Chapter 95
Chapter 95
nan naku bane na matan aure?" Harara ta jefa mata "Ke matar shika ce?" Sai zancan ya bawa shahidan dariya,ta bude robar ta ta soma sha,zaqinsa da dadinsa yasa sai data sha rabi,abun har ya baiwa anty zubaida dariya tace "Ya haka?" "Wannan kam yayi dadi sosai shima" "Tsumin maman farida ne,jiya aka aikomin shi daga zariya"tana rufe robar tace "Amma yayi dadi wlh ya tsumu" dariya ta sake baiwa antyn. Bata gane inda sukazo ba saida anty zubaida tayi parking,wajen da aka mata gyaran jiki ne na aure,saida suka shiga ta gane wai ita antyn ta kawo ayiwa,narke mata tayi don ita sam bata sha'awa,hasalima tasan cewa asarar kudi kawai za'ayi "Don Allah anty,iya qunshinma kawai ya isa" daga qarshe dai da qunshi kawai aka tsira ja da baqi,itama antyn aka mata jaa sannan sukayo gida,zuwa lokacin har anyi sallar magariba,saboda haka tana shiga salla kawai tayi,ko abinci bata ciba ya iso suka wuce. Tun daga falon qasa taga gidan gaba daya kamar ba nata ba "Sama zaki wuce" ya furta mata yana zama saman daya daga cikin kujerun,bata kulashiba ta shige,saidai tayi tayi qofar dakin nata ya budu amma sam yaqi,haka ta dawo falon tana raba ido zuciyarta fal qunci,da gaske kenan ya maidata saman ya saka nafisan a nata dakin?,zuwa yanzu baya falon,haka ta gaji da zama a falon bacin rai na sake cikata,tilas ta haura saman. Dakin da yake kallo nashi ta tura,komai na dakin sabo ne kaman yadda kayan falon saman ma suke sabo dai dai dana qasan,abu daya yasa ta gane dakinta ne takacen kayan makeup dake jere saman mudubinta gasunan jere saman sabon mudubinta,ta jima tana qarewa dakin kallo yadda yatsaru yayi wani kyau,dukka colours din ciki masu kyau da kwantar da hankaline,sai data gaji don kanta sannan ta cire kayanta tafada wanka,tana wankan tana kallon lallenta wanda yayi kyau sosai ita kanta ya burgeta. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Kallo daya zaka yiwa fuskarta ka tabbatar da cewa yau din rana ce ta musamman a wajenta,hakanan farincikin da take ciki ayau din shima farinciki ne na musamman. Ta kasa boye duk wani jin dadi da walwalarta,duk da cewa yadda taso ba duka haka anwar yayi mata ba,dinner daya yaje mata a gaggauce,hatta yau da yake daurin aurensu tana da labarin a makare ya iso wajen,bai kuma jima ba ya koma,saidai duka wannan ba damuwarta bane,da taimakon mima tasan cewa komai zai daidaita,zata kuma samu yadda takeso. "Qawata jimana" mima dake tsaye dankwali gaban goshi ta fada bayan ta gama yiwa duk yarinyar dake madaidaicin falon nafisan kallon tara saura "Kowa zaici uwasa" ta fadi a ranta,shigowarta kenan ita dinma batazo da wuri ba,ta jima tsaye daga waje tana kallon yafda nafisa ke wani rawar kai kamar zata taka kan shege "Gani,ta samu ne?" "Eh kusan hakanne,amma qawata,bayan sauran event da ango baizo daurin aurenma ance a makare yazo ko?" Tabe baki nafisa tayi da alama tadanji haushin abun "Hmmmm,wallahi in gaya miki mima,ban sani ba ko waccar matar tashice ta tsaidashi Allahu a'alamu" Sake tabe baki mima tayi "Waxai hanashin idan ba ita ba?,kinga abinda nake gaya miki aiko?" Sanyin jikin nafisa yayi,saita zubawa mima ido kawai tana kallonta,da alamun neman mafita take,hakan yayi dai dai da tsarin miman,saboda haka tasa hannu cikin jikirta ta fito da wani qullin baqar leda ta soma warwareta,layune tafka tafka guda biyu wanda jikinsu yake wani iri babu kyan gani ta nuna mata "Wannan,ki tabbatar ayau ko gobe idan an kaiki kin maqalata gefan gadonki" ta ajeta ta dauko wasu baqaqen garin magunguna da wani mai kama da man shafawa saidai kore sharr yake "Wadan nan kuma kin gansu?" Tafada tana duban nafisan sosai,alamun maganar da zata