Chapter 39
Chapter 39
me nayi maka?,me yasa kakeson sanya zuciyata cikin rudani,kasan ya nake ji duk sanda na kiraka baka daga ba,ko na turo maka saqo baka karanta ko ka turamin reply ba?" Idanunshi ya daga ya dubeta sai ya sake kautar dasu yaci gaba da abinda yake,tunu qwalla ta cika mata idanu,ta tsani wannan miskilancin nashi ya motsa,wahala takesha,tana ji a ranta duk sanda ya soma shariya irin hakan kaman dai ya tuna tsinanniyar yarinyar da yanzu tsanarta ta ninku a zuciyarta wato shahida,data sani baya ga rabasun da tayi ta nakastata yadda ko da wasa ma bazai sake kawota cikin zuciyarsa ba,amma data taba masa zancan ya tunata ne ranar taqa zallar bacin rai,ya gaya mata karta sake mishi wannan zancan don ba huruminta bane,sannan kuma karta sake masa maganar wata shahida,abinda ma yasaka ranta ya danyi sanyi kenan,ta cika da fatan Allah yasa tabar ranshi kenan har abada. "Meye laifina dear..." Ta fada cikin son fashewa da kuka,saiya tattara dukkan abinda yake gefe guda ya rufe system din sannan ya daga kai yana dubanta duba na kai tsaye,yana fata Allah ya yaye mata wannan son da take masa,sam ko kadan shi hakan baya masa dadi "Ni na aikeki kona bada daman ki bada sanarwar engage dinmu rana ita yau?" Kai ta girgiza tana dubanshi hawaye na sake cika idanunta "Wannan wacce irin banzar dabi'a ce,mu yahudawa ne nafisa?" Nan ma kai ta gyada saidai cikin ranta tana jin dadi da sauqin radadin da take ji,ta zaci wani babban laifi ne ta aikata,koya ganta ne ranan nan da saddam randa sukaje dinner din abokinsu,wanda basu dawo ba sai sha biyu da rabi na dare,ita a ganinta wannan sam ba laifi ne ba,hasalima saika isa ka qasaita ka amsa sunanka wani sannan za'a ga wani abu daya shafi event dinku a gidan talabijin din "Kayi haquri,kuskure ne,bani na biya bama siyama ce tace lallai a saka" "Siyama....ita tace rana ita yau din kiyi wani bikin engage namu kenan?,ohk tunda haka ne rana ita yau din ita saita tabbatar da abun kota tursasani" ya qarashe fada yana janyo wayarshi dake gefe,da sauri ta riqe hannun nashi don tafison a kawo qarshen komai,bata jurewa fushinsa,jinsa take har zuciyarta,kallonta da yayi ya sanyata saurin janye hannun nata,yasha mata kashedin tabashi ba sau daya ba ba sau biyu ba "Don Allah dear don Allah,wallahi na fasa ba za'a yi ba" yana da tausayin mace hakanan mutum ne shi da tun asali yake tausaya raunin 'ya mace ko wacece "Kome mutum xaiyi ya kamata ya dinga duba da abinda bai sabawa addini da al'adarsa ba,sannan ka dinga dogon nazari da tsinkaye a duk lamarinka kafin aiwatar dashi" "Kayi haquri" "Ya wuce" ya fada a taqaice "Yanzu daga ina kike?" Kame kame ta soma yi,don tun dazun suka fito gantali ita dasu mima,yanzu haka suna cikin mota su suka rakota bashi haquri,ko hajiya bilkisu ma batasan tazo ba,ganin ta rasa qwaqwqwaran abun fada guda daya ya dakatar da ita "Is ok...yanzu ki wuce gida" "To yaushe xakazo?,kwana biyu ma gaba daya ka daina zuwa ko cin abinci,mama nata complain" ta fada cikin shagwaba "Zanzo da zarar na samu dama" "Can i call you anjima?" Ta sake tambaya,idanunsa ya lumshe kana ya bude,don maganar ta soma isarsa "Allah ya kaimu anjima" miqewa tayi ta masa sallama cikin salon nuna qauna sannan ta juya ta fice daga gidan,ajiyar zuciya ya sauke sanda yaji fitarta,saiya hada kayanshi gaba daya don zaman gun har ya fita akanshi kuma. Bacci ya samu yadanyi,qarfe hudu ya tashi,yayi alwala ya fice masallaci,daya dawo ya shiga wanka ya shirya tsaf cikin dogayen kaya wanda bai fiya sakasu ba,ya dauki wayoyinshi da maqullin motarsa ya fice,ya yiwa mai gadin sallama ya wuce. Tafiyar mintuna qalilan