Chapter 22
Chapter 22
data shiga dakinta tana dubawa abun ya sake burgeta,duk da anwar ba wani mai hali bane amma Allah ya hore masa tsari da iya siyayya,komai daya bata ya burgeta,ta jima tana kallon wani zobe,duk dana azurfane amma an qawatashi qwarai dole ya burgeka,zanen heart ne a jiki amma heart din rabi ne,murmushi ta saki tana sakashi cikin yatsunta,yayi masifar yi mata kyau,saita tattara kayan ta kaiwa ummanta wanda ita kanta ta yaba da qoqarinsa kaman yadda abbanta ya yaba,hakan ya mata dadi qwarai,ya kuma bata tabbacin kenan bata da matsala bata da wani shamaki da zai hanata mallakar anwar,tuna haka cikin jin dadi ya sanyata qanqame filon da take kai tana hango kanta da anwar dinta a matsayin ango da amarya qarqashin inuwa guda. Cikin farinciki da walwala ta gabatar da walimarta,komai ya tafi lpy ya kuna qayatar sai jiran sakamako,a sannan komai na tafiyar mata lpy,rayuwar tana hangen nan gaba kadan zata yi mata kyau,komai zai qarasa dai daita musu,anwar ma an masa qarin albashi wanda hakan dukka su biyun ya musu dadi. *SANADIYYA* Ana tsaka da haka gagarumin tashin hankali da yayi sanadiyyar lalacewa komai,ya zama silar tabuwar rayuwar mutane da dama,yayi sanadin wargajewar wannan iyali,ya kuma silar tarwatsa rayuwar shahidan...ya zama wani sanadi na dasa baqinciki mai tarin daci da zafi a rayuwarta ta faru. Rayuwa tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta rayuwa ce ta rashin haquri,dauke kai yafiya da juriya da akasan dukkan ma'aurata da yiwa junansu,fada gaban yaransu wannan ba wani sabon abu bane tun tasowar shahidan,wanda hakan ya sanya bayan girmanta abun ya zame mata wani ciwo da duk sanda ya taso mata yake mata zafi da quna a zuciya,dukkan wani mataki da take ganin ya dace ta dauka a matsayinta na diya mai qarancin iko da abun fada ta dauka harma wanda ya zarta huruminta amma babu abinda ya sauya,duk da alqawari da qoqarin sauyawar da suke. Kwatsam dare guda mahaifinta ya jijjigo maganar qarin aure suna tsaka da rayuwarsu cikin rufin asirin Allah,wanda hakan ya sanya mahaifiyarta tayi tsalle ta dire tace batasan wannan zance ba,dalilin daya janyo tashin tashina da fadan da bata taba gani ya wanzu tsakaninsu ba,hakan ya sanya walwalarta da duk wani kuzari nata ya ragu,anwar ne mutum na farko dayafu kusanci da ita a sannan shiya soma gane tana cikin damuww,amma baisan dalili ba,taqi kuma sanar masa,ta yaya zata gaya masa wannan murdaddeb zance?,tun baya baisan halin da gidan nasu ke ciki ba saboda kare martaba da qimar iyayenta,duk sanda ta fuskanci akwai rashin jituwa tsakanin iyayen nata bata taba yin zance a gidansu,a gidan anty amina take zancanta,toko yanzu ma da lamarin gidan nasu ya lalace can take tafiya ya sameta anan,don ba zataso wataran wani mummunan abun ya faru a gabansa ba duk da yana musu kallon iyayensa amma asirin ciki sai hanji. *MAFARI* Cikin tashin hankalin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta fito daga gidan nasu tana hawaye,yau a gidansu a gaban idanunta ake doki in doka tsakanin ummanta da abbanta?,wanne irin iyaye gareta?,ya ilahi ji take kaman zuciyarta zata fashe,ji takae bugawa zuciyarta zatayi,ita kadai tasan yadda takeji tana jin kaman zuciyarta ta kumbura ne ta cika qirjinta,zataso ace zunnurah na nan saidai ina,gidan anty amina takeson zuwa amma babu ko nutsuwar daukan kudin mota a wajenta,ba tare da tuna nisa da tazarar dake tsakaninsu ba ta hau tafiya cikin fitar hayyaci da tashin hanakali bacin rai da baqinciki. Dawowarta kenan daga inda taje ta sauka a abun hawa,tana