Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,294 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

eyes dinshi ya lumshe gaba dayansu,yana jin wani abu mai ciwo na sauka saman zuciyarshi kamar ana d'iga masa wuta,wani boyayyen murmushi ta saki sannan cikin shagwaba tace "Karka damu nawan....ba abinda ya faru dani,am safe..." Bude idanun nasa yayi kaman zai kalleta saiya kalli wani sashe na daban,yana sauke ajiyar zuciya a boye,a duk sanda yaji ko yaga labari irin wannan babu wadda yake tunawa sai ita,hakanan haushi tsana da qyamarta yakan sake ninkuwa a ransa. "Yaya" ta kirashi tana son kauda damuwar data ziyarceshi,tunda haqarta ta cimma ruwa "Yaune fa zamuje yaya?,don Allah karki sake cewa kana da wani uzurin" "Saura minti goma sha biyar mu shiga meeting....saidai bayan mun kammala kuma" ya fada yana miqewa a hankali kai tsaye ya wuce bandakin dake cikin office din nashi ta bishi da idanu tana tantamarsa. A hankali ya tura qofar bandakin sannan ya maidata ya kulle,gaban dan fanfon dake maqale a bango mai hade da madubi dake manne a samanshi ya isa,yasa dukka hannayenshi ya dafe sink din tangaran dake qasan famfon,qirjinsa na zafi haka zuciyarshi,ya jima a haka kanshi a duqe yana kokawar maida yanayinsa yadda yake sannan ya dago yana duban kanshi a madubin kamar baisan halittar kansa ba saiyau,maganganu yake da zuciyarshi,magana yake gayawa kansa wanda shi kadai yasan meke kai kawo a ranshi harna tsahon wasu lokutta sannan ya zare 'yar samam suit dinshi ya daura alwala bayan ya tattare dogon hannun ta ciki,sai daya saka dan qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida rigar ya fito. Da sauri ta jiyo a firgice suka hada idanu dashi,tana tsaye gaban wani dan qaramin akwatinsa da ake budeshi da lambobin sirri,wanda ta budeshi ta kuma soma fiddo wasu kayayyaki dake ciki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida kan d'an akwatin dake zaune dirshan daga can wani saqo na office din,baya taja cikin rawar murya muryarta can qasa tace "Am sorry" baice mata uffan ya taka a hankali zuwa wajen,inda ta janye jikinta ta rabe a bango,ya durqusa ya dinga daukan kayan d'aya bayan d'aya yana maidasu muhallinsu,duk abu guda idan ya dauka yana jin kaman yana qarawa zuciyarsa nauyi ne. Har ya saka wani abu ya sake cirosu ya kalla,suna nan kamar yadda ta bashi su,hatta da ledarsu itace dai wadda ta qullesu a ciki,d last thing data bashi a tarayyarsu,da hanzari ya maidasu ya rufe sannan ya sauya lambobin sirrin ya miqe zuwa gaban teburinsa ya amsa wayar daketa burari,sai daya kammala a nutse sannan ya aje,ya kalli nafisa data tsarki kanta tare da ala wadai da shegen qwaqwqwafinta da yakeson ya bata mata dukka plan dinta "Ki wuce gida,saina qaraso" daga haka ya soma diban wasu files,dai dai sanda P.A dinshi ya shigo suka soma yunqurin barin ofishin,hakan ya sanya dole tabi bayansu jiki a sanyaye,a wajen elevator suka rabu,su suka hau wadda zata kaisu third floor ita kuma tayi qasa don barin companyn. *GA MAI BUQATAR WANNAN LITTAFI ZAI BIYA NAIRA KACAL 200 YA SAMESHI,WANDA KE BUQATAR DUKKA ZAFAFA BIYAR DUN KUWA ZAI SAMESU NE AKAN FARASHIN NAIRA 500* πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½ *_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DINπŸ‘‡πŸ‘‡_* 2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_ saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layinπŸ‘‡πŸ‘‡ *07067124863* *_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*πŸ‘‡πŸ‘‡ *09032345899* _Sayen nagari, maida kuΙ—i gida masoyan asaliπŸ˜‰πŸ˜»πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ‘ŒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*πŸ™πŸ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *** 