ta sadashi da gidan anty usaina,suka gaisa sosai da mai gadin qofar da yake shiga,saidai qofar ana gyaranta ne saboda gate din yana masa tauri bai buduwa da sauri,tilas yayi rivers ba don son ranshi ba ya zagaya ta daya layin. Idanunshi fes yana iya hangen qofar gidan daga qofar gidan anty usainar,a hankali ya dauke kanshi yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,horn daya yayi aka bude masa don tuni ya zagayo mai gadin,ya saka motar tashi yayi parking sannan ya kasheta ya fito. Anty usainan ya tadda da yaran ta zaune cikin valcony din dake gefan matattakala hudun da zata sadaka da babban falon gidan,assigment sukeyi,dukansu suka hada baki suna masa sannu da zuwa cikin girmamawa ya amsa,har ta miqe zasu shiga ciki taga yana zare sau cikinsa "Barni daga nan anty na zauna cikinsu nima,sati biyu kenan bamu hadu ba" da d'aya da d'aya ya dinga bibiyar karatunsu,yammata masu kimanin shekara sha hudu sha biyar da sha shida,sai namiji mai shekara sha uku,yaji dadin yadda yadda ya samu karatun nasu na tafiya daidai,wansa daga qarshe ya sallamesu da kyautar dari biyar biyar suka shige cikin gida suna murna,wajen ya rage daga shi sai anty usainar. "ya jikin naka?"anty usainar ta tambayeshi bayan sun gama gaisawa,dubanta yayi "Waye yace bani da lafiya?"gajeran murmushi ta saki "kana tunanin zaka iya boyemin ne,tun zuwan da kayi cikin wancan satin nasan baka jin dadi" "Don dai karkice na musa miki ne...amma da nace lafiyata qalau,kawai stress ne na wajen aiki" kai ta kada kawai,tasan dama bazai taba yarda ba,baisan tsohon abu bane wannan a wajenta,ta karanceshi ciki da bai "Hakane....Allah ya taimaka to" "Amin" ya amsa yana ciro wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo,nafisa ce,ya karanta ya maida mata da thanks sannan ya maida wayar idonsa kan anty usainan "Dama inason muyi wata magana ce da kai" "Toh anty,Allah yasa ta samu" "Eh to.....zancan nafisa,munyi magana da ita ta sanarmin kace rana ita yau kakesan suje su sami alhj abba,amma saga bangarenka banji kace komai ba har yanzu,ya kamata fa anwar ka maida hankalinka jikinka,da da yanzu ba daya bane,kullum shekaru qara yawa suke akan mutum,baya ga haka ma ya kamata mu fita kunyar yarinyar nan da iyayenta" shuru yayi yana saurarenra idanunsa na kallon carfet din da suke kai,har sai data kammala sannan ya dubeta cikin nutsuwa da jeranta kalamai "Anty,har yanzu banji nutsuwa da gamsuwar nafisa ta zama mata agareni ba,har yanzu ina qoqari da tsarawa kaina yadda zan amshetq,bana son ayi abinda daga qarshe zai xama wani batu na daban,ina matuqar ganin qimar mama da abbanta,ina ganin mubi komai a sannu har zuwa sanda komai zai dai daita,zuciyata ta amshi abun dari bisa dari yadda ya dace"fuska anty usaina ta canza,har cikin ranta tana jin anwar din zai aikata ba dai dai bane kawai "Anwar,idan ka sauya ra'ayi ne kawai ka furta,har xuwa yaushe kakeson yarinyar tayita zaman jiranka?,tun tana kara har takai ga tana takowa ta sameni da maganar,waishin ma idan bakayi aure ba yanzu sai yaushe xakayi anwar?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da idanu "Duka anty ba wannan maganar bace" "To wacce ce gaya min?" "Kamar yadda na gaya miki ne a baya,har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwa da yadda da soyayyar kowacce yarinya,da nafisa zata haqura dani da nafi kowa murna,saboda zanso mata ta auri wanda yake sonta ba wanda takeso ba" "Maganata ta tabbata kenan,kawai anwar ka fasa auren nafisa kakeson cewa,ka shirya butulci wa mahaifanta" cikin bacin rai ta qarashe maganar "Banason ranki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96