Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 93

Chapter 93

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta gaya mata kenan,ita kuwa a rayuwa yanzu burinta na gaba shine ta shiga gidan anwar ta zama ita ke fada aji,ita zata sa ayi ta hana kuma a hanu,wanda daga qarshe take fatan shahidan ta fita tabar mata gidan gaba daya taci gaba dayin yadda takeso. "Gaskiyar magana mima banason nayi rayuwar da bani zance ayi ba cikin wannan gida,saboda har yau ina tsoro kuma ina shakkar soyayyar dake tsakanin anwar da wannan mayyar yarinyar" abun nema ya samu wajen mima,hanyar da zata wargaza rayuwar auren nafisan cikin sauqi,duk da haka saita sake tsuke fuska ta kuma gum da bakinta harsai da nafisan ta sake magantuwa cikin mitar tayi mata shuru,fuska ta yatsina "In sake shiga sabgarki ki watsamin qasa a ido?,ina qoqarin fiddo miki da daraja da martabarki amma ke baki gani,gwara kawao na qyaleki kici gaba da samawa kanki mafita" harara ta watsawa miman "Banason wulaqanci wallahi mima,haba don Allah,sau daya dai don nayi amfani da shawarar kaina saiya zama matsala?" Sai data gama shan qamshinta sannan tace "Shikenan,zaki samu yadda kikeso,zaki mulka anwar ki kuma juyashi shida waccar yadda kikeso matuqar zaki jure ki kuma bi doka da qa'ida,zan dawo next week randa kikacemin zaki fara rabon IV zakiji sauran qarin bayani" kamar ta goya mima haka nafisa taji,kudade masu yawa ta baiwa miman sannan ta rakata. Dariya mima ta saki bayan ta gama irga kudaden,mota takeson sauyawa,kuma ba shakka lokacin da zata sauya motar da takeso din yayi,a jikin nafisan zata hada kudinta tsaf,daga qarshe kuma ta tashi a tutar babu,ba anwar din ba kuma kudinta,daga haka ta tada motarta taci gaba da tafiya tanabin waqar dake tashi cikin motar cikin nishadi gami da tsara yadda zata mallaki anwar ita kadai bayan ta fitar da shahida da nafisan ma daga gidan dukkansu. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kaman a mafarki take jiyo sallamar anty xubaida cikin falon nasu,da sauri ta sauko daga gadon wanda ta maidashi wajen rayuwarta,idan kaga ta fito tota tabbatar anwar ya fita baya gidan sannan zata fito tayi aikace aikacenta a gaggauce ta koma,sam bata qaunar haduwa dashi ko daya,Suna shirin yiwa kansu mazauni ta fito fuskarta a washe "Anty yau a gida na?,ashe xakixo?" "Kamawa ai take,gashi ta kama shahida naxo" cikin walwala da farinciki ta tarbesu. ,sun jima sosai ranar,sunata hira dasu huda,duk sai yaji kewar gida ta sake kamata,kaman ta koma gidan haka takeji. Saida suka dan kebe sannan anty zubaidan ta gaya mata abinda ya kawota,zancan auren anwar,kebe fuska shahidan tayi cikin nuna halin ko in kula,saidai can qasan ranta wani abu ke tsinkulinta,maganganu sosai anty zubaidan tayi mata,gami da jan hankalinta,suna gama cin abincin rana tace zasu koma,kaman shahidan tayi kuka amma hakan ta haqura,taso sosai antyn tabar mata hudan amma qememe taqi,haka suka tattara tanaji tana gani suka tafi. Zuwan antyn yasa tadan sake ranta,ta koma sabgoginta kamar baya,saidai ta sake janye sosai daga anwar din,sati biyu da faruwar hakan anwar ya shigoda set din manyan akwatina guda hudu,da farko tayi burus amma daga bisani tayi tunani kada ya tsammaci kishinsa take saita karba ta masa godiya,yayin daya bita da kallon mamaki,da gaske bata jin kishinsa? Hakan na nufin bata sonshi?. Cikin kwanakin ka'in da na'in ya maida hankalinsa ga koyon abinda yasa gaba daga raha computer instute,ya ware lokaci har gida yake iskeshi malamin,baisan me yasa abun ya tsaya masa a rai ba,bai san me yasa ya maida hankali fiye da yadda ya xata ba,wanda yake da tabbacin cewa cikin wata uku ya cimma abinda yakeso ya cimma din,ta bangare guda guda kuwa yayi qoqarin kawo sauyi ko