Chapter 45
Chapter 45
murfin ta rufe ta daga masa hannu "Allah ya kiyaye" shima hannu yadan daga mata,har zai tada motar tayi hanzarin tsaidashi "Sorry...don Allah ka yimin alfarma mana" "Allah yasa batafi qarfina ba" murmushi tayi "Bata fiba,saidai idan ba za'a min ba" dan qaramin murmushi yayi "Fadi muji"sai data danyi shuru na sakanni sannan tace "Kamfani triple R Gem nakeso ka rakani don Allah" shuru yayi yana dubanta "Me zakiyi a can" hannu ta yarfar "Kai ya anwar,da banso gaya maka ba Allah,amma..." "A'ah,riqe cikinki" yayi maganar sanda ya tada motar,da sauri ta zaburo "Bafa wani abu bane,wasu sarqoqi nakeson saya a can" kallonta kawai yake,burin nafisa yayi girma da yawa,duk sarqoqin garin nan amma sai taje har triple R ta saya?,iya saninshi wajene dake da babu abun qaramin kudi a can,dutse ne masu daraja da tsada suke sarrfasu,wanda ba kowa ke iya siyan abun kwalliya ba acan,bayason ya fiya gwasaleta har taji kaman ya tozartata,sai ya gyada kai "Alright..amma gaskiya bani da lokaci cikin satin nan gaba daya,saidai ko zuwa next week" "Well,yayi indai zaka rakani din" da haka sukayi sallama ya fice daga gidan yabarta tsaye awajen sonshi na shawagi da ita,sai kuma ta tuna yau akwai partyn da zata saboda haka da sauri ta juya zuwa cikin gida. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe biyar ta fito daga kamfanin kaman yadda qa'idar lokacin tashinsu yake,saidai gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba saboda baqin hadarin daya hado yake kwance a sama yana shirin zub da ruwa. Kusan mutum uku ne sukayi mata tayin sauketa a gida amma ta doje don kare mutunci da qimarta,ciki harda alhajin dake nacinta wanda ta lallaba ta fito abinta ta baroshi a office din rayyan mai kamfanin gaba daya suna lissafin wasu sarqoqi da sukayi masa,haka ta fito cikin ranta tana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya qalau. Titin babu wadatar motoci sai jifa jifa,ko dama can titin bashi da wadatar wucewar ababen hawa musamman ma na haya,yawanci saina gida,hakan ya sanya ta ku sa kashe minti goma tsaye ba tare da taga gilmawar wani abun hawa na haya ba,cikin abinda bai gaza minti biyar ba hadarin ya taso sosai,iska ta shiga kadawa ko ina sama ta sake duhu,fargabarta ta dadu,ta runtse ido tana jin saukar ruwan saman bisa fuskarta,Allah dai yayi saiya daketa. A hankali yake tuqin saboda yanayin ruwan dake sauka din,uwa uba yanajin kaman yayita shawagi saman titi ba tare daya koma gida ba,yakan kasance cikin kewa da kadaici duk sanda ruwan sama irin haka ke zuba yana cikin gidan shi daya,yakan tuna masa wata hira da suka tabayi da uta,duk da yadda yakeson bunne komai nata amma duk lokacin da ake ruwan sama kaman haka sai hirar ta fado masa "Nafison damina akan kowanne yanayi,tana saka nishadi cikin zuciya,komai yana wankewa yayi fes,tsirrai zaka ga sunyi kyau ya anwar sunyi kore shar,kosu kasan suna farinciki da zuwanta,qamshin qasa iska mai dadin da babu kamarta" tayi maganar ne idanunta na alumshe,saita budesu tar cikin nashi a lokacin da ya zuba mata ido yana tayata murmushin da takeyi na tuna yanayin da tayi "Kasan me yaya anwar?" Ta tambayeshi wanda bata kai ga fadin abinda takeson fada din ba kiran nafisa a sannan ya katsesu,dai dai sanda shima nashi tunanin ya katse yana hango tsaiwar wata matashiya cikin ruwan saman da har hazo hazo yake,tsurawa wajen ido yayi yana ci gaba da tuqin a mugun slow kai kace motar na dab da mutuwa ne,baikai ga qarasawa ba wata farar mota ta yanko daga layin da yake kusa da ita,dab da ita ta tsaya na cikin motar ya fito riqe da lema ya iso gabanta ya