Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,325 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cike da idanunta ta soma silalowa,rikicewa yayi jikinsa ya soma rawa,kafin ya sake furta komai ta bude ledar hannunta garin ciki ya bayyana,kallan garin yayi sannan ya kalleta,tashin hankalin daya sauko masa yaji ya soma yayewa,hankalinsa ya soma kwanciya ganin ba abinda zuciyarsa ta raya masa bane,ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya wadda ta sanya duk wani qarfi na jikinsa raguwa,har sai daya jingina da bishiyar da suke tsaye qasanta yana sauke wata qatuwar ajiyar zuciya "Me yasa zakamin haka?,wannan abincine yanzu?" Sai yanzu ya sake fahimtar dalilin sauyawarta,kuka take sosai,saiya amshe ledar ya dora saman botikin daya aje gefansa "Wannan bai isa ya zama dalilin da zai saka min ke fidda wannan tsadaddun hawayen ba,wanda duk duniya babu kudin da zasu iya sayen darajarsu a wajena.....ungo nan share hawayenki" ya fada yana bata qaramin handkherchief dinsa wanda baya rabo dashi saboda share zufa da yake gwanin zufa ne,hannu ta saka tana goge fuskarta,tsahon minti biyar ya bata don ta nutsu sannan ya bata damar magana "Ohk...yanzu fadi duk abinda yake damuwarki" "Kafi kowa sanin ba haka mukayi alqawarin gina tarayyarmu ba,munyi alqawarin xamu ji dadi da wuya a tare,kukanka nawa ne,kukana naka ne,haka nan dariyarmu,don me zaka boyen wannan?" Murmushi mai kyau da qayatarwa ya subuce masa,kullum kwanan duniya yana jin ana qara masa sonta ne,duk sujjadar da zaiyi saiya roqi Allah yasa shahida mallakinsa ce daga duniya har lahira "A ganina wannan ba wani abu bane Allah ya taimakeki,na jima ina cinsa har kawo yau gashi ina raye ban mutu ba..." Saita mele baki cikin muryar kuka tace "Zancan mutuwa ma kake?....." Kasa qarasawa tayi ta sake sakin masa wani kukan,kanshi ya dafe sosai,ya tsani kukanta,idan yana ganin hawayenta ji yake kaman wani babban tashin hankali ya sameshi "Ya salam shahidaaah....,Allah ya baki haquri,kin manta cewa mu mutu ka raba ne?" Da tausasan kalamanshi dake sawa rayuwarta nutsuwa yayi amfani ya lallasheta sannan suka ci gaba da tafiya,bayan ta sa yayi mata alqawari bazai sake shan gari ba saidai da marmari. Sanda suka isa tsaidashi tayi ta shiga gida cikin sauri,bata zarce ko ina ba sai kitchen dinsu,tasan ba'a rasa abincin a gidan nasu,koda bamai yawa bane amma za'a dafa,foodflask dinta ta dauka ta cika masa shi da taliya da wake sannan ta fita. Yana tsaye harde da hannayensa a qirji,idan ka dubeshi da kyau ya zaka fahimci ya fada zurfin tunani ne,ledar hannunta ta miqa masa baqa wadda babu ta yadda za'ayi ya iya gane meye a ciki,saida dubeta ta masa alama da kai akan ya karba sannan yasa hannu ya amsa "Ka tafi dashi" "Meye wannan din?" "Guba na baka kaci nima naci saimu mutu tare" dariya ta bashi sosai har sai daya dara,itama sai data fada din maganar ta bata dariya "Kinsan kuwa zai zame min abun alfahari...kuma babban labarin da zai karade duniya...masoyiya ta baiwa masoyinta guba donsu mutu tare" murmushin daya qarawa fuskarta daraja da kyau ta saki "Zan iya cin guba don tunkudeka daga cinta" girarsa daya ya dage sannan ya sassauta murya "Idan babu ke ai babu ni shahida....kina tunanin idan kika mutu kika barni zan iya qara kwana daya a duniya" wani far tayi da ido wanda ya sanyashi yin baya da sauri "Inni sa'im...naga alama so kike ki....." Da hanzarinta ta juya masa baya cikin shagwaba tana dan buga qafa alamun batason ya qarasa maganar da yake "Shikenan.....sai anjima,na gode" ya fada yana takawa don barin wajen,tana wajen tsaye harya