunta. Baiko dubeta ya juya ya isa bakin qofa yabude zai fice,taso yunqurawa ta miqe ta bishi a baya da hanzari ko xata samu nasarar ficewa amma ina babu damar ta taka qafar,tana kallo yaja qofar,saidai wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye. Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta. Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane. A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara "Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});