Chapter 88
Chapter 88
yake shinshinar kowanne lungu da saqo na jikinta yana fitar da numfashi,ko ina jikin shahidan rawa yake itama,karon farko da irin hakan ya soma faruwa da ita a rayuwarta,tsoro da haushin anwar din ya cikata ganin da gaske yake yau ba wasa bane,kaman wanda aka tsikara ya saketa da sauri gami da turata baya shima yaja baya da hanzari yana zama gefan gado ya dafe kanshi dayaji ya sara masa lokaci daya "Ya Allah" ya furta yana ci gaba da dafe kan nashi,hanqota kawai yayi sanda take rungume jikin wani,bayaso ire iren wadan nan tunanukan su dinga dawo masa kwanya,saboda haka saiya dinga maimaita "Hasbunallahu wani'imal wakil" tana zuge zif din rigarta tana mamakin yadda lokaci guda yasaketa haka,yanayin da taga ya shiga din,saidai itama ba'a nutse take ba saboda haka tana gama jan zip din nata ta soma tattaki cikin hanzari zata fice "Dawo nan!" Ya fada cikin kakkausar murya,ba musu tadawo din ta tsaya cak saidai bata dubeshi ba,fuskarshi a dinke take tsaf babu fara'a ta sisin kwabo "Shiga ki hadamin ruwan wanka" jikinta a mace take takawa zuwa bandakin,ta hada mishin ta fito ta shaida masa,saiya miqe kawai ya zari towel "Karki tafi saina fito" ya fada yana shigewa cikin bandakin,tsayawa tayi cak,ta jingina da madubi tanajin yadda qafafunta suka mutu,jikinta babu qwari sam,ta soma tuna yadda taji daxun da yadda abun ya kasance,saita lumshe idanunta tana tuns komai,qamshin jikinsa daya goga mata yana zarya cikin hancinta har zuwa qwaqwalwarta,kasala na sake saukar mata,qarar da wayar tashi ta sakeyi ita ta katse mata duk tunaninta ta sanyata bude ido,bata tabata ba sai dubanta data kai kan wayar,sunan nafisa ne dai again,saita ci gaba da kallon wayar harta katse,tana shirin dauke idanun nata wani kiran ya sake shigowa. Ci gaba tayi da kallon wayar har kiran ya sake katsewa,duk kiran daya shigo din kan idanunta ya dinga shigowa yana katsewa,wanda a qalla kafin ya fito din an kira yakai sau goma sha biyar,kuma ba'a fasa kiran ba,bata dauke idonta ba itama saida taji ya soma qoqarin bude qofar bandakin sannan ta kauda kai tana tunanin wace wannan haka?,meye ya faru take jero kira haka ba qaqqautawa?,bakin mudubin ya tako saita matsa gefe tana sake dauke kanta wani sashen,towel ne daure a jikinsa iya qugu,sai wani daya ratayo wanda duka duka bai gama rufe jikinsa ba gaba daya,wani nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,gabanta ya dunga faduwa sosai,ta sake dauke kanta yadda ko inuwarsa ba zata gani ba,baice mata komai ba ya daga wayar ya duba mai kiran,duka nafisan ce,cikin zuciyarsa yaja tsaki yana tambayar kanshi me zata masa?,ya aje wayar yana cewa "Kije ki shirya,zamuje duba anty usaina batajin dadi" waiwayowa tayi cikin faduwar gaba da fargaba,bala'in kunya da nauyin anty usainan takeji,yanzu kuma zai kaita gidanta?,saidai a kamatance ma bai kamata ta musa masa ba kodon karamci irin na anty usainan da qaunar da take gwada mata. Tana shiryawa amma kiran wayar ya tsaya mata arai,ta rasa dalili,kiran sai takega kamar yayi yawa,a haka ta gama shiryawa tsaf cikin wani lace,ta yane kanta da yalwataccen mayafin daya dace da shigar tata,saidata dubawa anty usainan abinda zata kai mata ta saka cikin jakar hannunta sannan ta fito,a falon qasa suka hadu,saita tsinci kanta da satar kallonsa duk da bata shiryawa hakan ba,anwar badai wanka ba,tunda can tun lokacin da bashi da komai mutum ne mai tsafta da kwalliya ma gaba daya,yayi kyau cikin yadin kufta na maza,dubanta yayi sosai wannan karon kanshi tsaye babu boye boye "Wannan qamshin yayi yawa" yana takowa zuwa gabanta,tuna abin daxu daya mata tayi saitayi hanzarin jaa da baya