Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,298 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

waye daya sanka yadda kaqi jinin zuwa katsina dole yayi mamakin tafiyar taka" "Neman aure naje,na nema kuma sun bani" saita dakata da abinda take tana kallonshi sosai,saidai bata ga alamun wasa tattare dashi ba,hakan ya sanya ta gyara zamanta "Auren wa kuma anwar" "Shahida" ya fada kai tsaye kuma a taqaice,wani abu taji ya tsarga mata gaba daya ilahirin jikinta,saita aje rezar gefanta ta zauna sosai tana kallon anwar,tana jin wani farinciki na ratsata,da gaske ko mafarki take,shahidan da take tayi masa farautarta?,sun shirya kansu ne koko yaya abun ya faru?abinda ya shiga tsakaninsun dama baiyi girman da zasu kasa daidaita tsakaninsu ba amma har ya zama silar rabuwarsu na tsahon shekaru?,ya zama silar lalacewar soyayyar da kowa yake sha'awa,duka cikin lokaci kadan ya karanci tarin tambayoyin dake yawo a idanunta,qaramin murmushi yayi yana jin wani ciwo cikin ranshi,inama ace yadda kowa ya kalli lamarin hakan yake "Karki damu anty,na rage miki aikin da kiketa yunqurin yine" ya qarasa fada yana son ganin yanayin fuskarta,ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sosai zaman dake nuna ta soma samun nutsuwa "Zuciyata ta kasa karbar rabuwarka da ita ne anwar,inaji a jikina bai cancanci ku rabu ba" "Shikenan ai....yanzu dai anty abinda nakeso kici gaba da zama a yadda ta sanki har zuwa lokacin da komai zai daidaita" sai yanayin fuskarta ya sauya "Komai zai daidaita kamar yaya?,kana nufin baku daidaita ba ka nemi aurenta a haka?" Kai ya gyada mata "Eh kusan hakanne" "Me hakan ke nufi anwar?" "Babu komai,kema hakan kikeso mu kasance tare fa?" Eh...amma zanso ace hakan ta faru ne a lokacin da duk wani sabani dakw tsakaninku ya zama babu shi" "Karki damu anty" shuru tayi tana nazari,yayin da zuciyarta taji ta mata sanyi sosao,ta dinga jin farinciki na shigarta,tana ji babu shakka abune mawuyaci anwar ya samu soyayya irinta shahidan,abune mai wahalar gaske yaso wata kwatankwacin nata son koda shi yana qaryata hakan tasan wani dalili ne nashi na daban daya rufe masa idanu har yake qaryata hakan "Nafisa fa?" Ta sako mishi zancan da take ganin kamar ya manta ne "Ba abinda ya sauya tsakanina da ita" "Tasan da wannan maganar?" "Zata sani anty,zata sani idan lokacin daya dace ta sani yayi" "Shikenan,Allah ya shige gaba ya kauda dukkan abunqi"mai makon ya amsa saiya soko wani zancan "cikin satin nan ne tafiyata,ina ganin ki lissafa duk abinda kuke da buqata don bazan dawo ba saina gama wata biyun gaba daya,aiki ne mai muhimmanci a gabana" "Babu wata matsala,don bana tunanin zamu buqaci komai harka dawo din" 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Ranar juma'a qarfe biyu na rana suma gama shirin tafiya katsina,ga mamakinta sai uncle hisham ya hadasu ita da haidar da faruqu,ganin haka huda itama ta turje saita je,hakan yasa ta hada kayanta duka suka bar gidan sai anty zubaida kawai. Tafiyar tayi mata dadi sosai saboda su faruq,har Allah Allah ta dinga yi su isa,basu jima sosai saman hanya ba suka isa katsina. Sosai daada tayi farincikin ganinsu su duka,ta rasa inda zata sanyasu,kowannensu haba haba takeyi dashi,saida suka ci suka sha suka nutsu qarfe uku na yammaci,a lokacin su faruqu sun fita kewaya 'yan uwa dake nesa,shahida tace ta gaji ba zata iya fita ba sai gobe,jin haka yasanya huda itama cewa bazata bisu,nan tayi kwanciyarta saman cinyar daada suna hira abinsu. Duban shahida daadan tayi bayan ta maida nutsuwarta sosai "Rahama" ta kirayi ainihin sunanta,saita daga kai daga danna wayar da take ta dubi daada "Yau kuma sunan nawa kike sha'awar kira" maimakon ta maida mata yadda suka saba sai tace "Maida hankalinki jikinki