matsar da lemar zuwa kanta da alamu magana yake mata,idanu ya runtse yana tsaida motar duk da a tsakiyar titi yake,idanunsa qur akansu,alokaci shahida ta sake ja baya "Ka wuce kawai,bani da damuwa nasan ko ban samu mota yanzu ba ruwan daya tsagaita zan samu" "Haba yallabiya,ke kuwa yau dai kawai,uzuri ne fa,kiga yadda ruwa ke dukanki ke daya atsaye anan,uwa uba tsaiwarki a titi irin wannan lokacin hatsarine ga rayuwarki"kai ta girgixa "ba komai Allah zai kareni" "Duk da haka amma kiyi...." Ta gaji dajin kalaman bakinsa,saboda haka kaman adan hasale tace "Don qaunarka da mahaliccinka kayi tafiyarka" ya fuskanci kaman tanason hasala ne don haka yace "Allah ya baki haquri,naji zan tafi,amma kema don qaunarki da mahaliccinki ki karbi wannan lemar" batason dogon zance saboda haka tasa hannu ta amsa,ya koma ya shiga motar ya tasheta ya wuce,ajiyar zuciya ya saki ganin tafiyarsa,duk da haka saiya kasa tafiya yaci gaba da tsaiwa kaman me gadinta. Ganin ruwan yadan fara sauqi saita soma takawa don canza wani titin ko zata dace,shima saiya tashi motar yaci gaba da binta sannu sannu,yana kallon yadda take digar ruwa har cikin zuciyarsa,saidai bazai iya daukarta amotarsa ba,yanajin wani abu cikin zuciyarsa,kallonta na tuna masa da ganinta da yayi,fitowarta daga motar wani,wanda ba qaramin suya yake masa a qirjinsa ba. *ga mai buqatar littafina da zan fara bayan gama alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,daga qasa zaiga an rubuta SUBSCRIBE da jan rubutu,ya danna sau daya zai koma black,yayi screen shoot ya tiro zuwa wannan number,za'ayi adding dinsa agroup din in sha Allah* 07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣3️⃣ Gab da zata tsallaka daya titin mai adaidaita ya taho,ta tsaidashi da sauri,babu kowa a ciki ta gaya masa inda zata ya dauketa suka wuce,sai da yaga tashinsu sannan ya saki ajiyar zuciya "Wai anwar meye damuwarka ne haka?" Wani sashe na zuciyarsa ya jeho masa tambaya,sai a sannan ya dinga tuno abinda ke faruwa,sam duka baisan yana abinda yayin ba,kamar wani umarni yaji ana bashi,kai ya girgiza yana jin haushin kansa,yana ganin ya tsaya ne kawai ya bata lokacinsa,motar ya bawa wuta sosai cikin gudu ya figeta ya harba titi. Su duka suna zaune a falon suna kallo,da sallama ta shiga,dukkansu sannu da zuwa suke mata,anty zubaida na cewa "Wai wai,sannu rahamatullah" murmushi tayi tana zuge lemar hannunta,huda ta tashi da hanzari zata tarbeta ta dakatar da ita "Tsaya huda karki jiqe,don ni da kika ganni yau jalaf nake a kaina ruwan yau ya qare" tayi maganar sanda take aje jakarta "Ahto...haka kawai za'a baki mota kika qi,da kinga yanzu ba ruwanki da ruwa ko rana" "Wallahi anty to ya za'ayi....faruqu don Allah zazzagemin jakarnan ka duban wayata ka shanyan abinda kaga ya jiqe" da sauri huda ta amshe cikin shagwaba "Anty gani sai kice ya faruq kuma?"hararta faruq yayi "To kishiyata" Dariya shahida tayi "Auto auta yi haquri,gyaramin bari naje na sauya kayan jikina sanyi sanyi nakeji" "Idan kin saukoma ga dinkunanki nan an kawo" waiwayowa tayi "Yauwa,yaushe ya kawo?,jiya fa mukayi waya dashi yace bai gama ba" "Dazu ya kawo" "Ya kyauta,don kayan matar data bani aron style nakeson maida mata,kar taga rashin hankalina...bari naje na dawo saina gani" "Uhmmm" anty zubaida ta fada. Sai data soma kunna qwan dakin data kashe dazun da zata fita aiki,haske ya gauraye ko ina,ko.ina tsaf yana fitar da qamshi kaman yadda ta saba masa,ta kalli agogo,shida harda rabi na yamma,an kusa kiran magariba kenan,kayan jikinta ta fitar ta shiga bandaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96