Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,301 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Wallahi daada bana sonshi,shima daada ba sona yake ba bazai gaya muku gaskiya bane kawai" baki ta tabe tana mata duban sakarya "Au Allah ko?,ashe tun farkon saninmu dashi mu muka jajibo miki shi ko?,ashe qiyayya ce ta hadaku a baya ba soyayya ba?" "Daada baya sona yanzu bana sonshi!" Ta sake fada cikin kuka "Eh naga alama,shi yasa bai bar kakarki ba yaci gaba dayi mata aike a boye bai bari nasan wayeshi ba,kuma qiyayyar ce tasa ya tasl qafa da qafa ya nemi aurenki hannun iyayenki" "Wallahi daada kinji na ra ntse miki da manufa a lamarinsa" "Dama akwai auren da babu manufa?,shirme kenan" ganin duka taqi fahimtarta saita sauko gwiwoyinta qasa tana kallonta "Daada,don girman Allah ku maida masa kudinsa,ko bazaku bani nuradden ba na amince ko zabamin ko waye a lokacin da kuka saka na bikin nawa ayi dashi" nazarinta daadan tayi na wani dan lokaci sannan ta kamata ta miqar da ita tsaye "Naji,zauna muyi magana" sanyi taji yana ratsa zuciyarta,ta soma jin qamshin nasara,saita miqe din kamar yadda daada ta buqata suka koma saman kujera suka zauna. Saidata bata 'yan mintuna ta nutsu tukunna sannan tace "Komai da kika gani a rayuwa yana da dalili,inason ki gayamin dalilinki na duka wadan nan maganganun da tsallen badaken qin auren mutumin da kowa ya shaida kuma yana da labarin soyayyarku" shuru tayi kawai tana qiyasta ta yadda zata gayawa daadan komai bayan basusan komai ba akan rayuwar data fada a baya,sannan uwa uba shi kansa anwar din ta fahimci ba wanda ya taba gayawa ko bashi labarin komai,idan ta aikata hakan kamar ta dabawa cikinta wuqa,kamar ta yaye mayafin asirin da Allah ya rufa mata kenan?,ganin tayi shuru sai daada tayi tsammanin ko batason magana ne a gaban hasina,saboda haka ta korata waje "Ki gayamin dalilinki,indai matuqar na gamsu,toba shakka a yau basai gobe ba zamu maida masa komai nashi" tofa ga qoshi ga kwanan yunwa,ta ina zata fara ya zatayi?,batason tona komai,batason kowa yaji komai,tana ganin kamar ba muhallin kowa bane ba hurumin kowa bane Kai ta kada "Daada baya sona ne,nima yanzu na daina sonshi,kinga babu amfanin aurenmu" murmushi ta saki tana kada kai "Banda abinki shahida ta yaya masoya haka siddan zasu daina son junansu?,ai ruwa baya tsami banza" cikin nuna dagiya da qarfin hali tace "Hakanan nidai daada muka daina son junanmu,don Allah karku qulla auren qiyayya" hawaye ta siraro daga idanunta muryarta ta soma rawa,saita sake murmushi tana kallonta "Shahida,anyi auren hadin da baki taba ganinsa ba bai taba ganinki ba sai hadi kuma an zauna lafiya harma yafi na soyayyar qarko,kin ganni nan gani da ran Allah?,to sanda na auri kakanku sai randa ya shiga dakina nasan shi na aura,saboda haka indai rashin soyayya ne hujjar fasa aurenki da anwar indai kikaga an fasa to la shakka mutuwa nayi bana raye,ko bana raye zanbar wasiyyar a tabbatar an daura,don anwar din ya cika dukkan siffa da kamalar da annabi yace a baiwa mutum aure" daga haka sai daadan ta miqe ta qyaleta,tashin hankalin data ji a sannan yasa taji zuciyarta ta bushe gaba daya,hawayen idanunta sun bushe tas,saita miqe itama ta shige daki tayi rub da ciki tana sakin ajiyar zuciya ko zataji sanyin tuquqin da ranta yake. Ta shafe a qalla minti talatin a haka kafin daga bisani ta janyo wayarta,ta lalubo number nuradden ta kira,bugu daya tak ya daga,ajiyar zuciya ya soma saukewa da alamu hankalinsa shima ba'a kwance yake ba,duk sai taji bacin rai ya sake shigarta,shi ya janyo komai,shine silar komai "Ka dawo ka sake neman aurena karo na biyu nuradden,bazan iya aurensa ba" ta fada kai tsaye ba tare da tayi sallama ba ko tace komai,kafin taji yace wani abu taji an karbe wayar,da sauri