bacewa ganinta,saita lumshe ido ta saki hannayenta tana sakin siririn murmushi,tsakanin ita da anwar batasan waye yafi wani son dan uwanshi ba,wannan amsar kuwa tasan cewa Allah ne kadai masaninta. Cikin kudinta ta cire dubu uku ta siya qaramar waya sabuwa irinta anwar,ummanta bata hanata ba bare abbanta,sunsan cewa waya ba damun shahidan tayi ba,yanzun ma sun tabbatar saboda anwar ta siya,wanda dukkansu zuwa wannan lokacin anwar ya zama kamar d'a a wajensu,mutum ne da Allah yayi masa baiwar saurin shiha zukatan al'umma,hakan kuwa baya rasa nasaba da hankali nutsuwa uwa uba tarbiyya da yake da ita,ko cikin unguwarsu dattawan nan son anwar suke,kusan kowa zakaga yana janshi a jiki,shi kuwa ya daukesu dukkansu tamkar mahaifansa,dalili kenan daya sanya wasu daga cikin matasan unguwar kejin haushinsa suka kuma qwafa masa,hakanan suka daura dambar sake danqwafar dashi,hakanne yasa duk sanda ya samu wani abu sakakke sai an haura gidan an sace,kama daga sutura zuwa takalma ko d'an kudi,ya rasa su waye?,baisan kuma meya tsare musu ba,shi da bashi da komai?,bai baiwa kowa ajiya ba amma ya tsone musu ido. *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½* πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½* πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 0️⃣9️⃣ Tun daga lokacin ta maida abincin anwar ya zama wajibinta,duk sanda ya nuna alamun turjiya na bazai amsa ba anan ne zasuyi fada,har hakanma ya zame masa jiki. Gefe daya kuwa rayuwarshi sai hamdala kawai,kusan duk wani fadi tashi ya zame ma rayuwarshi jiki,ta fannin kudin registration kuwa ba wani ci gaba da aka samu,iyakar qoqarinsa bai hada komai ba kaman yadda ya saba,yaqi kuma sanarwa anty husaina,tun yana jin babu komai harya soma shiga damuwa,ganin lokaci yana quracewa,sannu a hankali ya soma yanke tsammanin samun kudin ma gaba daya,wanda hakan ya jefashi cikin damuwa mai tsanani,damuwar da tasa anty husaina ta gane halin da ake ciki,ta kirashi tayi masa fada sosai,ta kuma saida dan abinda ke gareta na kudi,saidai kudin basu cika ba,kaso d'aya aka samu cikin biyu,a lokacin ya rage saura kwanaki makarantar su rufe registration. A hankali take takowa zuwa cikin soron nasu,niyyarta ta tsoratashi kaman yadda yayi mata shekaran jiya ya tsoratata,taji tsoro sosai ya koma gefe yana mata dariya yana fadin "Ashe farar kura ce ke bansani ba?". Yau da yazo kan dakalin qofar gidan nasu yaci burki,hakanan yake jin ranshi babu dadi,wanda hakan ya bayyana har gangar jiki da fuskarshi,saidai duk sanda ya tuna yanzu zaiga sanyin idaniyarsa sai yaji yanayin da yake ciki din ba komai bane,wayarshi dage aljihun wandonshi ta dauki qara,ya zura hannunshi a hankali ya zaro wayar,anty husaina ce ke kiranshi,yasan kuma kiran bai rasa nasaba da cikon kudin registration dinsa ba,zayaso kunnuwanta su jiye masa ya samu,saidai ba mai yiwuwa bane yayi mata qarya,abokin kuka shi ake gayawa mutuwa,sannan uwa uba bayaso wani abu ya kawowa karatunshi tsaiko,babban burinsa a yanzu shine ya kammala karatunsa ya samu aiki,ya auri shahidansa ya kuma kula da anty husaina,itama ta huta taji dadinsa "Yaya dai muhammadu an samu cikon kuwa?" Ta tambayeshi bayan ya gama gaidata,cikin nuna kasawa da sarewa yace "Anty ina ganin saidai nayi haquri....wannan karon duk wani qoqarina na samun cikon kudin na gaza,kudin sunqi samuwa....ina tsoron asarar karatuna..." Tausayinsa ya kama anty husaina,tasan abune mai wuya ganin karayar anwar "Kaci gaba da addu'a,ina nan ina nawa qoqarin mu zubawa sarautar Allah ido,in sha

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});