kada ya maimaita,don har yanzu jikinta a mace yake,tsayawa yayi cak saiyayi murmushi cikin ranshi,ya gane me take gujewa,itakam ba wani turare ta saka ba bayan na jikinta,juyawa yayi ya fice ta mara masa baya. Zata shiga baya kamar yadda ta saba masa taji qofar taqi buduwa,haka tayita qoqarinta na budewar amma taqi da alama lock ya saka,dole ta dawo gaba ta bude ta shiga. Horn biyu maigadin ya dage masa gate din ya saka motar,ya qaraso suka gaisa da anwar din sanda yake fitowa daga motar,suka soma takawa zuwa cikin gidan,suna gab da valcony din da zata sadasu da qofar falon tana fitowa cikin doguwar riga da yalolon mayafi,hada idanu sukayi da anwar,saita kasa dauke idanunta daga kanshi,gabanta na faduwa qaunarshi na sake ratsa zuciyarta fiye dada,sai taga kaman an qara masa kyau da haske,ga wani kwarjini na musamman da gake fitarwa,shi ya soma janye nashi idanun ya soma yin gaba,suka hada idanu da shahida dake bayanshi,kowacce nata idon cikin na 'yar uwarta,sake kallon shahidan nafisa take sama da qasa,kishinta na ratsata,ta sake kyau da aji fiye da daa,duk da cewa ba zata taba mance fuskarba,duk da cewa ta ganeta amma saita janye idonta daga kanta ta rufawa anwar baya,tana jin wani abu na sukar zuciyarta,da kallo tabi bayan shahidan har suka wuce,sannan taja qwafa ta wuce,tanajin a zuciyarta wannan karan kam ba zatabi shawarar mima ba,zuciyarta takai maqurar da bazata iya jurewa ba. Yana gaba tana binsa a baya cike da kunya har cikin babban falon anty usaina,gaba daya yaran suke miqe suna musu sannu da zuwa,sa'ida ta soma tare shahida ta rungumeta "Oyoyo anty,uncle,amma bakacemin zakuzo da anty ba yau" "To ai gata kin ganmu" ya bata amsa yana zama saman daya daga cikin kujerun,yayin da maibin sa'idan ta haura sama donta shaidawa anty usainan zuwan sun tana cewa "Yanxu ma tahau saman,anty nafisa ce tazo dubata" cikin shi da shahidan ba wanda yace komai ba,itakam nunawa ma tayi kaman bata santa ba bare ta ganeta,sunata taba hira da sa'idan,yayin da shi kuma ya shiga tunanin me nafisan tazoyi gidan anty usainan?. Dawowa tayi ta shaida musu tace su hau saman,shine dai a gaba tana binsa a baya har suka bayyana wani falon dake daman,anty usainan na zaune qasan carfet suka shiga da sallama,fuskar anty usaina wadace da fara'a takewa shahidan lale kota anwar ma bata biba,a kunyace ta zauna gefan anty usainan tana jin anwar na tambayar antyn fitilun harabar gidan da wasu suka mutu "Ka qyalesu hakanan tunda dai gidan da haske ai shikenan" saita sake maida kanta ga shahida wanda kanta ke sunkuye a qasa,gaidata tayi a kunyace anty usainan ta amsa cikin kulawa,Shahidan ta mata sannu da jiki ta amsata "Aina warware alhmdlh,shine sai daya tattagoki" qaramin murmushi ta saki kanta a qasa cike da jin kunya da nauyinta,daidai lokacin sa'ida ta shigo dauke da tray wanda ta cikashi da kayan ciye ciye,kai tsaye ta aje gaban shahidan,ta durqusa tana zuba mata duk abinda ke cikin farantin,qasa qasa shahidan ke kallonta tana dariya idanu a waje yadda su anty usaina bazasujiba tace "Sa'idah,wannan duka?,aisai cikin antyn taki ya fashe" "A'ah anty kici wallahi,yauke baquwarmuce ta musamman" "Mu kuma aisai a koramu ko?,yauni aka yiwa danwaken zagaye saboda kin ganta ko?" Tana dariya sa'idan ta daga kai daga shiryawa shahida cake da take cikin plate ta kalleshi cikin dariya "Ba haka bane uncle nina isa?,kawaidai nasan ka gayamin cewa kaida anty abu guda ne,kaga idan na bata kamar kai na baiwa" murmushi yayi yana daga mata hannu yana satar kallon shahidan,shi sam ya mance daya gaya mata hakan,ya fada ne a gaban anty usaina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96