Chapter 43
Chapter 43
maida wayar aljihu,ya tarbeta cikin fara'a ya amshi ledar hannun nata sannan ya bude mata gaban mota,dubanshi tayi sosai "Kaima kariga da kasan qa'idata ko,mu taka zuwa titi ka tsaremin napep" kai ya langwabar mata yana dubanta "Kar muyi haka dake don Allah,yau dai daya kiyimin wannan alfarmar na kaiki,tunda muke dake shahida ko kara babu baki taba shiga motata kosau daya ba,koda batan hanya" maganar tashi ta bata dariya amma ta maze,ita bata da ra'ayin hakan kwata kwata,ganin yadda yaketa roqarta gashi dare nayi yasa tayi bismillah gami da addu'a ta shiga ya zagaya ya rufe ya tada motar. Farinciki yau fal zuciyar nuran,haka ya dinga sako mata hira,suna tsaka da tafiya taga ya dauke hanya,idanu a waje zuciyarta na gudu ta kalleshi "Ina zaka dani malam" dariya yayi "Karki damu shahida,duk sanda kike tare dani cikin aminci kike,wani waje kawai zamu shiga,ki rakani zanwa mama siyayya"shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya,duk da haka hankalinta bai kwanta ba har sai data ga sunyi parking qofar wajen ta bude murfin motar suka shiga. A tsaye yake wajen biyan kudi da yake dab da qofar shiga da fita,yana saka pin dinshi jikin p.o.s machine da ma'aikin wajen ya turo gabanshi,yana gama sawa ya tura musu donsu ciri kudinsu wanda hakan yayi dai dai da ganin gilmawar wata da zuciyarsa hakanan ta afu da sanin wacece,suna miqa masa resit ya karba ya soma takawa don ficewa daga wajen,saiya tuna ya yiwa sa'ida alqawarin turare,tace tana son irin turarenshi randa yaje gidan,yace mata ba lallai a sameshi qasar nan ba,amma zai siya mata copy dinshi,yana da wuya yayi alqawari ya saba banda haka da bazai sake komawa ba,a gajiye ya sake juyawa zuwa ciki ya soma laluben sashen turaruka. Tunda ya shiga side din daga nesa yake hangowa kamar shahidan,tana tafe yana biye da ita a bayanta kaman wani bodyguard,taku kadan zai qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,tana zaban abu tana zubawa a cart din da nuradden ke turawa,ya bata dama ne ta zabarwa maman komai,da fari taso zuqewa yace indai tayi hakan bata dauki maman mamarta ba,dole tayi yadda yakeso. Sanda ta waiwayo don dawowa daya side din fuskarta ta bayyana fes cikin idanunshi,tana murmushi ne gami da hararar nuradden daya tsokaneta da "Iyee,ashe madam din tawa an iya siyayya,irin wannan siyayya me aji haka?,gaskiya idan mukayi aure ke xaki dinga min shopping" dauke kanshi yaso yayi tare da aiwatar da abinda ke gabanshi amma sai ya gaza hakan kamar wanda aka haneshi,haka kawai yaji idanunsa na masa yaji yaji,wani abu mai zafi ya sauka a qirjinsa,suna dab da cimmasa ya juya ya soma takawa don barin shagon gaba daya. Kallon bayanshi kawai ya haifar mata da mummunar faduwar gaba,duk da batasan waye ba bata ga fuskarshi ba,haka kawai ta dinga kallon bayanshi har ya bacewa ganinta nuradden nacan yana zaben zobe,yanayin tafiyarshi da bayanshi kaman anwar "And so what koda ya kasance anwar dinne?" Zuciyarta ta gaya mata wanda hakan ya sanyata tabe baki da daga kafada. Tun kafin ya qarasa ya bude motar,yana zuwa ya shiga ya maida murfin ya rufe,saiya samu kansa da kasa tafiya,ya sauke glass din side dinsa gaba daya qasa abinda ba dabi'arsa bace,numfashi yake fitarwa dai dai idanunsa kan qofar fitowa daga wajen,shi kansa baisan zaman me yayi ba me yake jira oho duka bai sani ba,saiya duba agogon hannunshi,tara saura,tara saura fa na dare?,sake maida idanunsa yayi qofar shagon dai ya kafeshi da ido. Minti goma ya sake duba agogo,tara na dare saura kadan,har yanzu dai shuru?,ya tambayi kansa "Lafiyanka kuwa anwar?,wai shin ma me kake jira ne?" Ya tambayi kansa da kansa,tuna hakan da yayi yasa ya dage gilasan