Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wannan karon bai rufeta ba,abinda ya sanyata sakin ajiyar zuciya kenan,ta maida kanta jikin filo ta jinginar tana lumshe jiqaqqun idanunta da duka jiqe da ruwan hawaye. Tun tana sauke ajiyar zuciya tana shaqar qamshinsa daya kama dakin har bacci ya soma fisgarta,ta dinga dagewa don bata son yin bacci saman gadonshi amma ina yafi qarfinta. Qarfe biyu na rana ya sake dawowa saman,duka yau ba inda ya fita,duk da yaso yayi fitarsa ya qyaleta amma saiya kasa,sanin cewa mawuyacine ta iya tabuka komai saboda targaden data ji din ba kadan bane. A hankali ya turo qofar dakin,yayi tsammanin samunta zaune,sabanin hakan saiya sameta a kwance a rigingine tana bacci sosai,ya qarasa a hankali ya tsaya kanta hannunsa rungume a qirji ya zuba mata ido,irin kallon daya jima baiyi mata irinsa ba,abubuwa biyu na kokawa cikin zuciyarsa,ya samu ya kauda su,ya isa gefan kanta yadan bubbuga filon da take kai a hankali,bude idanunta tayi sannu sannu,saita tuna inda take,saboda haka ya ware idanun nata da sauri gami da miqewa zaune sosai tana masa wani kallo da yafi kama da harara "Ki tashi ki sallah" ya fada yana aje mata takeaway,sannan ya goya hannunsa a baya ya tsaya yana kallon yadda take kokawar miqewa cikin dabara,da alama tana shan zafi amma taqi nemon taimakonsa,data gaji da kanta ta koma ta zauna tana lumshe ido saboda zafin da wajen yake mata,gami da sauke numfashi "Ki tashi na taimaka miki badon halinki ba" "Banaso" ta fada da hanzari,sai ya daga kafadunsa alamun bai damu ba ya soma takawa zai fice,ta kalli agogo ta tabbatar idan ya fita da matsala,lokaci zai iya qwace mata,ita kuma idan tace zata tashi da kanta zata sha wahala,saboda haka kaman wadda aka yiwa dole tace "Dawo ka tayani,amma karka soma tabamin jiki don zaka rakani alwala" "Riqe jikinki na riqe taimakona" ya bata amsa sanda ya tura qofar kamar xai fita,tana kallo ya sake ficewa,sai wani abu ya tokare mata maqoshi,ita zaiwa wulaqanci?. Sau uku tana gwada takawar amma zafi da tsoro ya hanata,dole ta koma ya zauna tana kallo lokacin sallah na sake wuceta,baqinciki kamar tayi yaya. Turo qofar da aka sakeyi yasata daga kanta,shine dai ya sake dawowa dauke da wata roba dake fidda tururin ruwan zafi,hannunsa dayan riqe da towel,gabanta ya iso saitin qafar ya aje robar sannan ya jawo wani qaramin qawataccen stool dan gajere ya dora robar akai,bai kalleta ba ya kama qafar ya dora saman robar,zafi yasa ta saki 'yar qaramar qara zata riqe hannunsa sai kuma tayi saurin janyewa,tana ji ya dinga tsoma towel din yana matsewa gami da danna mata wurin,tun tana jin ciwo harya soma sake mata,radadin ya ragu,tunda ya soma aikin bai daga kai ya dubeta ba,lokaci lokaci idanunta kan fada kansa ba tare data shirya ba,amma ko sau daya taci sa'a basu hada ido ba,tsahon mintuna sannan ya miqe ya dauki towel da robar ya fice dasu. Sake gwada miqewar tayi wannan karon saita dan taku,a daddafe ta samu ta tura qofar da zata sadaka da falonshi don dakinta takeson tafiya,sam bata qaunar zaman dakin nasa,a bakin qofar falon wadda zata sadaka da matattakalar benan suka kusa karo yana dawowa tana shirin sauka,fuskarnan a tsuke kaman baisan meye dariya ba yace "Ina zaki haka?" "Inda nafi wayo" ta amsashi tana duban ta inda zata rabashi ta wuce "Koma ba inda zaki,kin dawo nan kenan harsai kin gane kece matar nice mijin,don na fuskanci baki banbance tazarar dake tsakaninmu ba" wani kallonsa tayi "Ba inda zan koma,dakina xan koma" girarshi ya dage "Ashe?,tunda kin yarda dakinki ne can ashe nine mai gidan ko?" "Oho?" Tace tana juya masa baya gami da turo baki,anwar din yakai mata ko ina,ya