Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,314 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Allah wulaqanta dan adam ba dabi'arta bace,zatafi kowa farinciki idan har noraddeen ya janye daga qudurinsa daga kanta,ga sabanin tunaninta sai taga ya saki murmushi "Bani da damuwa shahida,nasan cewa mahaqurci mawadaci,zan iya jure koma meye indai a kanki ne shahida" idanunta ta lumshe tana jin kamar jiri zaya kada ta,a rayuwa yanzu babu abinda ke damunta sama da matsalar nuradden,ya soma shiga jiki da zuciyar makusantanta,bata da buqatar a yanzu dukkan abinda zai kuma d'aga ma rayuwarta hankali. "Koma meye tabbas mai wucewa ne watan wata rana" furucin nuradden ya sake ratsa dodon kunnenta,a sanda take kiciniyar dai daita kanta "Don Allah.....shahida inason ki bani dama,ki saurareni koda wayata ce kadai ki dinga dagawa,bazan takuraki kan koda yaushe saikin fito na ganki ba,amma ki daga wayata,hakan kadai ya isarmin....don Allah" ya fada yana hade hannayensa waje d'aya alamar roqo "Naji ya isa,ka sameni ta wayar" ta fada tana juyawa don ta shige gida kamar wadda take kan qaya ko wuta "Tsaya mana shahida....." Yayi hanzarin fada,tsayawa tayi cak kamar yadda ya umarta,saidai bata waiwayo ba a haka ya cimmata,gabanta yasha,yana murmushi ya miqa mata wata leda "Ga wannan,ki karba don Allah....." Batason doguwar magana saboda haka ta saka hannu ta amsa kawai ta shigeshi,kallo ya bita dashi yana jin dad'i cikin ranshi,yau an samu wani ci gaba da har shahida karo na farko ta amshi abun hannunsa,tabbas watarana yana saka ran komai zai wuce,bai taba tsammatar tsintar kanshi cikin soyayya makamanciyar wannan ba,saidai shahida ta cancanci komai,tana da nutsuwa tana da hankali uwa uba kyau,shahidan tayi masa,tako ina ta amsa sunan irin macen da yakeso,yake da burin mallaka,macen da cikin dubu sai an duba. Tana shiga a nan falo ta ajewa huda ledar,tace ta dauka ta bata,tana jin huda na tsallen murna da kacaniyar bude ledar tawuce dakinta ta hau sabgar gabanta,duk don ta yakice komai,wanka ta soma yi,sannan ta jawo plate din abincin data shigo dashi daxu sanda zata fita wajen nuraddeen din ta soma tsakurar abincin ciki,ci take kawai,amma ko za'a rutsata da bindiga batasan wanne taste ke ga abincin ba,tana cusa wa ne kawai maganin yunwa,duk sanda taji irin wannan yanayin tattare da ita tasan cewa can cikin zuciyarta ba lafiya qalau take ba,ta hanata kanta dukkan wani tunani,ta bude jakar makarantarta ta dauko exams din dalibanta ta shiga marking tana shigarwa cikin paper din dake dauke da sunayensu. Tana tsaka da haka wayarta dake aje can gefe ta soma haske,don dama abadan wayarta a silent take,batason wani qwaqwwaran motsi da xai dameta,daga kai ta dubeta,kamar ba zata daga ba saita miqe tsam tace ta duba,anty amina sunan dake yawo saman screen din kenan,dan qaramin murmushi ta saki wanda bai bayyana ba koda saman fuskarta ba bare mutum ya gane,saida ta bari wayar ta katse da kanta sannan tabi kiran "Ranki ya dade yallabiya,don naga alama kin xama hukuma saida lallashi,kinbar rayuwar kowa bare ki nemeshi ko?" Wani murmushin ta kuma saki wanda yafi ja daxu armashi fa bayyana,sai data koma ta zauna inda ta tashi sannan tace "Ni na isa,ta yaya zan manta da anty amina ta?" Ta fada tana tura hular kanta zuwa baya,hakan saiya qara fidda kyanta,sakamakon gashinta mai santsi daya bayyana "Gashi kuwa?,kin d'aura aniyar mantawa dani din?,anya duniya da amana kuwa shahida?" Duk sai komai ya tsaye mata cak,duk da cewa gaskiya anty aminan ta fada,abinda bata sani ba tana gujewa kiranta ko haduwa da itane,saboda tana daga cikin abubuwan dake tuna mata baya,wanda take ra yaqi shafe komai shekara da shekaru "Yanzu dai ayimin afuww,inayini anty amina mun yini lpy?"ta