Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hakanan batayi qasa da yawa ba,hakan ya sanya iskar ke kadawa dai dai "Ina ka tsaya haka daga cewa yanzu zaka ka dawo?" Sosai yakejin gajiya da kasala yadan motsa fuska "Wallahi inna..nima ban zaci zan dade haka ba" dauke kai tayi ta kalli jijarta bushira dake xaune tana kallo falon inna tace ta miqawa anwar tuwon darenshi da mamarsu ta aje masa,cikin sabbin fulasai kaman da plates masu kyau harda ruwan sha a jug kaman yadda suka saba masa duk sanda yazo. Qasa ya sauko ya soma zubawa da kanshi duk da cewa ba wata yunwa yakeji sosai ba,amma saboda innar kar tava dazu baici ba yanzun ma haka taji ba dadi "Naje gidan daada ne,kakar shah....." Saiya kasa qarasa fadin sunan "Rahama" ya qarashe fada da ainihin sunanta,wanda baya jin tsahon zamanin da yayi da saninta ya taba ambatar ainihin sunanta "Wacece haka?" "Yarinyar da zan aura..na taba baki labarinta shekara shida baya,wadda ta kasa zuwa gaidaku?" Murmushi inna ta saki "Shahida wai?,yarinyar da usaina ke bamu labari wadda ta damu kan rabuwarku?" Kai ya gyada yana ci gaba da ci tuwon "Ma sha Allah,amma saidai wani hanzari ba gudu ba,ina maganar yarinyar can nafisa 'yar wajen alhajin nan?,ina cewa duka duka watanni aurenku ya rage?,don dama zuwan naka nake jira naji ainihin sati nawa ya rage" "Maganar nafisa tana nan,kuma watanni uku suka rage" "Anya anwar?,kana nufin auren mata biyu lokaci guda?" Inna ta fada tana kallonshi,kai ua gyada "In sha Allah inna,tunda Allah ya hore saidai a tayamu addu'a" shuru ta danyi kadan kafin daga bisani tace "Shikenan...Allah yayi jagora,ubangiji ya kore abinqi" "Ameen"sai daya hadiye lomar bakinsa sannan ya sake cewa "Na shaidama kakartata gobe su kawu zasu je su tambayamin izini a wajensu,to gashi ban samu na sanarwa kawun ba,kuma a goben nakeson na koma saboda na baro ayyuka,ban tsammaci ma yau din zan kwana ba" "Aiba wata matsala bace,ai ado kawai za'a yiwa waya(qaninta kenan)a sanarwa,shehu da dahiru suna kan hanya yanzu muka gama waya,sunje duba ta'annabi,idan suka shigo sai kuyi maganar". Bashi yabar gidan ba sai qarfe goma na dare,sai daya tabbatar komai ya kammala ya kuma tsaru sannan ya nufi masauki,yana fitowa daga wanka yana shirin kwanciya wayar nafisa ta shigo,ya gaji tubus duk da yaga tarin miscal dinta niyyarsa saida safe zaya kirata saboda bacci yake da buqatar yi,dole ya daga bayan ya kwanta sosai saman gadonshi "dear,ina ka tafi ne?,muhsin yace min baka gari" "Katsina" "Me kuma kajeyi can dear?" "Kin manta ina da dangi ne a can?,naje gaida su inna,sannan kuma na gabatar da wani dan aiki" "Au haka ne,me yasa baka hadani da ita ba na gaidata?" "Idan kin matsu kina iya karbar lambarta tunda tana da waya,da can baki gaidata ba saida nazo zakice na baki?" A shagwabe tace "Am so sorry dear,ka turomin number din nata saina kirata" "Saidai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun kam na gaji bacci nakeson nayi" da haka ya samu ya sallameta ya aje wayar tunani nakai kawo cikin ranshi,kenan yanzu idan lamarin ya tabbata mata biyu zai aure kenan?,juya lamarin yayi cikin zuciyarsa,koda wasa bai taba kawowa kanshi xai auri mata biyu ba,sai kuma tunaninsa ya juya kan shahida da nuradden,zayaso yaga fuskar kowannensu a sanda labari ya isa kunnensa,murmushin mugunta ya saki yana mirginawa hannun damanshi ya soma karanto addu'ar bacci bayan ya kunna suratul baqara cikin wayarshi ya rage mata sauti sosai. *ga mai buqatar littafin da zan soma bayan kammala rubutun alqawarin Allah,zaije youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,akwai jan rubutu na SUBSCRIBE daga qasa,zaka dannan sau daya zai koma baqi,sai kiyi