yunqurjn shigowa layin nasu ta hangi kaman shahidan,tayi mamaki don shahidan bata taba zuwa gidansu ba,hakanan bata yowa layinsu don asalan ita bamai yawo bace,sauri ta qara donta cimmata,sai taga itace dince kuwa,amma a binda ya bata mamaki hawayen data gani shabe shabe a i fuskarta,hannu tasa ta kamota tana cewa "Shahida,meye haka kuka kike fa akan hanya" sai a sannan ta kula da fiddausin,sake fashewa da kukan tayi,ita koma waye ta gani zata iya fada masa abinda ke damunta ko zataji sassauci a zuciyarta,abun ya mata yawa,wannan damuwar bata shekara daya bace ko biyu,ganin haka sai fiddausin ta janye shahidan zuwa gidansu,ta tura gate din gidan suka shige sannan suka nufi dakinta ta qofar baya,sau tari takan iya shigowa ba tare da an sani ba saboda gidan nada girma babu laifi. Kuka take sosai tana cewa "Na gaji fiddausi....na gaji da wannan bacin ran,ina zanje naji dadi,me zanyi na samu sassauci?" Murmushi fiddausin ta saki,duk da shahidan bata gaya mata damuwarta ba amma tana ganin sara ne yazo kan gaba "Ina da maganin damuwa shahida,maganin da zai dauke duk wata damuwa da kike ciki komai qarfi da girmanta,zaki jiki fresh kaman yau aka haifeki,nauyi da zuciyarki keji ya sauka kaman bai taba faruwa ba" idanunta dake jiqe da hawaye ta daga tana kallon fiddausi "Don girman Allah ki bani kona daina jin suyar da qirjina yakemin" "Kwantar da hankalinki basai kin hadani da girman Allah ba" ta fada tana zuge jakar data shigo da ita,kwalabe ta fito dasu ta hada abubuwan ciki ta gauraya sannan ta miqawa shahida "Daga kanki ki shanye nina daga wajen likita nake shi ya rubutamin shi yace maganin damuwa ne" ba tare da kowanne tunani yazo kanta ba,ba tare da tayi lissafin komai ba,ba tare da ta jinkirta ba ta daga kai ta shanye duka din kamar yadda fiddausin tace mata,cikin wasu qananun mintina ta soma jin dummm,ta soma ji kamar ana sauyata daga tata duniyar zuwa wata daban,ta soma daina gane komai,take a nan ta zube saman gadon fiddausin,lokaci qanqani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dariya fiddausin ta saki tana rufe kwalabenta tare da maidasu haka tana cewa "WASA FARIN GIRKI YARINYA". *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *Ko kuma* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videoshttps://youtu.be/T9a10h1Apqs 👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣2️⃣ A hankali ta farka tana mutstsuka idanunta da taji sun mata nauyi,sam ta mance inda take saida tayi dan tunani sannan ta tuna,da hanzari ta tashi ta zauna ganin gari yayi duhu sabanin sanda suka shigo gidan akwai hasken rana,agogon bango ta kalla sai taga qarfe takwas,hakan yana nuna kenan ta rasa sallar la'asar magariba dama isha'i. Da hanzari tayi nufin tashi saidai gaba daya jikinta a mace yake babu qwari,daidai lokacin da fiddausi ta shigo dakin dauke da plate din abinci,cikin murmushi take duban shahida "Sannu kin tashi?,ya kike jin kanki yanzu fresh ko?" Eh to,lokacin da tayi baccin ta mance komai,saidai yanzu bayan ta farka komai ya sake dawo mata,saidai baccin da tayi din ya rage mata bacin rai kadan,amma duka ba wannan ba,sallolin data rasa lokacin da take bacci su sukafi damunta,saboda haka tace "Banyi sallah uku ba fiddausi,nunan bandaki na daura alwala"ta fada tana jin babu dadi har cikin ranta,wannan wanne irin bacci ne?,bata taba irinsa ba,hakanan koda bata da lafiya bata taba hada salloli ba. Qofa ta nuna mata wadda take cikin dakin gadon nata,nan shahida ta shiga ta daura alwala,ta fito
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96