Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,313 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

iriyar soyayya mai ban mamaki da daure kai,zaka rantse da Allah sun doshi shekaru masu tsayi tare,kowannansu yayi amanna da d'an uwanshi,kowanne ya yarda cewa rayuwarshi ta d'an uwanshi ce,baqincikin dan uwanshi nasa ne haka farincikinsa,wuya da dad'i basujin zasu iya rabasu,qaddara kuwa sun jima dayi mata magiyar kada ta shiga tsakaninsu,komai nasu ya zama iri guda,tunanin da wannan yake a mafi yawancin lokutta zaku samu irinsa dan uwanshi yake,tamkar tare aka haliccesu haka sukeji,tamkar zuciya daya aka halitta musu su biyun kowanne bari daya na cikin jikinsa na aiki,anwar kullum kwanan duniya shike rakota gida,bayajin an halicci wani uzuri a duniya da zai iya hanashi rakota gida,yakan xauna a rumfar balarabe yana hangota cike da kishi,duk wani motsinta yana kan idanunshi,baya samun nutsuwa ko sukuni har sai ta kammala ya tattara mata kayanta ya kaita gida,da ace yana da iko da tuni ya hanata zuwa wajen,kishi yakanyi kamar xai halakashi duk sanda take zaune tana rabon abincin,daga bisanima da yaji bazai iya jurewa ba shike amsa ya zubawa kowa,itama a nata bangaren tanajin shine karsashinta,duk motsi d'aya idan zatayi saita daga kai ta kalli qwayar idanunshi take samun salama,tana jinsa har cikin jini da jijiyarta,zata iya sadaukar da komai dominshi,saidai tana mamakin yadda ko sau d'aya bai taba zuwa ya karbi abincin da take rabawar ba kamar yadda sauran mutane ke amsa. Bangare guda kuma bai taba gaya mata yanayin wahalar rayuwar da yake fuskanta ba,tadai san cewa bamai qarfi bane,hakanan yanayinsa ya tabbatar mata da cewa shi din mai wadatar zuci ne,don bata taba jin wani qorafi daga bakinsa ba,ko nunawa kasawa ko gajiya a fuska da jikinsa ba gaba daya,hakan kuma ya sake burgeta dashi,ya kuma sake saka mata qaunarsa. Yau bayan ya rakata sunyi sallama ta amshi botikinta ta juya zata shiga gida taga baquwar mota qofar gidan nasu,tana kallon motar ta tabbatar da cewa sunyi baqi ne,kuma bata raba d'ayan biyu uncle hisham ne,wanda shine ya baiwa ummanta kwangilar dafa abincin sadaka da kullum take kaiwa bakin masallaci a rabar,da farincikinta ta qarasa cikin gidan,don kuwa jininsu ya hadu qwarai da matarshi aunty zubaida,a tsakar gida ta taddasu,fuskarta washe da fara'a ta aje botikin nata ta qaraso saman tabarmar da suke zaune anty zubaida na cewa "Oyoyo 'yammata....sannu da qoqari" tana dariya dariya ta gaidasu,cikin kulawa suka amsa ta juya tana tambayar yaron anty zubaida na faro farouq yashe sukazo?, "Sannu da qoqari khadijatu....lallai na yarda ba qaramin qoqari da amana gareki ba.....gaskiya ali Allah yayi maka baiwa da yarinyar qwarai" cewar uncle hisham,kanta na duqetana murmushi "Alhamdulillahi kam,Allah ya azurtamu da diyar qwarai,mu kanmu muna alfahari da hakan" umma ma kai take jinjinawa,don ita kanta zata iya cewa cikin yaranta shahidan ta dabance,wani irin hankali da nutsuwa gareta,biyayya da kyautata iyaye tana sahun gaba,hakanan take qaunarsu,dalili kenan dako yaushe itama take ta qoqarin daina biyewa mahaifinta suna raba gari shahidan na kallo,sunfi kowa sanin cewa abun ba qaramin ciwo yake mata ba a rayuwa "Nawa ake bina ne kudin kai sadaka khadija?" Uncel hisham ya tambaya yana fiddo kudi daga aljihunsa,dariya ita abun ma ya bata,wanne irin binsa kudi?,mutum mai tsananin kirki da kyautatawa a garesu?,ko iya kai abincin ma da take ita ta sani Allah ne kadai yasan ladan da take samu "Ba kudin da nake binka uncle....nima ai ina samun ladar kaiwa" kai ya gyada "Na sani,wannan amma dole na baki haqqinki ne" "Banda abin shahida aiko kayan kwalliya kya saya ki dinga gogawa idan surukin namu zaizo ko?" Kunya ta kamata ta dan duqar da kanta qasa tana murmushi,mubina uwar