Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tasha sosai,bata fita ko ina,hakanan hatta da wayarta ma a kashe take,daga daki sai daki,sam anty zubaida batasan meye ya faru ba,saidai dukkaninsu tattalinta suke har ta soma jin dadin jikinta. Ranar wata karaba qarfe hudu na yammaci ta fito daga dakinta,gidan yayi mata shuru haka yayi mata fadi,haka take ji duk sanda su huda suka wuce islamiyya saisu barta daga ita sai anty zubaida kawai,hakan ya sanyata tunanin samo islamiyya itama da zata dinga zuwa daukan karatu,don sanda ta fada din anty zubaida dariya ta dinga mata "Ohni zubaida,shahida bansan inda zakikai wannan son karatun naki ba" murmushi kawai tayi "Anty karatu fa baya yawa,indai ba mutuwa kayi ba ilimi bai yanke maka ba,ba zaka rasa cin karo da wani abun da baka sanshi ba" "Gaskiya ne" ta fada cikin nuna gamsuwa. Sanye take da atampha riga da zani wrapper,sai qaramin mayafi data yane kanta dashi,ta sake haske haka ta fada,a hankali take takawa har zuwa cikin ainihin falon,babu kowa kaman yadda ta zata,sabida haka ta juya ta nufi kitchen don tasan a wannan lokacin anty zubaida tana can. Da sallama a bakinta ta shiga da dashasshiyar muryarta irin ta marasa lpy,anty zubaida ta juyo tana amsawa fuskarta qunshe da murmushi "Patient an taso kenan" "Wallahi anty...na gaji da kwanciyar nan" ta furta tana jan kujera ta zauna akai "Ai gwara ki tattaka ko zakiji dadin jikinki" sama sama suke hira ita da anty zubaidan,inda tana daga zaune ta amshi wasu ayyukan tana tayata,a haka su faruq suka dawo daga islamiyya suka tarar dasu,zama sukai cikin kitchen din suma,saidai basu bar bakin anty zubaida ya huta ba,wannan ya buda wancan wannan ya buda wannan wai duka yunwa sukeji,sudai tunda anty shahida ta soma lalura kawai gidan sai a slow,waiwayowa anty zubaidan tayi "Kinga shahida...don Allah debe qannenkin nan ku bani waje na yafe taya aikin wallahi" dariya shahidan ta bushe da ita sannan ta miqe tana duban su huda "Oya....lets go" ta furta tana kada hannunta,ba musu suka bita a baya suka fice zuwa falon. Haidar ne ya soma canza tasha zuwa mbc bollywood faruq yace sam shi mbc action xai kalla,huda kuma ta tubure ita mbc three takeso "Dalla malama matsa kona kwada miki mari" faruq ya fada yana duban huda gami da zare mata ido "A'ah wallahi,dalili dame?,bani remote din gaba dayanku na raba gardama "please anty" faruq ya fada cikin langwabe kai yana miqa mata remote din,ta gane me yake nufi,saita basar tana cewa "Babu wanda za'a kamo zabinsa,zabina kowa zai kalla" gwalo kowa kema dan uwanshi,tana murmushi ta kamo TVC news kwana biyu tayi missing labarai bata samun kalla,tana jin haidar na gulmarta "Miss news" ta waiwaya ta kalleshi "Zamu hadu anjima" da sauri ya dawo ya fasa hawa saman da yake qoqarin yi "Sorry my aunty kar aji kanmu,niba dake nake ba,Allah kwana biyu dama da baki da lafiyar nan duk sanda ustaz zai karbi hadda fecewa nake kar 'yammatan ajinmu su min dariya...ki taimakeni" "Saika biya cin hanci" "Na yarda" ya fadi yana dariya,idnunta a kansu sanda suke wucewa dakunansu don sauya unifoarm dinsu,saida suka bace mata sannan ta janye idanun nata tana sauke ajiyar zuciya,duk sai taji kaman ita kadai keda matsala,takura da quncin zuciya,tana son ta rabu dasu amma ta rasa me yasa qoqarinta ya gaza?. Ganin cewa suma ba labaran suke ba saita sauya tasha zuwa FASHION TV,sabuwar tasha ce amma tana tashe kuma ta samu karbuwa wajen al'umma sosai,sukan nuna abubuwa kala daban daban,kama daga sutturu na zamani,bukukuwa,birthday,engagment da sauransu,wani lokaci tana son kallon tashar saboda takan debe mata kewa,wasu abubuwan da suke nunawa na burgeta. Yauma