0️⃣2️⃣ Qarfe biyu na rana suka shigo gidan ita da huda,a falo suka tadda anty zubaida gabanta plate ne dauke da alala guda uku tana ci "Wash" kadija ta fada tana zama saman kujerar dake falon,sannan ta zame dankwalin kanta don tasha iska,dogon gashinta da bashi da cika saboda santsi da tsahonsa ya bayyana "Ina kuka jima haka yau?" Muskutawa shahida tayi,muryarta dauke da alamun gajiya tace "Kin manta na gaya miki muna shirye shiryen ziyarar da mai makarantarmu zai kawo mana next week?" "Af,na manta haka ne fa....amma da alama ba qaramin shiri kukewa zuwan nasa ba,ga dalibarku nan ta kasa zaune ta kasa tsaye" inji anty zubaida tana duban huda dake zare safarta tana dariya,yatsina fuska shahida tayi cike da qosawa "Nima abun duk ya soma ginsata anty,duk sun d'aga hankalinsu duka malaman makarantar.....amma hakan qila baya rasa nasaba da halayyarsa,don a yadda kausar ke gayamin bashi da sauqi sam,kuskure kadan zai gani da bai masa ya dauki mataki,don bai qaunar abinda zai taba students din,last year yazo lokacin ban soma koyarwa a makarantar ba" "To Allah ya taimaka yayi jagora...kece ma,da kin amshi aikin kamfaninsu abban huda da duk wannan jigilar kin huta da ita,har mota zasu baki kyauta saboda matakin da aka baki aiki akai yakai a bakin" murmushin gefan baki kawai tayi,sannan tayunqura ta miqe tana tattara mayafinta zuwa dankwalinta da jakar makarantarta "Au....kinga naso na manta...nuraddin ya bada saqo,yayita kiran wayarki wai bai samu ba" cak shahida ta dakata da abinda take ba kuma tare data juyo ba,fitar furucin daga bakin anty zubaida zuwa kunnuwanta jinsu take kamar harbin bindiga "Waima....ina kika aje wayarki?,nayita kira ni dinma ban sameki ba......anya shahida anya?,sai yaushe zaki saki ki koma dai dai?,saboda nuradden ne kika kashe wayarki?,nuradden kuwa deeja ya cancanci haka kuwa?" Batasan idanunta sun soma fidda hawayen da suka cikasu ba sai data ji saukarsu kan hannunta dake cukuikuye da mayafinta,kasa jure tsaiwa tayi saitayi gaba cikin sassarfa. Da kallo anty zubaida tabita harta bacewa ganinta sannan ta girgiza kai tana furta "Allah ya kyauta" bata sake tankawa ba saita maida hankalinta kan alalanta da take ci. Ganin har huda ta gama komai shahidan bata sake ko leqowa ba,sai anty zubaida ta bawa hudan saqon tace ta shiga ta kai mata,sannan ta gaya mata ta fito taci abinci. Qarfe hudu na yammaci ta fito a shirye tsaf cikin doguwar riga abaya wadda ta wadatu da adon duwatsu,tayi rolling da wadataccen mayafinta,tayi kyau duk da babu ko digon hoda fuskarta bare akai ga kwalliya,hakanan idanunta tarwai suke babu kwalli ko d'aya a cikinsu. Ci gaba da kallonta anty zubaida tayi harta kammala tsakurar alalen sannan tace "Zanje na dubo umma" "Saikin dawo,Allah ya tsare,bari na baki saqo" ta fada tana miqewa zuwa cikin dakinta,mintina qalilan ta fito da leda ta miqa mata "Gashi kikai mata" hannu biyu ta saka ta amsa sannan tayi mata sallama ta fice daga gidan,don 'yar rakiyar tata huda yau akwai islamiyya ta riga data wuce kuma,tilas ta wuce ita d'aya. A hankali take takawa zuwa bakin titi,jikinta a mace yake kamar yadda take jin zuciyarta sam babu wani qwarin gwiwa ko karsashi tattare da ita,tun daga can nesa ta hango shigowar motar,kallo d'aya tayi mata ta gane motar kota wace,hakan yasa ta sake tsananta d'aure girarta gami da kau da fuskarta tamkar bata ga motar ba. Ilai kuwa yana zuwa dab da ita ya rage saurin motar,saidai yadda ta dauke kai tare da qara saurin tafiyarshi ya hanashi damar ce mata komai,tana jinsa ya qara yin gaba,hakan ya nuna mata reverse zaije yayi ya dawo,don haka ta qara

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});