Chapter 71
Chapter 71
fuska suka wuce ciki,a rumfa suka samu dadan,duk da tsufarta ita dinma amma sai data lallaba jan lalle wanda yayi mata kyau,tana zaune cikin matan 'ya'yanta da jikokinta shahida da hasinan suka shiga,guri daya ta samu ta zauna don ba zata iya maida tsokanar da ake mata ba da kiranta amarya da ake faman yi,tana jinsu har sukayi suka gama suka qyaleta. Da daya da daya kowa ya fice ya barta a rumfar daga ita sai dadan,ta dubeta sosai gami da gyara zamanta tana kallonta "Abinda yasa nace a turomin ke tun yanzu saboda bani da tabbas din xamu samu zama kamar haka idan kuka fara wadan nan bidi'o'in naku" baki shahida ta tabe,su waye a gaba idan ba goshi ba da zata ce haka,duk basu suka tada aurenba,suka tayar da zaune tsaye,sosai daada ta zama cikim seriouse ta soma magana tana duban shahida "Kafin rasuwar mahaifinki Allah shine shaida cewa ya baki tarbiyya bakin gwargwado ya baki duk kulawar data dace,hakanan mahaifiyarki itama ta baki tata tarbiyyar bakin gwargwado,abinda nakeson cewa shine,kinar gani ko karki duba cewa anwar mun lanqwasaki ne kan dole kin aureshi,ba ruwan Allah da wannan,yi masa biyayya ya zama miki wajibi,dole kiyi idan yace dole ki bari idan yace,sauke dukkan haqqinsa ki sani ya rataya a wuyanki babu fashi,ruwanki ne kije ki masa tsiya ruwanki ne ki kyautata,koma meye kikayi abinda za'a soma fada shine tarbiyyar gidanku ce ta uwa da uba kenan,idan kinso kija musu yabo,idan kuma kinso kija musu zagi,Kiyi biyayyawa mijinki sauda qafa,yi nayi bari na bari,anwar ya riga ya zama mijinki Alqawarin Allah ne wannan daya cikashi"a fakaice ta sake tabe baki sannan ta miqe tsam tana cewa "To,na gode" ta soma yin gaba zata fice daga falon,a tsakar gida ta samu hasina tana tsakiyar mutane suka kwasar cafta,da hannu kawai tayi mata inkiya ta fice,hasinan ta tashi ta bita bayan ta yiwa su umma sallama. Qarfe hudu na yammaci harabar gidan maqotan anty zubaida ta cika ta tumbatsa da jama'a,wanda shahida dake zaune cikin dakinta anty zubaida ta kasa ta tsare mai kwalliya na mata takejin surutun jama'a da hayaniyarsu har tsakiyar kanta,babbar harabar gida ce wadda aka qawata da decoration me kyau da tsari wanda ya dace da sutturar da amarya zata saka,kota ina mutane ne dangin shahidan na uwa dana uba,manya da yara da yammata,wajen a tsare yake duk da yawan mutanen da suka halacci kamun. Anty zubaida ita ke riqe da ita har mazauninta inda aka tanada saboda ita,bata barta ba sai data duqa ta mata gargadin karta sake ta bata musu taro ta hanyar yin wani abu na daban,hakanan cikin mayafinta da aka lullubeta har saman kanta ta dinga hadiyar wani abu mai tauri a maqogaronta,ta dinga kokawar maida kukanta,duk wanda yazo a haka zai mata liqi ya wuce taqi ta daga kaima bare ta tantance su waye a wajen,a haka har lokacin soma kamu yayi,tana jin sanda dangin mahaifiyarta dana mahaifinta suka iso inda take zaune,aka buqaci dangin ango su matso "Ga turaren da za'a yiwa amarya kamu dashi inji angonta" taji wata murya wadda kamar ta santa tana fada,aka saki dariya gaba daya,wata mai azabar murya ta rangada guda wadda shahida taji kaman ana sakatar qwaqwalwarta,ta runtse idonta hawayen da take boyewa suka gaza riquwa,sai suka silalo suka zubo har saman tafin hannunta dake aje saman cinyarta,feshin farko na turaren da aka mata gabanta yayi mumunan faduwa,tabbas wannan qamshin anwar ne,turarensa ne,sake rintse idanunta tayi tanajin radadi a zuciyarta,waishin me yasa kowa ya kasa fahimtarta ne?,basa ganewa ne?,me yasa kullum kwanan duniya suke jawo