motar da gaggawa ya zura key zai tasheta,dai dai sanda ya sake duban qofar kanti,sai gasu sun fito fuskokinsu cike da murmushi,yana riqe da ledojin siyayyar,yayin da ita kuma take riqe da iya tata jakar. *Ga mai buqatar littafin da zan fara bayan kammala alqawarin Allah,ya shiga youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA zaiga an rubuta (subscribe) dajan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa wannan number zanyi adding dinsa a grpup din in sha Allahu 07038670166* https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos alliya: *Alqawarin Allah* 2️⃣2️⃣ Fasa kunna motar yayi ya tsaya cak yana dubansu ta cikin gilashin har suka isa bakin motar nuradden din,shi ya bude mata qofar motar ta shiga sannan ya sanya ledar daya a baya,saiya dora dayar saman cinyarta,runtse ido anwar yayi ganin haka yana jin wani abu ya dunqule masa a wuya. Hannu nuradden ya saka cikin aljihun wandonshi ya ciro wani dan qaramin akwati,ya budeshi yana murmushi ya ciro qayataccen zobe a ciki ya miqawa shahida yana murmushin,kallonsa tayi sannan ta kalli zoben "Da zaki miqo min hannunki na saka miki sai nafison haka,ki saka da hannunki shahida....amma shahida,don Allah zaki aureni?" Maganar ta shiga kunnenta a bazata,daga idanunta tayi ta kalleshi "Me ya kawo wannan maganar nuradden?" "Ban cancanci nayi wannan maganar bane shahida?,kina tunanin akwai wani namiji da zai kalleki yaji ba burinsa bane ya mallakeki?,ko tsahon zamanmu tare bai kamata ace na nemi mu zama miji da mata ba?" Bayyananniyar ajiyar zuciya ya saki,gaba daya ya rusa mata lissafi da plan dinta "Hakane....amma kayi haquri zamuyi wannan maganar daga baya,kaga yanzu dare yayi naga kiran anty xubaida ma" "Shikenan" ya fada yana maida zoben akwakunsa sannan ya miqa mata,ta saka hannu ta amsa ya zagaya seat dinsa ya shiga ya tayar da motar. Kashi anwar ya jingina da kujerar da yake kai idanunsa kan motar tasu har suka fice daga wajen,hakanan yaji ya kasa zama shima ya tada motar tasa ya figeta yabi bayansu da hanzari,ba jimawa ya cimmasu,haka ya dinga bin bayan motar har zuwa cikin unguwarsu qofar gidan,gotasu yayi yayi parking din motarsa daga gaban tasu ya kasheta yana kallon abinda ke faruwa,motar ta bude ta fice ta tura gate din gidan ta shige sannan nura ya tashi motarsa ya fice daga layin. Ya kusa a qalla minti goma a tsaye a wajen "Wanne abu kake ne haka anwar,kana cikin hayyacinka kuwa?" Yaji maganar daga sama,wani sashe na zuciyarsa na tuhumarsa "Ya Allah" ya fada shima cikin jin haushin kansa,gami da tuhumar kansa na me ya kaishi aikata haka,saiya kunna motar yana duban agogon dake gaban motar,qarfe tara harda minti goma sha shida,yana jin da qyar idan zai iya zuwa gidana anty usaina yanzu duk da tana can tana jiranshi,kawai saiya wuce gidanshi,zuciyarsa na masa wani irin zafi haka kawai. Baiyi nisa a tafiyar ba wayarshi ta dauki qara,ya kalli wayar da ido kawai,sa'ida ce ke kiranshi,saiya danna sannan ya maidata handsfree yace "Ya akayi sa'in(shi yakan kirata dashi wani lokaci)" "Uncle,zaka zo ne?" "Me ya faru?" "Uncle wani abu na gani,wata na gani tazo wajen ummi uncle kasan dawa take kama?" Kai ya kada "A'ah,dawa take miki kama?" "Uncle kaman anty shahida nidai haka na gani,amma wannan ta dan fita girma ta kuma dan fita kyau" gabanshi ne yafadi baisan sanda yace "Yaushe?" Ba "Dazu dazu suka shigo gida tare da ummi" dan shuru yayi na dan wani lokaci sannan ya sauke boyayyar ajiyar zuciya "Shikenan...yau bazan samu shigowa ba,amma ki bari gobe idan nazo sai muyi maganar" "Toh uncle,ka siyomin turaren?" "Zan kawo miki karki damu,ki gaida ummin naki kice mata wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96