fadi tana kada biron dake hannunta hagu da dama "Lpy alhmdlh....ya gida?" "Lpy qalau muke,ina yarana?" "Yaranki duka sunyi fushi" murmushi ta sake saki "Suyimin afuwa,ina nan zuwa,zuwan ba zata" "Haka dai,kullum maganar kenan,fafur kin qimu kin gujemu,na rasa ma LAIFIN NA WAYE?" jin anty aminar nason fadawa wani bigiren na daban ya sanyata soko wata hirar don kauda waccar maganar "Zan baku mamaki anty amina,kedai ki sharen hanya" "Yo sharar hanya kuma ta nawa,na share na share har na gaji,kedai sai an ganki kawai" sai ta miqawa yaran nata wayar suka shiga gaisawa d'ai d'ai da d'ai,su dinma bikonta sukeyi duk tace musu tana nan zuwa susha kuruminsu,daga bisani suka miqawa mamarsu wayar suka dan sake tattaunawa sannan sukayi sallama da juna. Tana shirin aje wayar wani kiran ya sake shigowa,anty zubaida ce take kiranta "Ki sameni a falo" ta fada kawai ta yanke kiran,saita sauke wayar daga kunnenta tana miqewa tsaye ta gyara daurin zaninta,tana zura hijabinta wayar ta sake haske,nuradden ne ke kira saita dauke kai ta qarasa saita hijabin nata ta fice a falon. Abbi anty zubaida da huda ne zaune gaban kwanukan abincin,kamar yadda al'adar abbi take bai hawa dining saidai a sauke masa abinci a qasa a shimfida masa table mat,yanzun ma abincin suke ci,ta qarasa cikin nutsuwa ta zauna gefan huda tana gida abbun,ya amsa mata fuska a sake kamar kullum yana tambayarta dalibai,murmushi tayi ta sani sarai baison koyarwar da take ko kad'an,amma ya haqura ya bata damarta don baison ya tauyeta ko ya hanata abinda ta zabawa kanta,duk da cewa tana koyarwa ne bisa wani sharadi da bata tunanin ma akwai randa sharadin zai gindaya yayi sababin afkuwar barinta makarantar "Wannan kayan da kika baiwa huda fa?" Cewar anty zubaida tana nuna ledar da baki,waiwaya tayi yana duban ledar don sam ta mance ma tayi kyautarta,kunya ce ta dan kamata ganin kayan da suke ciki,katuna ne masu dauke da kalaman soyayya sai sauran tarkacen kaya da suka shafi masoya,idan ma akwai abinda ya shafi huda a ciki bai wuce choculet masu tsada dake ciki ba,dan satar kallon uncle abbu tayi taga shi sam hankalinshi ma ba'a kansu yake ba,saita maida wajen antyn "Ki cire mata choculets din saiki ajemin sauran kayan" "Eh da yake ni aka bawa ko?,to tattara kayanki ki bar wajen dasu tun ban gayawa abbu abinda kike yi ba" da hanzari ta miqe tana miqawa anty zubaidan ban haquri da ido,haka ta tattare kayan tana jin kamar ta watsar dasu a wajen "Yaushe zakuyi hutu ne khadija?,inason wannan karon kuje kankia kuyiwa su dada hutu,tanata qorafin kin yada su gaba daya bakya ta tasu" "Kwana uku ya rage,donma sun tsaya jiran zuwan mai makarantar ne" "Na qagu abbu ranar tazo wallahi...." Cewar huda cikin zumudi,waiwaya shahida tayi tana duban hudan,batasan me yasa take yawan zumudi da zuwan mutumin da kowa yake masa shaidar baida sauqi ko rangwame ba,kamar anty zubaida tasan tadin me take a ranta tace "Oh hudaaaa...irin wannan zumudi kullum zancanki kenan?" "Ummi....yana da kirki wallahi,yanasonmu,idan yazo kowa sai an bashi chaculets masu dadi da biscuits manya manya" "Sarkin kwadayi...." Abbu ya fada yana lakuce mata baki,dariya sukayi gaba daya "Ina tunanin randa zakuyi hutu ranar su faruq zasu dawo suma" abbu ya fadi yana zuba lemo a cup,shahida dake niyyar barin falon ta dakata,fuskarta qunshe da murmushin data kan jima bata yi ba,tayi kewarsu sosai,duk sanda suka koma makaranta gidan baya mata dadi,tace "Abbu amma baka gaya mana ba sai yau?" Dubanta yayi,yana mamakin shaquwarsu "Eh,saiku hanamu sakat da shirin zuwansu,kaman su kadai ne mutane a gidan" ya qarashe zancan nasa yana duban anty zubaida,tasan sarai su yake tsokana ita da shahida,don haka ta dauke

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});