Chapter 12
Chapter 12
yanayin ba,duk yanayin rayuwa da yake ciki hakan bai hanashi bacci ba,sai gashi a karon farko saboda ita ya kasa bacci daren ranar gaba daya,duk juyin da zaiyi itace cikin ranshi. Yana biye da ita bata sani ba,baiyi mata magana ba saida suka gota wajen suka shiga wani layi "Yanzu yau kuma haramiyar ladan rakiyar za'a yimin?,wanne irin laifi nayi haka?" Cak ta tsaya,farinciki da kuma faduwar gaba na cakuduwa cikin ranta,idanunta a waje har ya iso gabanta yasa hannu ya amshi botikin,ya jera kafada da ita "Muje" ya fada cikin sassanyar muryarta da kullum take mamakin dad'in muryar da Allah ya bashi,idan yana magana dole sound dinshi yaja hankalin duk mai sauraro,yau saitakejin nauyin tafiya dashi,ta kasa yin gaba,ya sake dubanta "Waiko amsar tambayata itace a'ah akemin irin hakane" wani wal tayi da ido,saiya dafe qirjinsa da hannunsa daya "Kiyi haquri karki qarasa tarwatsamin zuciya,wannan zuciyar mai rauni ce akanki" Fuskarta ta qunshe cikin hijabinta tana dariya qasa qasa,wawiyar ajiyar zuciya ya saki "Wai Allah na,alhmdlh,ko iya haka aka tsaya na tabbatar da cewa ina da nasara...amma dai a gayamin ana sona?" Kai ta kada cike da tsananin kunyarsa,wani dan tsalle ya saka sannan yace "Alhmdlh,alhmdlh" yana rungume da hannayensa. A hankali suka ci gaba da takawa shida ita,saidai ita gaba daya nauyinsa takeji,yayin da shi kuma yake janta da hira jefi jefi,yau duk masu binsu da kallo mutanen cikin unguwarsu basu dameta ba,har sai taji ma batason su isa gida yace zai wuce. "Kina son wanda bakisan sunanshi ba hakanan bakisan waye shi ba" ya fada bayan ya miqa mata botikinta,ita sam bata damu da wayeshi ba,sonsa takeji irin wanda bata taba zata ko tsammatar akwai irinsa ba a duniya,tanajin koma wayeshi yayi mata hakan "Ni sunana muhammad anwar aminu,haifaffen kano ne kuma dan kusa da unguwarku ne ni,maraya ne ni bani da uwa bani da uba,sai 'yar uwata d'aya data ragemin anty usaina,ina karatu ne a fce kano...kefa?,shahida ko?" Murmushi ta saki tana dubanshi cikin tausayi jin cewa maraya ne,kai ta kada sannan tace "Khadija amma shahida,nice ta farko wajen umma da abbana,ina da qanne hudu,nan ne gidanmu a nan aka haifeni,ina SS 2 yanzu" kai ya kada sannan yace "Idan nazo anjima za'a barni na ganki" kai ta gyada da sauri,don tasan yadda zatawa ummanta bayani yadda zata fahimta "Shikenan zanzo anjima in sha Allahu,inason mu soma mu'amala cikin fahimtar juna gaskiya da amana...ki shiga gida lokacin islamiyya ya kusa ko?" "Na gode" ta furta cikin siririyar muryarta data dauki hankalinsa,kai kawai ya iya gyadawa ya bita da kallo harta shige. "Waye a waje kuke tsaye dashi?" Tambayar da ummanta ta soma jefo mata kenan sanda ta aje botikin tana shirin zama,kunya ta d'anji ta kamata,saita kasa amsa mata da wuri har sai data maimaita "Ba kowa umm,yadai taba rakoni gida sanda su ahmadi suka fasamin botiki,shine...shine...." Saita kasa qarasawa,murmushi kadan ummantata tayi,saboda burinta bai wuce su aurar da shahida ba da zarar ta kammala secondry schl,ita kanta tasan basa kyauta mata yadda koda yaushe suke cikin fada da juna suna sakata kuka qunci da baqinciki "Shine me?" Ta sake tambayarta tana tura mata kwanon da tayi kwadon zogale ta rage mata saboda tasan tana sonshi,sai data sadda kai sannan tace "Shine yace wai anjima zaizo idan za'a barni na fita" "Allah ya kaimu" ta fada tana miqewa don ta wanko hannunta,cikin farinciki taja kwanon ta soma cin zogalenta,wanda tana gamawa ta shige bandaki ta sake watsa ruwa saboda ranar da ake,fitowarta kenan daga bandaki dauke kwandon wanka zunnurah ta iso,tana shiryawa tace "Zunnu...akwai labari fa yau"bakin zunnnura a washe tace " ta samu kenan?"kidai