Chapter 42
Chapter 42
bude flask din dake gaban mubina ta gutsiro wainar takai bakinta "Da tunima na gama ai,maqociyarmu ce ta shigo umma tace a zuba mata shine nake tara miki wata yanzu" "Ummmm....amma fa tayi dadi sosai" ta nemi waje kusa da mubinan tana zama ta janyo yaji ta soma gutsira tana dangwala,mubina na bata labarin bikin wata cousin dinsu dake matsowa,shirin da akeyi anko da dai sauransu "Kowa shiri yake yaya sosai,kinsan wanda zata aura din yana da kudi ba laifi" murmushi kawai shahida ta fitar,wato duk wadda akace yau zata auri me danshi murna ake mata "Allah yasa abokin zama ne,ya sanya alkhairi" "Ameen yaya,naga umma ma tasa an kawo mana ankon,amma bandake" harararta tayi "Ce miki akayi ni cima zaune ce da za'a min anko?" Dariya mubina ta qyaqyace da ita "Waya isa yace miki cima zaune,hajiya accountat da kanta"sai data ci ta qoshi sosai sannan ta isa bakin famfo ta wanke hannunta ta daura alwala ta wuce falon umma. Da sallama ta shiga,su biyu ne zaune suna hira,ita da wata baquwar fuska da batasan wace ba,saidai kallo daya ta yiwa matar taji gabanta yayi mummunar faduwa,itama matar idanunta kan shahida,murmushi kan fuskarta tana amsa sallamar tata,dauke idanunta tayi ta samu gefen kujera ta zauna "Sai yanzu kika shigo?" "Haba tun daxu umma,na tsaya naci waina ne" "Ashe takice amma umma ta bamu muka cinyeta" cewar matar cikin fara'a,sai shahida ta juya ta dubeta itama fuskarta ba yabo ba fallasa tace "Ina yini?" "Lafiya qalau,mun yini lpy shahida ko?" Ta amsa gaisuwar gami da jeho mata tambaya daga qarshe,kai ta gyada tana mamakin yadda akayi matar ta san sunanta,bayan umma bata furta sunan a gabanta ba "Tunda nake zuwa ban taba ganinki ba sai yau,Allah dai yayi yau zanga yaya shahida" ta kuma fada tana murmushi,itama murmushin shahidan ta maidata mata,ganin kaman bata saki jiki ba ya sanya umma cewa "Maqociyarmu ce nan gaba kadan gidanta yake,tayi wajen wata shida da tarewa sai yanzu Allah yayi ta leqo mana,gidan nan da faruq yake gaya miki ana sadaka duk juma'a?" Sai a sannan ta fahimci gidan da take nufi,kai ta gyada tana sake fadada fara'arta,don mubina tasha bata labarin kirkin matar,daki ta wuce daga haka tana jiyo hirarsu da umma. Har ta gama zamanta ta soma shirin tafiya matar tana nan,a nan taci abincin dare tare dasu umman,mamaki take sosai shahida,a ina suka santa ne?,wace ita?. A falo tana rataye da jakarta ta dubi mubina "Cikin kayan da antyn katsina ta kawo miki daukomin na zabi style zankai dinki,yi sauri ki daukomin,sa'id yayi anguwa mai nisa yace ya barshi basai ya dawo dakata ba tunda kusa da anguwarsu yake,motar haya zanbi kar dare ya sake yimin" "Wallahi duka na sakasu yaaya suna wajen wanki" goshinta ta dafe tana jan dan tsaki cikin rashin jin dadi "Halinku daya ai indai mubina ce,kowanne kaya da an saka an cire duk kyanshi sai ruwa,saiki haqura ai har sai ta karbo itama da dan banzan sanabe,ki kama kayanki ki wanke amma saikin kai wankau" murmushi matar tayi har fararen haqoranta suka bayyana kan idanun shahida,gabanta ya sake faduwa,matar tana mata kama da wata,kaman ta taba ganin fuskar "Kinga qanwata zo muje ki zabi style wanda kikeso kinji"tayi maganar sanda ta miqe tsaye ta dauki hijabinta dake aje gefe tana sakawa,kallonta shahida tayi,sai taji tana jin nauyinta sosai,banda haka ce mata zatayi a'ah ta barshi,amma saita kasa fada,don ita gaba daya ta jima rabonta da sake amincewa da wani a rayuwarta,duk wata baquwar fuska da zatayi kutsewa rayuwarta kaffa kaffa take da ita. "umma...ina kuka samota newai?,ni gaskiya ba wani