screenshoot ki turawa wannan number da zataso daga qasa,za'a sakaki a group din littafin da yardar Allah* 07038670166 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gansu don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣6️⃣ 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Washegari qarfe tara na safiya ya gama shirinsa tsaf cikin yadinsa na maza mai kyau da tsada,yayi masifar kyau yadda hularshi ta zauna kanshi sosai kawai ya isa ya gaya maka ya hada jini da kanawa,hakanan yake jinsa wani sawai kuma fayau dashi,ya qarasa reception yayi maida musu key din dakinsu ya sallamesu ya wuce zuwa gidan inna. Falon inna ya wuce kai tsaye bayan ya isa gidan,ya tadda kawu dahiru da kawu modu suna rumfar innar suna hira da alama anan sukari karin safe tare,cikin girmamawa ya gaida inna sannan ya gaidasu yana zama daura da ita,ita ta yunqura da kanta ta hada masa lafiyayyen kunun tsamiya da sukayi da wainar gero,cikin marmari yake ci suna ci gaba da hira dasu kawu dahirun,yana kammalawa kawu shehu ya iso,basu wani jima ba suka miqe gaba daya zuwa gidan daada,shi yaja motar,kawu shehu da yake shine babbansu yana gaba,kawu dahiru da kawu modu kuma suna baya. Sanda suka isa gidan sha daya na safe har ta dan gota,hakan yasa suka tadda kawun nan shahida sun riga da sun iso,sulaiman shi ya musu jagora kamar ko yaushe zuwa cikin gidan "A'ah....shehu,kardai kacemin yaron dake neman shahida dan wajenka ne?" Kawu ummaru wanda yake yaya ne ga mahaifin shahida ya fada yana dariya sanda sukayi musabaha da kawu shehu "Yaro na ne,dan wajen qanina ne mai rasuwa" " "Kai ma sha Allah,amma naji dadin abun nan qwarai,to ai abunma duk na gida ne,ita kanta daadan ma bata sani ba,inaga basai anje anata kaiwa da kawowa ba,ayi komai kawai a gama lokaci guda" "Kana ganin babu wata damuwa ko matsala?" "Haba shehu,kaine fa,babu wata damuwa wallahi,dama meye burinmu banda muga yaranmu sunata aurensu". A ranar gaba daya kawu ummaru suka amshi kudin auren shahida harda sadaki,aka kuma tsaida lokacin biki ko ince daurin aure a wajen maza watanni uku masu zuww,wanda yayi dai dai da watannin da aka tsaida a farko na daurin aurenshi da nafisa. Yana tsaye jikin motarshi qafafunshi amatuqar sanyaye,irin wannan lokaci ya jima yana mafarkin zuwanshi shekara shida baya,ya qiyasta yanayin farinciki da zai samu kansa a duk sanda Allah ya tabbatar masa a wancan lokaci har baisan sau naya ya qiyasta din ba,sai gashi abun yazo a bahagon yanayi,yanayin daya kasa tantance wani iri ne,farinciki ne ko baqinciki?,kansa ya daga a hankali sanda ya soma jiyo muryoyin su kawu dahiru da alama suna sallama ne dasu kawu ummaru. Ranar kasa shiga yayi wajen daada duk da yaso suyi sallama,haka ya sake dibansu kawu shehu ya sauke kowanne a gidansa sannan suka wuce wajen inna shida kawu modu. Murmushi ne kawai ke fita a fuskar daada sanda 'ya'yan nata ke gaya mata yadda komai ya kasance "haba,ba banza ba nutsuwar yaron ta yimin,naji ya shiga raina sosai,ashe jinin gidan malam usman ne(sunyi zama na maqotaka ne tun iyayensu da kakanni,zaman da sukaji dadinsa,kunsan mutanen daa akwai riqo da zumunci da kuma girmama alaqa da dangantaka komai qanqantarta),na godewa Allah,Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi" "Amin daada" dukkansu suka amsa suna jin dadin hadin "Yanzu daada za'a sanar dasu kenan?"kai ta girgiza "qwarai kuwa,ka shaida ma ita uwartata,sannan kuma ka kira can gidan hishamun a shaida musu,duk da cewa shi ya sani amma sai a gaya masa an karba harda kudin auren da sadaki,gobe idan ka dawo kai ummaru ka kiramin rahamar ka hadani da ita" "To shikenan daada"

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});