muje na baki kisha,ta fada tana zura plate shoes dinta,ta dauki jakarta suka leqa suka yiwa umma sallama suka wuce. A hanya ta labartawa zunnurah komai,dariya ta dinga "Kai amma wannan gayen yayi addu'a tuquru kafin yazo,shahida da babu wanda ya isheta kallo?,da kinga wata da saurayi ma zakice wannan ai iskamci ne dududu shekarunmu nawa?,ashe harkin girma" dundu ta dumawa zunnurah "Banason iskanci qawa,wallahi nayi mamaki nima sosai,dama haka abun yake?,kinji kuwa yadda nakejinsa a raina?,har banason mu rabu,idan yana kallona wlh zunnurah ni kadai nasan me nake ji a zuciyata,ban taba tsammanin akwai wani da zanji haka a kansa ba" dariya zunnurah taketa tiqawa "Na shiga uku ni zunnu,sati daya kacal amma shine kika zare haka?,Allah yasa to nan gaba kar ya haukatamin qawa ya cuceni" "Ba komai idan ya haukataninma zunnu" ta fada tana tayata dariyar,gab da zasu shiga makarantar sukayi kacibus da fiddausi,da fara'arta take musu magana amma shahida ce kawai ta amsa suka rankaya suka shige makarantar tare. Tunda ta dawo daga islamiyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,qiyasta da qimanta yadda haduwarsu zata kasance take,wannan ne karon farko data soma son wani a rayuwarta,kuma karon farko da zata fara tsayawa zance da wani. Tuni ummanta ta yiwa babanta bayani,bai kuma ce komai ba,illa ya kirata ya masa tambayoyi game da shi,ta bashi amsa gwargwadon abinda ta sani game dashi,yace ta kula kuma idan sun fahimci juna zaiyi magana da yaron. Ba wani kwalliya tayi ba,tadai saka kayanta masu kyau atamfa riga da skert,ta kuma yafa wadataccen mayafinta,sanda ya aiko kiranta tare da mubina suka fita,yana zaune saman yalwataccen dakalin qofar gidansu,daga soron ta tsaya tana qare masa kallo,yayi kyau sosai fiye da dazun cikin qananun kaya,iya kwanakin kadai da tayi tana ganinsa ya tabbatar da cewa shi din dan gayune kuma mutum mai son tsafta,bata taba ganin kayanshi babu guga ba,hakanan bata taba ganinsa da datti ko wani abu makamancin haka ba "Daure ki fito princess...saiki kallenin da kyau" habawa,wata iriyar kunya ta taso ta lullubeta,bata taba tsammanin yana kallonta ba,saita sake lafewa ta kasa fitowa,tashi yayi yana murmushi ya tsaya a qofar soron nasu yana kallon mubina dake gaidashi,ya amsa yana shafa kanta gami da yi mata wasu tambayoyi tana amsa masa,rabi duk a kan shahidan ne,kunya duk ta sake kamata ganin yadda mubina ba abinda ya shalleta,komai ya tambayeta gaya mishi take,saida suka gama hirarsu sannan yace "ALLAH YA TAIMAKEKI...kona koma ne yau ba za'a samu ganina ba?" Dole ta fito ta saka musu tabarma daga soron nasu,da yake yana da yalwa sosai masu wucewa ba zasu takurasu ba. Gaisheshi ta sakeyi ya amsa yana tambayarta gida kaman ba dazu suka rabu ba,cikin wani shauqi da yake fusgarsu gaba dayansu.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGππ½* ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ππ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos ALQAWARIN ALLAH 08 Anwar dinne ya soma cewa"Kamar yadda kika sani na gaya miki daxun cikakken suna na sannan kuma ni maraya ne,na rasa mahaifina da mahaifiyata da qannena guda biyu duka rana guda" zaro idanu shahida tayi cike da mamaki da tausayi tana duban anwar "Eh rana daya,sanadiyyar hatsarin mota da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga qauyenmu" "Wayyo....Allahu akhbar" ta fada fuskarta na nuna tsantsar tausayi,qwalla na cika idanunta,tausayin anwar ya kamata,rayuwa ba uwa ba uba ya zata kasance kenan? "Mu biyu muka rage a gidanmu,ni da yayata kaman yadda na gaya miki,yayata nada aure tun kafin rasuwar iyayenmu,yanzu haka tana gidan aurenta ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96