gidanta da zan bita" shahida ta fada dai dai saitin kunnen umman cikin nuna rashin yarda "Babu komai matar sananniya ce,hakanan mun dan jima tare,kije kawai" hakanan jiki ba qwari ta fito ta sameta bakin famfo tana daura alwala,ta kammala ta yiwa umma sallama suka fice. Ko a tafiyarma bata yarda sun hada kafada ba,tana gaba ne tana binta a baya,duk da haka takan juyi jefi jefi ta sako ma shahidan hira,nata eh ko a'ah ne har suka qaraso gate din gidan,tsaiwa shahidan tayi tana kallon gidan,kaman taso ta taba ganin anwar tsaye bakin gate din sau daya,saidai bata tabbatar dashi dinne ko bashi bane,kawai dai tun daga ranar ta tsani kallon qofar gidan ma "Muje ciki mana shahida saiki zaba a nutse" murmushin yaqe ta saki "Nan ma ya isa,idan da yara saiki turo su miqo min na wuce,yau nayi dare sosai a waje takwas ta kusa" "Yanzu zaki wuce ai,ki shigo ko kuma nace mubina ta fiki kirki dason mutane" murmushi tayi saita bi bayanta kawai. Sosai falon ya burge shahida,komai a kammale a tsaftace yana fitar da qamshi "Zauna gu waje nan shahida" tana nuna mata kujera da hannu,a darare ta zauna din tana bin falon da kallo mai gwanin sha'awa da burgewa,sanda yake fidda hijabinta wata 'yar budurwa ta sauko daga sama ta matakalar benan dake falon "Sannu da zuwa ummi kin dade yau" ta fada tana duban maman tata "Wallahi sa'ida...yauwa shiga dakina ki bude wardrobe dina,inda na aje dinkunan da aka kawomin din nan shekaran jiya ki cirosu gaba daya" "Toh" ta amsa tana shirin juyawa idanunta ya sauka kan shahida,saita sake juyowa da sauri ta kalleta ta kalli ummin nata,sai kuma ta juya ta sake hayewa saman. "Ina zuwa shahida kinji" ta fadi tana nufar wata qofa dake nuna alamun kitchen ne,wayarta dake jaka ta dauki kuka alamun kira ke shigowa,ta cirota tana dubawa,noradden ne,saita latsa tana karawa a kunnenta "Ranki ya dade,ya akayi sa'idu yabarmin ke a waje da daren nan?,naje gida baki nan,na kirashi yace wajen umma yabarki,kuma kince basai ya dawo ba" "Eh uzuri nayi masa ne" ajiyar zuciya ya aje "Ni gaki kin fiddoni,kema kinsan ba yadda za'ayi na iya kwanciya kina waje,fito gani a qofar gida" "Na fito daga gidan ai" "Ina kika je?" "Ina maqota" sai tayi mishi kwatancen gidan yace gashinan,babu jimawa ta fito dauke da wani dan qaramin faranti da aka dora ruwa da lemo,gefe daya dambun nama da meatpie ta aje gabanta "Ga ruwa kisha" murmushin yaqe ta danyi don har yanzu a darare take,hakanan taji ta kasa sakewa "Na qoshi wlh anty" "Da alama dai da gasken shahida baki da kirki" dariya maganar ta bata,saita kuma sakin murmushi sosai "Ba haka bane anty,kina gani kusan ma tare mukaci abincin" "Eh...amma ko albarka kyasa" bata sake cewa komai ba ta gutsuri meatpie din kadan,dai dai sanda ta qwalawa yarinyar kira "Sa'ida me kike ne?,kiyi sauri sauri fa take gida zata wuce" "Gani nan ummi" tana maganar ne sanda take sakkowa daga saman cikin sassarfa rungume da kayan a qirjinta,a gaban ummin ta zubesu "Riga daya ce ban gani ba ashe ta shiga cikin wasu kayan "ok...gasu ki xaba wadanda zasu miki" a nutse take daga dinkunan,duka sun mata hakanan sunyi bala'in kyau,tana son yace xata dauka duka tanajin nauyinta,saita zabi uku daga ciki "Wadan nan ma sunyi,na gode" tura mata sauran tayi "Jeki dasu gaba daya,mai yiwuwa telan yaga wanda zaifi miki kyau akan wanda ke kika zaba" haka ta tattara duka kayan ta zuba mata a wata 'yar jaka mai kyau,ta mata sallama ta fito. Yana tsaye jikin motarsa wayarsa na hannunshi yana danne danne,ganin fitowarta ya sanyashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96