Chapter 17
Chapter 17
ita,murmushi shahida keyi yawancin lokaci,ta sake yarda Allah ne kadai.ya isa ya hada zukatan bayinsa,har yau bata tana ganin wani abu mai kama da abinda zunnurah ke tuhumar fiddausi dangane da ita ba. Anwar ya samu ya kammala karatunsa cikin wahala da dagiya da kuma taimakom anty husaina wadda ta sadaukar da dukkan wani abu nata don ci gabanshi,yayin da shahida ta zamo mutum na biyu data sadaukar da dukkan wani abu da take ganin ta mallaka saboda anwar din. Bayan fitowar sakamakonsa wani yayan abokinsa ya kirasu yayi musu tallar aikin d'an sanda da za'a soma dauka,rimi rimi sukayi komai da karime karime da qarfafawar gwiwar shahida data dage kan sai yaje,sai kuma batun tafiya training ya taso,a nan ne ya sare saboda lissafen lissafen abubuwan da za'a buqata daga garesu,wanda kusan duka harka ce ta kudi,koda wasa bazai doshi anty husaina da wannan batun ba saboda yasan cewa wahala ce da nauyi kawai zai dora mata,saiya shiga neman kudi babu ji babu gani,sai lokacin da tafiyar ta matso sannan ya shaidawa anty usaina,ta masa addu'a sosai,ranar da zaiyi sallama da shahida ta dauko baqar ledar viva ta dire masa. Sai daya gama kalla sannan ya dago yana dubanta,baisan ma da wanne baki zai mata magana ba,da wanne harshe zai gaya mata yadda take a wajensa?,kaya ne da tasan cewa zai iya buqata a ciki,wanda ko bata fada ba yasan a qalla zata kashe dubu biyar,Da hannu ta masa nuni dole yayi shuru,tamkar ba zasu rabu ba ranar,ji yake kaman idan yaje zaiyi shekara ne bai dawo ba. Kwanansa uku acan shida wasu mutum biyar suna cin wuya saboda ance sam babu sunansu cikin list din,bawai kuma babu dinba,yanayin qasarmu ne kawai,an suba wadanda sukafi kowa rashin galihu an cire sunayensu daga list din an maida gurbinsu dana wasu,hakanan suka tattara suka dawo gida. Randa shahida ta ganshi ya dawo ba qaramin jin takaici tayi ba,har kuka ta kusa yi,shi ya dinga lallabata yana bata haquri "Duk randa Allah ya horemin abu na farko da zan fara ginawa shahida shine makaranta,zanyi irin makarantar da yaran masu kudi suke zuwa,irin makarantar da suke karatuna zuba yaran masu qaramin qarfi,su samu irin ilimin da yaran masu hannu da shuni suke samu,su samu gata da kulawa irin na yaran masu dashi"shuru shahida tayi tana karantarsa,har cikin zuciyarsa maganar take fitowa saboda yadda hakan ya bayyana saman fuskarsa "Yaran marasa shi suna shan wahala,suna shan wahala matuqa wajen neman ilimi,bayan sun samu karatun da qyar ya zamana karatun ya kusa zama na banza,sakamakon yadda aiki ke musu wahala,wanda wasunsu daga qarshe sakamakon karatun nasu kusan dai dai yake da takardar tsire" nan ma dan shuru yayi yana hadiyar yawu,sosai lamarin ke sukar zuciyarshi,sun jima suna tattaunawa game da halin rayuwa sannan daga bisani sukayi sallama. Anwar bai gajiya ba bai kuma sare ba yaci gaba da neman aiki baji ba gani,burikansa din nan guda biyu su yake fafutukar ganin ya cimmawa,yana tsoron shahida ta kammala secondry ba tare daya samu aiki ba,babban burinsa a duniya suyi aure sanda zata kammala makaranta,ya kuma tsaya mata tayi karatu kaman yadda takeso harsai tace ya isheta,yana da burin yi mata halacci kwatankwaci koma fiye da yadda tayi masa. *BAYAN WATA HUDU* Kallonshi take tamkar ta zabga masa mari haka takeji,saidai hakan ba maiyuwuwa bane tunda ba tarbiyyarta bace,dawowarta kenan daga gidan anty amina ya tsaidata,sam batasan yana biye da ita tun daga qofar gidan anty amina ba cikin motarsa saida ta iso layin nasu,ta shiga gida da niyyar ba zata saurareshi ba yadda yaketa zabga aike yasa umma tace ta fita ta saurareshi. Hakanan cikin jikinta takeji kamar akwai wanda yake kallonta,kamar anwar na wajen tare dasu,a hankali