gaya mata babba ce "Kin gansu dakyau ko?"ta sake jaddada mata,gyada kai nafisan tayi tana kallonsu tana kallon mima "qananu ne amma amfaninsu yawa ne dashi,wadan nan da kike gani idan kikabi doka da tsarinsu to rayuwar gidan aurenki zata inganta ta tafi yadda kike fata,idan kika tsallake doka daya ko sharadinsu to kuwa babu shakka kjn wargaza komai,kuma komai zai iya biyo baya" cikin nuna zaquwa da qaguwa ta gyara tsaiwarta tana cewa "In sha Allahu ba abinda zai faru,gayamin ya amfaninsu yake" sai data daure ta miqa mata sannan tace "Daga randa za'a kaiki gidanki zaki jiqa kowanne kiyi tsarki dashi,mai kama da man shine na shafawa,zakiyita amfani dasu har tsahon watanni uku cif cif,sharadinsu sune,idan kika soma amfani dasu babu maganar kwanciyar aure harsai kin kammala,kinga kenan daga randa xaki shiga gidanki harki kammala amfani dasu ba zaki bawa anwar kanki ba harsaikin gama amfani dasu,ammafa daga randa kika gama amfani dasu yasanki a 'ya mace ko?" Sai tayi shuru tana juya idanunta sannan tace "Uhmmm.....abun ba'a magana kawai" ta furta murmushi na qwacewa fuskarta,shuru nafisa tayi tana nazari,da alamu ta shiga damuwa,cikin zuciyarta tana jin babu dadi,ba qaramin buri ta cuwa first night dinta ba,tayi alqawarin saita hana shahida bacci a ranar saboda tayi tayi anwar ya kaita gidansa na alfarma data sani wanda da yake zaune a ciki amma yaqj,gidan da xai kaitan sam yayi mata qanqanta "Yanzu har watanni uku kenan ba wani mu'amala tsakaninmu?" "Eh...indai kinanson samun yadda kikeso,idan kuma ba haka ba,kina iya bani maganina na juya dashi,saiki shirya fuskantar duk wata rayuwa da zaki gani" da sauri ta janye maganin ganin mima ta miqo hannu tana cewa "A'ah,Allah na tuba don dai wata uku kawai?" "Ah to nima shi na gani,kuma gidan nan bake kadai bace bare kice akwai matsala,idan ya matsu ya tafi wajen dayar" harara nafisa ta watsa mata cike da kishi "Tabdi,lallai ma,to bari kiji,nijin kaina nake ni kadai nake wallahi" dariya mima ta kwashe da ita harda tafa hannu tana duban nafisan,yayin da nafisan ta taka tayi gaba ta koma cikin mutane yana yiwa miman godiya,juyawa tayi mima ta fice daga gidan tana sakin murmushi don tace mata ba zata zauna ba akwai inda zata,amma anjima da ita za'a kai amarya. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Sake dawowa yayi jikin qofar karo na babu adadi,tun kafin ya fita daurin aure take cikin dakin kuma taqi fitowa,yayi juyin duniya amma taqi tabude mishi,ko bata fada ba koda bai sani ba jikinsa ya bashi kuka take,dalilin daya sanyashi makara baije akan kariba kenan,bayan yaje ya dawo kuma nanma ko reception din da aka shirya bai tsaya ba yayo gida saidai jiya iyau,daga qarshe badon yaso ba ya yanke tilas ya kira anty xubaida ya gaya mata. Sakin ajiyar zuciya tayi tana aje wayar bayan gama doguwar waya da sukayi da anty zubaida da kuma zunnurah,ita kanta tanason tayi controlling kanta amma ta kasa,wani irin bacin rai da baqin ciki ke taso mata,tadan dauki wasu mintuna a zaune a wajen sannan ta miqe ta shiga bandaki,ta hada ruwan wanka mai dumi sosai tayi wanka,already ta riga data sauko ta gyare gidan tun sanda taji fitarsa,shi kadai dinne kawai batason gani,amma dole ta haqura ta dauki maganar anty zubaida da zunnurarta,donta wuce komai a wajenta. 'Yar madaidaiciyar kwalliya tayi cikin wani sabon coffe lace me adon silver pink da golden,sosai ta dinkin ya tsaya mata,hakanan lace din yahau fatarta qwarai,ta saka awarwaro dan kunne da sarqa duka silver ta wadata jikinta da turare. Dai dai nan taji ana sake knocking,ta kalli qofar ta dauke kanta,sannan ta soma takowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96