surutu kuwa tayi caraf "Kullum sai yazo kuwa mamansu faruqu,yana da kirki kullum saiya kawo mana tsaraba,ko ya bamu goma goma yace mu siya" kunya tasa shahida kasa zama saita miqe zata gudu,yayin sa antu xubaida ta soma tsokanarta "Ah lallai,zanso naga wannan surukin namu,na tabbatar shima yana da kyau da nutsuwa kamar diyarmu..." "Rabu dasu shahida....dawo ki xauna muyi lissafi" uncle husham ya tare mata,haka ta dawo tana sunkui da kai ta zauna "Mu lissafa kwana nawa akayi ana kaiwa?" "Allah uncle ka barshi kawai" "Naqi din" ya fada yana soma irga kudin "Ki fada kona baki yadda naga dama"dariya ta danyi tana basar da maganar,kudi mai yawa ya irgo yace "toh gashi" "Uncle ka bawa umma ta ajemin" "A'ah a'ah,ba ruwan umma,wahalarkice karbi kiyi duk yadda kikeso dashi...iyakata in baki shawarar me zakiyi dashi" cewar umman tana miqews don zuwa kitchen ta hadowa su anty zubaida abinci,hannu biyu ta saka ta amsa tana masa godiya,a nan ta barsu anty zubaida harta gama shirin islamiyya suna zaune suna hirarsu,tayi musu sallama ta wuce. ************************ "Malam balarabe ina kayan anwar?" Shahida ta tambayi balarabe mai kanti lokacin da anwar din ke can yana hada kwanukanta don lokacin komawarta gida yayi "Gashinan ina aunawa...bari na hada miki harda kwakin"murmushi tayi sanda take amsar ledar kwakin daga hannunsa "Anwar...anwar kaina dabanne,ko me zakayi da garin kwaki kuma?" "Na'am?....ai aikin muhammadu kenan,ba yadda banyi dashi ya dinga sauyawa da wani abun ba,ya amshi bashi duk sanda Allah ya hore masa ya biyani amma sam sam ya qiya...gaskiyarki kuwa shi na dabanne,rayuwarsa ma haka,ni tsorona ma kar yayi masa illa yawan cinsa da yake,bashi da abinda ya wuce gari" sam batasan zancan zucin da take ya fito fili ba saida taji sharhin malam balarabe fadi ba'a tambayeka ba,saidai maganar tashi ta taba ta,ko a fuska bata taba ganin wani abu makamancin haka daga wajen anwar ba,hasalima bai taba karbar abincin da take kawowa wajen ba ko sau daya kuwa,a gabansa take rabarwa har ya qare iyakarsa ya dauka mata kayanta suje gida ya aje mata ya wuce,a sanyaye take bin ledar garin da kallo,tausayin anwar din ya kamata,ta yaya mutum zai rayu da cin gari kullum?,tsananin maraicin ne yasa haka?,amma indai da gaske ne sun zama abu daya mai yasa bai taba gaya mata ba?,ta yaya tana cin shinkafa kullum anwar yaci gari?,sosai taji haushin boye matan da yayi,wasu qwalla suka cika mata idanu,saita dauki ledar kawai ta juya ta fice daga kantin ba tare data ce komai ba. Sanda ta isa wajen har ya gama hada komai tsaf yana dube duben nemanta,fuskarshi yadan tsuke kadan "Ina kuma kika shiga?,banason ki dinga darawa ko ina daga nan fa,kinsan halin mutane da shegen kallo da sa ido" "Ba wani waje naje ba,na karbo maka saqonka ne daga wajen malam balarabe" "Balarabe kuma?"ya tambayeta yana nazartar fuskarta,fes ya fuskanci yanayinta ya sauya,ganin bata ce komai ba yasa shi daukan botikin ya soma yin gaba,ga tunaninshi zata biyoshi amma saiyaga bayansa take bi kamar yadda suka fara can watannin baya da suka shude sanda suke baqin juna. Cikin jinin jikinsa yaji sauyin yanayin shahidan bai masa ba,ko shakka babu akwai abinda ya faru shigarta shagon zuwa fitowarta,zuciyarsa yaji ta tsinke sanda ta qyasa masa wani tunani game da malam balarabe,baisan sanda yaja birki ba,ya waiwayo a sukwane,wanda saura qiris suyi karo da juna,baya ta danja kadan tana duban qwayar idanunshi da suka sauya launi,saiya sake matsowa gab da ita,kanta ta girgiza qirjinta na bugawa gana duban hagu da damarta,layin tsit yake babu kowa,yana daya daga ciki layukan da yake da qarancin zirga zirgar jama'a " me malam balarabe yayi miki?"ya tambayeta da wata iriyar rikitacciyar murya,tuni qwallar data

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});