Chapter 73
Chapter 73
yasa ta sanya ayar tambaya a kanta,wace anty usaina?ta tambayi kanta lokacin data tsaya gefan anwar suna magana qasa qasa yadda shahidan bataji,gabanta ya fadi cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take zato bane. Saidai kuma addu'ar tata batayi tsaho na aka ware fili na musamman saboda babbar yayar ango aka bata dama,cikin qananun hawaye da suka kasa riquwa a idanunta ta miqe ta isa inda anwar da shahida ke zaune,tasa hannunta ta tashesu tsaye gami da dan matso dasu gaban step din da suke kai kadan yadda kowa zai iya ganinsu,ta karbi abun magana tayi taku biyu gaba kadan dasu sannan ta tsaya "Yanzu da zan tambaya cewa suwa kuke gani a tsaye a nan wasunku zasuce amarya da ango,wasu zasuce masoya,eh....masoya ne saidai ba ordinary masoya da kowa ya sani ba,masoya ne da kalar soyayyarsu ta bambanta data kowa,masoyan da Allah zai cika alqawarinsa a kansu koda ba wanda yaso hakan,nasan zaku yarda dani idan kukaga wannan" saita juya ta kalli masu gabatarwa,cikin sakannin da basu wuce goma ba majigin dake kafe a bango daban dake hall din ya soma haske wanda hakan yaja hankalin kowa,ciki harda anwar da shahida,cikin qanqanin lokaci hotuna suka soma bayyana kansu daya bayan daya,hotunan anwar da shahida shekara biyar zuwa shida baya,mamaki ya kama anwar ni na a ina anty usaina ta samo wadan nan hotunan?,hotuna ne da sukan dauka lokaci zuwa lokaci shida shahidan idan yaje zance sanda ya siyi waya torching ya siya mata itama,tana ainihin shahidarta yana ainihin anwar dinsa,nan fa murmushi ya cika fuskokin al'umma kowa nabin hotunan daya bayan daya da kallo,abokan tsokana suka samu nayi,yayye da iyaye suka dinga dariyar hotunan,wasu da hijabai a jikinta,wasu ta sunne kai,shi kuwa yana dan tsirit dinsa babu wata cika ko kumari tattare dashi,a hankali hotunan suka dinga shiga zukatansu suna tuna musu wani lokaci can baya,lokutan da sukafi kowanne dadi cikin rayuwarsu,hoto na qarshe ya soki zuciyarsa shida ita,dukkansu basu manta ba,wannan shine hoto kusan na qarshe da suka dauka tsakaninsu dab da mai afkuwa zata afku,idanunta ta runtse hawaye nason saukowa tana hanashi,turota da anwar yayi daga gidansa shine abinda yazo mata a rai,daidai sanda shima ya dauke kanshi daga kallon hotunan,suna qarewa gurin ya rude da hayaniya da kuma tafu gami da sowa,saida mc ya daidaita komai sannan anty usaina taci gaba da magana "Zuwa yanzu nasan kowa ya gasgata maganata ko?" "Eh..." Duka hall din ya amsa,kaita jinjina sannan ta sake komawa gabansu tana dubansu har yanzu abun magana na hannunta "Inason ku sake tabbatarmana da cewa zaku kula dakanku,zaku kula da amanar juna,ga shaidu nan suna kallo" ta qarashe maganar tana fidda murmushi gami da fatan hakan ya kawo sauyi tsakaninsu komi qanqantarsa,anwar ta fara miqawa abun maganar tana tsareshi da ido,dole ya amsa yakai bakinsa,sassanyar muryarshi mai cike da mazantaka ta cika hall din wanda hakan ya taso da tsohon mikin dake danqare zuciyar nafisa dake maqale ita da mima a wani sashe na hall din,ji tayi kaman zuciyarta zatayi bindiga,sonshi da qaunarshi ya sake narkewa cikin zuciyarta,taji inama tun farko batayi sakin bakin cewa ta fasa aurenshi ba? "In sha Allah zan kula da ita,zan sauke duk wani haqqi nata dake wuyana..." "Kayi mana qwange....zaka bata soyayya da kulawa?" Anty usaina ta tari numfashinsa ta fada cikin sauri ta sigar tambata,kasancewar ba abun magana a hannunta yasa wadanda ke zaune gaba gaba abokanshi su kadai sukaji me tace sai kuwa su,idanu ya fiddo yana kallon antyn ya tabbatar qure takeson yi masa,cikin qasa qasa da murya yadda su kadai zasuji yace "Idan naga ta cancanta ba" yana miqawa antyn abun maganar,duka takai masa wanda