ta tadda suna hira da wata mai gyaran jiki shuwaarab cikin harshen turanci,shirin ya qayatar da ita sosai,ta bada dukkan hankalinta akai,sai suka yanke suka tafi talla,tallan farko da suka sako na engagment din wasu igbo ne,tsaki taja tana gyara zamanta saboda sam bata ji dadin tafiyarsu hutun ba,cikin ranta tana ganin rashin aikinyi ne kawai da zaka tsaya batawa kanka lokaci saboda an maka egage da wani,wai itama soyayyar nan gaba daya meye zaqi ko ribarta?,ta sake jan tsaki sanda aka nunosu suna bayyana yadda suke son juna da farincikinsu da kuma saqon godiya ga duk wadanda suka halacci bikin engage din nasu,remote ta dauka da niyyar sauya channel idan sun gama ta dawo,talla na gaba da suka fara haskowa sai yaja hankalinta matuqa fiye da komai,engage ne na wasu couple da za'ayi musulmai masu cikakken sunan hausawa,hoton farko na amaryar ne tayi kyau cikin shiga ta alfarma,wanda kallon farko idan kayi mata zaka tabbatar ta samu gata,hoto na biyu shi ya sanyata jin wani abu ya tsirga mata,a hankali kanta ya sara,hoton anwar ne a matsayin shine angon da za'a gudanar da bikin engage din nasu kwanaki goma masu zuwa,sosai ya fito tarwai,ya cika screen din tvn tamkar yana tsaye ne a gabanta,sanye da wasu shegun suit,daga sama har qasa shigarsa abar birgewa ce iya kallon mai kallo,miqewa tayi tsaye ba tare data shiryawa hakan ba,wani abu mai nauyi na danne zuciyarta kamar ana shirin riqe numfashinta ne,remote din taji ya mata kadan ta kauda fuskarsa daga screen din tvn,saboda haka bata tsaya ba har sai data dangane da socket din dake jone da kayan kallon ta kasheshi gaba daya,sannan ta juya da sauri don barin falon zuciyarta na wani irin gudu tamkar wadda taga wani abun tsoro. Sallamar uncle hisham ita ta tsaidata cak,tasan dole ya ganta bai kyautu kuma ta wuce ba tare data yi masa barka da zuwa ba,daidaita yanayinta taketa qoqarin yi,kafin afkuwar haka anty zubaida ta fito daga kitchen din,da sauri ta juya don batason taga fuskarta,ta gwammace ta fuskanci uncle hisham a haka akan anty zubaida,yanzu zata saka ayar tambaya kan sauyawar yanayinta lokaci guda bayan ba haka ta baro kitchen ba. "Sannu da zuwa abbu" ta fada a sanyaye idanunta na kallon qasa saboda tana ji a jikinta kamar qwayar idanun nata ba dai dai suke ba "Yauwa rahamatullah(ya kirata da ainihin sunanta),ya jikin naki" "Da sauqi abbu" ta amsa masa da sauri saboda wani abu dayake qoqarin shaqe mata wuya "Ma sha Allah" juyawa tayi da zummar barin falon yace "Shahida" sake juyowa tayi "Na'am abbu" "Anjima inason ganinki" "Toh" ta fada tana sake juyawa zuwa dakinta. Takai ta kawo tayi hakan yafi sau babu adadi,hawaye keson fita daga idanunta amma ta hana kanta hakan,tanason lalubowa kanta dalilin da zai sanyata kuka "Enought is enought shahida,kinyi kuka a rayuwarki da yawa...ya isa haka,ya kamata ki kawo qarshen komai,ya kamata komai ya qare" take fadawa kanta da kanta bayan ta tsaya gaban mudubin tana duban qwayar idanunta da kanta gaba daya saika zaci zararriya ce,kallon kanta da kanta take tana bawa kanta qwarin gwiwa,saidai ina hawaye ba'a masa shamaki,saida daya ya ziraro mata wanda ya baiwa dukka sauran damar samun hanya,ta fashe da kuka sosai cikin sassarfa ta isa saman gadonta tayi rub da ciki tana cusa kanta qasan filo tana kokawar hana kanta ci gaba da kukan. Kaman ba zata falon ba amma dole ta qarfafa jikinta ko don saboda abbu da yace yanason ganinta,ta gyra fuskarta gaban mudubi ta zizara kwalli bayan ta shafa powder,batason kowa ya fuskanci tayi kuka,a kasalance take kawowa har ta iso cikin falon,wanda a al'adar abbun

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});