abinda zai sake kusantata dashi ne?,a haka har aka qare fesheta akayi addu'a sannan akaci gaba da saka kidan qwarya,dangin ago suka buqaci yi mata liqi,haka anty zubaida tazo ta dagata zuwa amma ba tare data bude mata fuskarta ba suka shiga mata liqi,kowa sai daya tsaya ya kallesu ya qara. Qarfe sha daya da rabi na daren ranar bayan taron kamu ya watse tana tsaye gaban window din dakinta dake bude iska na shigowa sosai mai sanyi na alamun dare ya soma nisa,iskar dake shigowa cakude take da turaren da aka yi mata barinsa daxu a jikinta wanda duk da wankan da tayi kusan aikin banza ne qamshin bai rabu da jikinta ba,kusan a yanzu ba wannan ne ya dameta ba,saqon anty zubaida data gaya mata kafin shigowarta dakin shine babban abinda ya hanata sukuni a yanzu,dinner da za'ayi gobe tsakanin ango da amarya da abokansu,ta yaya zata zauna bigire daya da anwar din a matsayin amarya da ango?,yadda anty zubaida ta tsume take ja mata kunne kan goben ta tabbatar kome tayi a laifi yake,ranta a bace yake sosai,ga mari ga tsinka jaka?,itakam me anwar zaice da ita?,ya jima da rusa dukka wani farinciki nata yanzu gashi ya sake dawowa yasa hannu ya takwabe wanda yayi saura,bata da wata mafita gashi ta gaji da tsaiwar,saboda haka ta saki labulen ta dawo cikin dakin wanda su uku ne duka duka a ciki don tace ba zata kwana da kowa ba,tsallakesu tayi wanda tuni sun fara barci ta shiga bandaki ta daura alwala sannan ta dawo ta kwanta tana fatan bacci ya dauketa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Duk yadda taso ta taushi kanta ta kuma qwararawa kanta gwiwa donta fita ga motoci hudu na anwar dake jiranta a qofar gidan hakan yaci tura,a dakin baqi na uncle hisham dake dab da qofar fita ta shiga ta zauna. Ran hasina ya baci it hankalinta ya tashi na kada ta bada su,ga zunnurah tayi gaba tuni a motar mai gidanta da yace bai yarda tahau motar kowa ba bare ta mata magana ko shahidan zataji maganarta,irin kudaden da aka kashe mata kawai a ranar donta fito ba kadan bane,ta kuwa fita din tayi kyau,irin amaryar da duk wanda ya kalleta sau daya saiya maida kanshi ya mata duba na biyu,gashi dukka wanda ya dace hasinan ta yiwa magana kan yasa shahidan ta fito sunyi gaba,kusan su suka rage kawai,bata da wata dabara dole daga qarshe ta fita ta shaidawa muhsin da suke zaman jiran fitowarsu. Kai ya jinjina kawai sannan ya juya ya nufi daya daga cikin motocin datafi kowacce kyau da girma,bude gidan baya yayi ya shiga inda anan anwar ke hakimce,cikin dan bacin rai yace "Wai zaman me muke muhsin,haka kawai ka kawoni cikin mota ka aje bayan kasan inada abunyi da yawa" "Kaga saurara....wayarka zaka dauka ka kira mana amarya ka lallabata ta taimaka ta fito" cikin rashin gane me yake nufi yace "Kaman yaya?" Girarsa muhsin ya dage "Eh to....qila sarautar tasu ce ta motsa,tana ciki taqi fitowa" dan jim yayi na wani lokaci sannan ya saki wani tsaki da qarfi "Koma meye kaika jawa mutane wallahi" ya qarasa fada yana kokawar cire babbar rigar shaddar dake jikinsa wadda taci aiki tayi bala'in yi masa kyau,ko ba'a fada maka ba kana kallonshi kaga ango "A'ah,meye na cire babbar riga kamar me shirin dambe?" Sai daya bude murfin motar ya saka qafarsa daya a waje sannan yace "Damben zanyi" ya qarasa fita yana rufe murfin motar,yanajin muhsin din na cewa nifa kiranta nace kayi a waya ka fiddota fa ba wani abu ba,ko kallonshi baiyi ba ya wuce abinsa,dukka 'yammatan dake tsatstsaye suna jiran fitowat amarya donsu wuce dakin taron sai dayaja
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96