ta manta ma a inda suka saboda jin haushi ya goce yana dariya,abun ya baiwa mutanen dake wajen sha'awa suka saka dariya gami da sanya musu tafi,harara ta jefa masa sannan ta juya ta miqawa shahida abun maganar "Uhmm...uwar gidan anwar,ina naki alqawarin" murmushi ta qaqalo sannan ta jefawa anwar harara wanda har cikin zuciyarta ita tayi hakan,yayin da sauran mutane suka tsammaci soyayya ce "Alqawarin daya dauka baiyimin ba anty,ba abinda ya iya,baisan haqqin soyayya ba baisan mutuncin masoyi ba,baisan komai ba a soyayya bai iyata ba" tsit kowa yayi yana saurarenta cikin mamaki,gaban anty usaina ya shiga faduwa,hasina da zunnurah dake zaune cikin mutane ji sukayi kaman su rugo da gudu su qwace abun maganar daga hannunta,yayin da nafisa ta tsaya cak farinciki na ratsata,me zai farune?,ba hadin kai tsakaninsu kenan ko jituwa "Haka kikeso anty na fada irin kalaman da wata amarya da aka yiwa auren dole ta fada?,idan ban yabi masoyi kamarshi ba me zance?,bashi da buqatar yabo ko daukan alwashi a kansa,shi yasan komai,duk alqawarin da zan dauka anan na fallasa sirrin soyayyarmu ne,alqawarin daya dauka duka namu ne mu biyu basai nayi maimaici ba,ni dashi duka abu daya ne" ta qarashe fada tana murmushi saman fuskarta can qasan ranta kuma tana jin ciwon lafazinta,sowa da ihu wajen ya kaure dashi,ba wanda ya fuskanci me take nufi daga anty usaina saishi uban gayyar,sai zunnurah da hasina,kowa ya zaci cewa abinda ta fada din zallar soyayya ce da qauna,miqawa antyn abun maganar tayi,tana juyowa suka hada idanu dashi saita dauke idonta gefe guda. Sosai dinner din ta qayatar ta sanya farinciki cikin zukatan al'umma da dama,takuma burgesu,komai ya gudana yadda anty zubaida tayi fata shahidan bata bada matsala ba,tayi qoqarin kula da duk wani motsi nata da action nata. *Alqawarin Allah* 3️⃣6️⃣ 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Daurin auren da za'ayi sha daya na safe amma tun takwas na safe gidan ya soma cika da 'yan uwa,a sannan tana kwance daga saman gadonta tana kallon yammatan nata hada hadarsu abinsu suna breakfast,ko sha'awar abincinma batayi bare takai gaci,babu yadda hasina batayi da ita ba amma ko kallonta batayi ba bare ta tashi,sai juyi take daga nan zuwa can,ji take kaman zazzabi zai kamata,har goma saura tana kwance tana kallon masu wanka nayi masu kwalliya nayi. A sannan ne anty zubaida ta shigo tana dubanta "Wankanne yau baki da niyyaryi ko kuwa?" Bata amsa mata ba illa miqewa da tayi ta zauna sosai saman gadon tanajin jikinta a matuqar mace,haka zuciyarta a cunkushe,kanta a qasa anty zubaida ta aje ledar hannunta "Ki tashi kiyi wanka ki shirya,mai kwalliya zata shigo tayi miki" "Anty.." Ta kira sunan anty zubaidan zuciya a karye,juyowa tayi tana kallonta "Don Allah ki qyale mai kwalliyar nan yau,don Allah" dan shuru tayi sannan tace "Shikenan zata koma,hasina ta shafa miki ko powder ne" daga haka ta fice daga dakin. Dariya hasina tayi sosai tana qarasowa inda shahida ke zaune tana tare qwallar idonta,idan da hali yau batason ko sau daya tayi kuka "Hajiya shahida,nikam na rasa me kike nufi,don Allah yammata ba kukan dadi wannan matar take ba?" Ta tambayi sauran yammatan dake dakin tana watsa hannaye,dariya aka sanya sannan ta dora "Allah ya baki miji irin wannan da yaji komai da komai amma ki tsaya kina wani nuna qiyayyar banza,ke idanunsa kawai aka kallah Allah ansan dan soyayya ne na qarshe,baku lura da yanayin kallonsa bane?" Ta sake jefawa 'yammatan dakin tambaya "Ashe bani kadai na gani ba,nida daada ta fadamin tun farko aini zan sako kai akwai amanta da batunki" daya daga cikin cousin sis din shahida ta fada,muryarta kamar ta mutumin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96