soma quret,ta fuskanci duk abinda zaiyi ya qureta ya iya,saita soma qoqarin rabeshi,qyaleta yayi harsai data raba tsakiyarsa sannan ya cukukikuyeta gaba daya cikin qirjinsa ya mata wani kyakkyawan ruqo,karon farko shida ita a rayuwarsu,ihu ta saki kaman wadda taga abun tsoro tana qoqarin qwacewa,daukarta yayi cak kamar yadda ya saba mata,abinda tafi tsana kenan,saboda idan yayi hakan gani take kaman ya raina mata wayo,bai sauketa ko ina ba bandaki,ya ajeta saman toilet sit,ta bude baki zatayi magana yasa yatsa ya dalle mata bakin gami da cewa "Shshshs,karki sake ki mana surutu a bandaki" yana maganar yana zaro ido kaman wanda yakewa qaramin yaro,bacin rai ya hanata magana,saita qyaleshi tana kallonsa ya daura mata alwalar,zai sake sungumota ya fito da ita ta zille,ta tashi tana dingisawa ta fito,fafur taqi zama a bedroom dinsa sai a falo,a nan tayi sallarta. Daidai sanda ta idar wayarta tayi tsuwwa,lokaci daya idanunsu suka sauka kan jakar,ya rigata saka hannu ya dauki jakar ya zuge ya ciro wayar,zai daga ta dubeshi "Karka daga min waya,bani abata" fuska a tsuke ya daga kai daga daga wayar da yayi niyya yi "Saboda baki da gaskiya?" Saita ware ido tana kallonshi "Eh bani da gaskiyar,duk abinda zakace kace,ka fadima abinda yafi hakan idan kaso,bakinka rayuwarka kuma zuciyarka ba tawa ba" ta qarashe cikin hasala,yana tsaye cak yana kallonta saiya saki murmushi ya dauke idanunsa daga kanta "Ko baki fada ba dama ai haka yake,dama ai zuciyata ce ba taki ba,haka rayuwata vata taba zama taki ba ki rubuta ki aje" daga haka ya daga wayar ya kara a kunnesa,hakanan taji kalaman sun samata ciwo,saita jefa masa harara ta dauke kanta wani sashe daban "Lpy qalau....eh,to" kawai taji ya fada ya latse wayar,yana shirin maidata wayar jakar aka sake kira "Triple R company" ya furta a fili,ta waiwayo da sauri ta dubeshi,da alama kira ne daga kamfaninsu,saita samu kanta tana addu'ar Allah yasa ba daga cikin maza abokan aikinta bane,bata gama wannan tunanin ba tajishi yana bada amsa "Maigidanta zaishigo ya samu boss dinku,zamuyi magana dashi" daga haka itama ya yanke wayar,tana kallo ya juya wajen da layi yake ya ciroshi,ya fidda layin saiya soma lanqwasashi "Karka karyamin layina" ta fada cikin hanzari,saidai ina tuni ya karyashin ya watsashi cikin dan qaramin abun sharar dake kusa dasu sannan ya dubeta "Namiji ne ya kiraki yana tambayar ba'asin rashin zuwanki aiki yau,baisan kina da aure ba?,ko baya ga haka dole ki rabu da wannan layin,bazan lamunci kici gaba da amfani dashi ba" ya qureta matuqa ta kasa daure bacin ranta ya bayyana muraran "Wai me ya dameka da rayuwata ne?,ina ruwanka dani?,me yasa kakeson shishshigema rayuwata bayan ni bayan ni gana shigewa taka?,bayan ni ban damu da taka rayuwar ba?,me na tsare maka?,ohk....alwashinka kakeson ka cimma ko na quntatawa rayuwata shine kake aiwatarwa yanzu?" Tsaf ya xuba ido yana kallonta ba tare daya motsa ko yace wani abu ba,mamaki take bashi idan tana masifa wanda ko iyawa ma batayi ba,batasan me yake ji cikin zuciyarsa bane,batasan wanne hali yaje ciki ba,da yana da ikon maida bara bana daya dawo da ita ya goge dukkan wani tabo da aibu,ba zata fahimci komai ba,ba zata gane komai ba,tanata amfani da zahiri ne ba tare data binciki me badinin ta haifar ba,saiya saki hannuwansa kawai gami da fidda qaramin murmushi,indai ba tunzurata yayi ba bazai taba jin muryarta ba,idan bai tunzurata ba yasan halinta sarai ba zata taba yin magana dashi ba ko zasu shekare a haka,yasan halinta tsaf,baijin baya ga mahaifanta akwai wanda yasan halinta sama dashi "Donke baki damu da rayuwata

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});