yaya yake tsakaninsa da shahidan,don ko kusa baida burin nafisa taxo ta fuskanci komai dangane da zamansu,duk da qoqarin nasa sau da yawa yakan cimma tasgaro,saboda rashin samun cikakken hadin kai daga shahidan. Ta bangaren amarya nafisa kuwa shirye shirye sun kankama ka'in da na'in,dukkan wani abu da aka sani na bidi'ar biki ba wanda bata tsara xatayi ba,harda ma wanda ba' saba gani ba,ko sauraren abinda anwar din zai bayar batayi,sha'aninta kawai take. Qarfe shida saura malamin da suke karatu tare ya tafi,yarage saura shi kadai a dakin,ya shiga cumputer din sosai yayi shige da fice wanda ya tabbatar masa lallai ya soma nisa,hakanan yana cimma abinda ya nufa din,saiya kasheta yana sakin murmushi wanda yayi dai dai da shigowar kira a wayarshi,duban wayar yayi sai yaga nafisa ce,ya manta shaf cikin satin zasuxo jeran kaya,bai daga ba harta katse,saiya janyo wayar yana laluba inda ya aje numberta,cikin sauyin da aka fara samu wanda ada bashi da ita. Har tayi ringing sau biyu tana katsewa ba amsa,sai ana ukun sannan ta daga,shuru tayi tana sauraren muryarsa wadda ko mutuwa tayi ta dawo ba zata kasa gane muryar waye ba "Bakisan ina cikin gidan bane?" Ya tambayeta ganin tsahon zamansu baiji motsinta ko gilmawarta ba,shuru babu amsa saboda haka ya kautar da wancan zancan "Ki sameni a dakin karatuna....am yana nan daga baya kaman zaki shiga qofar kitchen ta baya" ya sake mata bayani don ya sani bata sani ba,tunda bata taba zuwa ba. Wayar ta sauke tana jin wani haushinsa na kamata,tome zaiyi mata,kiran me kuma yake mata?. Har sai daya zaci ba zata zo ba yaci gaba da aikinsa sannan yaji an murda murfin qofar,ya daga kai yana kallon bakin qofar,itace cikin jar doguwar riga wadda ta yane kanta da qaramin mayafinta,idonsa ya dauke wani abu na tsirga masa,ba kwalliya a fuskarta amma tayi masifar amsarta rigar wanda ya kasa kubuta daga qyasata da zuciyarsa tayi. Daga sallama bata sake cewa komai ba,ta samu gefansa ta zauna,saiya kashe wayar tashi da yake dannawa,ya juyo gaba daya suna fuskantar juna sosai yatsunshi sarqafe da juna idanunshi cikin nata,fuskarsa na nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne,sai taji kallon da yamata nauyi,ta kauda kanta gefe guda "Gobe jibi gata masu jeren amarya zasu zo...." "Me zanyi musu to?,meye amfanin gayamin din?,Allah ya kawosu lafiya" ta fada cikin zafi zafi wanda ita kanta batasan ta aikata hakan ba,idanu ya zuba mata har takai aya sannan yace "Babu abunda xaki musu,kawai inason ki kwashe kayanki xaki koma dakunan sama" waiwayowa tayi tana dubanshi,me zataje samanshi tayi masa,dai kawai ta miqe ta soma takawa tana cewa "Na barwa amarya,inda nake nan ya isheni na qarasa kwanakin da suka ragemin" bai fuskanci me kalmarta ta qarshe ke nufi ba,amma ganin zata fice sai yace da ita "Umarni na baki ai ba shawara bace bare ki gayamin naki ra'ayin" daga haka shima ya juya abinda shida kujerarsa,saita waiwayo tadan dubeshi kadan sannan taci gaba da takawai ta fita daga dakin. Tana shiga nata dakin taji kuka ya qwace mata,duk yadda taso hana kanta abun yaci tura,batasan me yasa takejin bacin rai da damuwa ba,kuka tayi sosai kafin taji zuciyarta tayi sanyi. *BAYAN KWANA UKU* Tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata doguwar riga na wani yadi me sulbi wanda yake kama da yadin satin,hakan yasa yabi jikinta ya lafe,gajeran hannu ne dashi gami da wuyan half shoulder wanda ya fitar da wuyanta da wani sashi na qirjinta sosai,kanta babu dankwali kana a tsefe yake,hakan yasanya gashinta da bata kamashi da ribbom ba ya biyota shima ya kwanta saman filon da take kai,gama wayarta kenan da ummanta tana nazarin maganganun data gaya mata taji

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});