ta daga kai don ganin waye,daada ce,bata ce komai ba ta kara wayar a kunnenta "Nura kana jina?" Ta fadi sanda take ficewa daga dakin,saita miqe ta zauna sosai saman katifar tana bin qofar da kallo. *muna muku fatan alkhairi tare da fatan zaku gudanar da bukukuwan sallarku lafiya cikin amincin ubangiji,Allah ya karba mana ibadunmu,ya gafarta mana zunubanmu,yaji qanmu ya jiqan mamatanmu,yasa mu cikin 'yantattun bayinsa amin umma amin,ZAFAFA BIYAR na muku fatan alkhairi* *_karku manta,ku kasance da tashar SAUTIN HIKIMA TV don sauraren littattafan da zasu debe muku kewa yayin ayyukan sallah a gida* *kundin qaddarata* *daurin boye* *mutuncin mace* Duka wadanda na rubuta *fatan alkhairi a gareku* #zafafa biyar #sautin hikima tv #team anwar #team shahida #team nafisa 🏃🏾‍♀️ _ma'assalam_🤝🏽🤝🏽🤝🏽 _ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsaffin litattafanmu dama sababbi da zamu fara dorawa nan gaba kadan in sha Allah_ https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *Alqawarin Allah* 3️⃣1️⃣ Minti goma kyawawa daadan ta dawo,ta miqa mata wayartata tana dubanta,sannan ta miqa mata kudin da anwar ya bata tana cewa "Tunda kin zabi zubar mana da qima rahama mu zuba nida ke" daga haka ta juya ta fice,a sannan ji shahidan take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu ko xata ji sanyi cikin zuciyarta,me yasa ba zasu fahimceta su bata uzuri ba?,me yasa ba zasu haqura ba?,wai da anwar da itama wa sukafiso ne?,waye nasu a ciki?,kira ne ya sake shigowa wayarta,ta daga ta duba da sauri sai taga nuradden ne,muryarsa kadai ta gaya mata cewa ya karaya bashi da wani sauran fata "Shahida,na rasaki shahida,ta ina zan iya jurewa rashinki?,zan iya tsira daga hukunci da horon rasaki da zuciyata zata yimin?,ki tayani addu'a bansan ya zata kayamin ba" daga haka ya yanke kiran,me daada ta gayawa nuradden?,shikenan ta rabata dashi?,dole ta zauna da mutumin da sam bata ra'ayinsa ne wai?,irin wannan masoyin zata rabata dashi?,kalamansa kawai sun tabbatar da tsantsar qauna da soyayyar da yake mata,saita kifa kawai rubda ciki tana lalube da binciken meye abunyi a qwaqwalwarta,mecece mafita?duk wata dabararta ta qare,wayonta duka ya qure,daada ta yanke komai. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe bakwai da rabi ne na daren ranar,yana zaune a harabar gidan saman daya daga cikin fararen kujerun roba dake wajen,shi ya zabi zama a wajen saboda yadda iskar damina mai sanyi ke busawa gabas da yamma,hakanan qwayayen lantarkin dake harabar gidan sun haske ko ina harda korayen tsirran dake harabar wajen,sai yake jin zuciyarsa wasai,hakanan babu nauyi qunci ko wani abu da yakejin ya dameshi a yanzu,shaqar iskar yake sosai yana fesarwa har cikin huhunshi qamshin iskar da sanyinta na sake sa zuciyarsa cikin wani shauqi da walwala,fuskarsa fes take a washe. A hankali take takowa cikin gayunta,tayi kyau don ba qaramar kwalliya ta dauka ba,don yau din na daya daga cikin ranakunta na musamman,saboda bako da yaushe take samun dama irin wannan ba,ace yau anwar din yazo zance takanas saboda ita,zata iya irga sau nawa hakan ya taba faruwa a tarayyarsu,shi yasa duk ransa zaizo din ba qaramin tanadi takewa ranar ba. Gabansa ta tsaya sannan tayi sallama tana kallon yadda yayi masifar kyau cikin qananun kaya sai kace wanda ya dawo daga europe,ya daga kai yana dubanta sannan ya amsa,cikin shagwaba shigarsa da yadda yayi kyau yana dada burgeta tace "Ya bakaci komai ba dear?" Ta qarashe fada tana jan kujerar dake kallonsa ta zauna,duban tulin kayan ciye ciyen dake gabanshi yayi sannan ya kalleta,shi sam a ra'ayinsa ba mutum bane mai yawan son ciye ciye,kusan ma babu cimarshi ciki sai kadan,kafada ya daga "Karki damu,duka

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});