ta kalli damanta,shine kuwa sanye cikin jibgegiyar rigar sanyi da wandon jeans,kasancewar ana cikin yanayin sanyi,yayi kyau matuqa,kai kace wani ne ko dan gidan wani,kyansa ya sake fitowa,fitilun motar daya bari a kunne sun haskeshi sosai kaman yadda suka haskesu,idanunta cikin nashi saiya ja da baya ya juya ya soma barin wajen. Wani tashin hankali ya ziyarceta,da wanne baki zata yi masa bayani?,ganin yadda hankalinta ya wajen ya sanya saurayin shima juyawa yana kallon wajen saidai baiga komai ba,bata sake bi ta kanshi ba ta shige gida da hanzari,wayarta ta laluba ta soma kiran layin anwar din,saidai harta qaraci ringing dinta ta gama bai daga ba,hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba,ba zata manta ba shekaran jiya suna hira yake ce mata "Shahida tsoro nakeji,gani nake kaman zan rasaki,kaman kinfi qarfina" cikin mamaki tace "Me kake fada anwar?" Murmushi yayi saidai ya taba har zuciyarsa "Shahida...kina kallon kanki a mudubi kuwa?,irinki ba qananun mutane ke aurenki ba....ina tsoron kada wani mai motar yasha gaba na" sosai taji haushi harma ta shige gida ta barshi ko sallama basuyi ba,da qyar yasha kanta ya waya,to jiya bai samu zuwa ba kasancewar ya samu dan wani aiki yana kulawa wani da provision dinsa cikin anguwarsu,ladan da yake bashi ba wani mai yawa bane kasancewar kanti ba wani girma gareshi ba,amma ya karba yana yi saboda ba mutum ne shi mai raina sana'a ba komai qanqantarta. Kusan ranar kwana tayi tana kiran layin nashi amma ko sau daya bai daga ba,daga nashi bangaren hankalinsa a tashe yake,hakanan zuciyarsa ke wani irin tafasa,kishi ne ki cinsa sosai,fargaba ta lullubeshi,fargabar kada ace zancansa ne zai tabbata zai rasa shahidansa,duk sanda ta kirashin bai daga ba sai yaji wani qunci na sake ziyartar zuciyarsa,bai iya daurewa yana jin kiranta na shigowa amma ya kasa dagawa,daga bisani tilas ya kashe wayar duka yana fatar ta haqura tayi bacci. Kwana biyu ba anwar din ba dalilinsa,hakan ya daga hankalinta don har wajen kai sadaka bata ganinsa,da yammacin kwana na ukun bayan ta dawo daga kai abinci wanda yanzu ajewa kawai take wajen baba ado dake wajen ya raba a aiko da botikin don fir anwar yace ta daina kaiwa,shiryawa tayi ta tadda ummanta zaune tana jan carbi bayan ta idar sallar la'asar "Umma....zanje gidan anty amina"kai ta daga ta dubeta sannan ta shafa addu'arta "gidan amina kuma?,makarantar fa?"kanta tadan sunkuyar tana wasa da farcenta "hadda ake karba,kuma ni na bada tawa tun jiya" dan jim tayi sannan tace "Shikenan,ki gaisheta....yauwa....kice mata yaushe za'a fitar da ankon umaiman,ki gaya mata lokaci yana qurewa fa" "Tohm umma....saina dawo" "Zan rakaki yayaa" cewar mubina wada ke shirin islamiyya ta fada bayan ta watsar da hijabinta wajen "Babu inda zaki,makaranta zakije" cewar ummanta,tana jiyo ihunta ta saka kai zata fice tana dariyar rikici irin na mubinan,dai dai lokacin abbanta ya shigo,saita koma da baya tana masa sannu da zuwa yayin da yake tambayar abinda aka yiwa mubinan "Wai gidan anty amina tace zata bini,kuma islamiyya zata" "Ke ina taki islamiyyar?" "Hadda ake amsa abba kuma na bada tawa tuni..." "To ma sha Allahu,dama inason ganinki" "To abba gani" ta dawo tana dawowa saman kujera 'yar tsuguno ta zauna, "Shahida....ina fatan ba wani abune ya shiga tsakaninki da yaron nan ba anwar?" "Abba meka gani?" Ta tambaya a sanyaye "Kwana biyu bana ganinsa yana zuwa" shuru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,dukkaninsu ummanta da abbanta wani irinso sukewa anwar din,halayen anwar abun sone,nagarta gareshi wadda ta zama tilas ko waye kai ya burgeka "Uhmmm...bakice komai ba" "Abba in gaya maka?"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96