ki aje wannan wayar" jin hakan yasa ta sauke wayar saman cinyarta tana kallon daadan "Abinda yasa nace a turomin ke,inason gaya miki cewa mun bada ke kuma mun karbi kudin aurenki" *KIYI SUBSCRIBING,KI TURA WANNAN NUMBER DON SAMUN DAMAR SHIGA GROUP DIN SABON LITTAFINA DA ZAN SOMA RUBUTAWA BAYAN ALQAWARIN ALLAH IN SHA ALLAH* 07038670166 SAUTIN HIKIMA https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata zata tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣7️⃣ Murmushi shahida tayi tana kada kai "Haba tsohuwa,wai gajiyar da kukayi dani yasa har kin soma min irin wannan wasan?,toki kwantar da hankalinki idan ma bugun cikina kike,ana gama azumi aka sallace zan kawomiki dandasheshen angona" "Ni banga miji ba kamar anwar" daada ta fada cikin ranta,amma a sarari saita sake hade fuskarta sosai,ta yadda shahidan zata fuskanci bada wasa take mata ba "Ki dakatar dashi,don hatta sadakinki yana hannu,kuma watanni uku ya rage daurin aurenki" cak ta tsaya ta nutsu sosai tana son karantar maganar daadan,ta fidda gaskiyar dake cikin maganar "Sadakina fa daada kike cewa kun karba?" "Idan baki yarda ba tunda ni sa'ar wasanki ce,saiki jirayi wadanda kike yadda da nasu zancan anjima suzo su shaida miki" tana kaiwa nan ta yunqura ta miqe ta nufi qofar fita,hakan yasa shahida ta miqe zumbur cikin tashin hankali harta manta da wayarta dake seaman cinya ta cimma dadan ta ruqo hannunta,muryarta na rawa tace "Daada....wa kuka baiwa ni?,nidai nasan ba wanda na bawa dama,da nura mukayi magana shi kuma sai bayan sallah mukayi dashi zaizo" juyowa tayi ta kalleta "Mai rabo muka bawa,zama zamuyi mu zuba miki ido sai sanda kika ga damar aure sannan kiyi?,to sakalcina baikai nan ba...idan zaki nutsu ki fahimceni ki nutsu idan ba zaki nutsu ba kuma kici gaba da shiriritar saina qyaleki cikin duhu" dakiya da dukkan juriya ta gayyato,ta soma kokawar maida qwalla da abinda ya tare mata maqoshi tana cewa "Na nutsu,ki gayamin don Allah" komawa tayi ta zauna inda ta tashi,itama shahidan ta koma ta zauna idanunta qyarr kan daadan,kamar ta fiddo zuciyar daadan ta karanta komai haka takeji "Yazo yana neman aurenki,dan mutunci ne yaro da mai mutunci kirki da karamci,bashi da wani aibu ko abun qi,hakan ha sanya ya turo magabatansa,kawunki ummaru ya sanshi kawun nashi gaba da baya,hakanan muma din akwai wata 'yar alaqa tsakaninmu duk da bamai qarfi bace,babu wata matsala hakan yasa aka amshi harda sadakinsa,karki damu karki daga hankalinki zaki sanshi zaizo ya sameki kuga juna,ke kanki kinsan shekarunki a yanzu sun isa ace kina gidanki harda albarkar zuri'a ma,idan baki aure ba shahida yanzu sai yaushe?" Kuka ta fashe sosai dashi,don tana ganin itace hanya guda daya da zata iya samun mafita da ita "Don shekaruna sun soma tafiya wanda har yau basu rufa ashirin da biyar ba kawai daada saiku amshi kudin aure harda sadakin wanda ban sanshi ba?,bansan daga inda yake ba?,bani na turoshi ba?,ba soyayya ko sabo tsakaninmu?,wallahi wannan zubarmin da mutunci kawai da ajina kukayi" ta qarashe cikin kuka wanda yasa huda ta tsaya sak tana kallon shahidan,daquwa daada ta watsa mata "Kinci qaniyarki,makaranta muka zubar miki ba aji ba,wanne aji kike nema bayan na gidan aure?,ba gata muka yi miki ba?" Haushi ya ciyota,saita sake saka kuka "Wanne irin gata daada haka ake gata tsakani da Allah?,kaman na rasa mashinshini?,kawai sai mutum yazo muku sama taka ku karbeshi?" "To yanzu aisai ki hadamu ki zanemu uwarmu,mun miki laifi ko?" Ta fadi tana fiddo idanu tana kallon shahida,wani tashin hankali takeji da bacin rai qwarai,idan taci gaba da magana batasan me zai fito daga bakinta ba,daboda haka ta gwammace ta barwa daada falon kawai,haka

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});