Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,297 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

qofar cikin mai fadi ce sai aka saka labule mai shara shara,falon kuma kujerun zaman custumers ne da kuma kayayyakin siyarwa na kwalliya kamansu ribbom,man kitso man shamfo,beads da sauransu. Shagon akwai mutane saidai ba sosai ba,a falon ta tadda mai saloon din tsaye da wasu mata suna siyan ribboms,cikin fara'a da muntuntawa ta tarbi shahidan,saboda tasan duk sanda tazo din ba qaramin qaruwa takeyi da ita ba,suka gaisa sannan tace mata "Kitso nakeso madam,amma manya nakeso yau ayimin ibra nakeso" cikin juyayyar hausarta tace "Ohk madam babu damuwa..saidai akwai wasu da za'a wankewa kai,amma bari na soma sallamarka su sai su jira" "A'ah madam,aisun rigani zuwa sallamesu tukunna" "Ohk maa" ta fada tana juyawa ta duba wani waje da take aje magazines ta zubewa shahidan sannan ta sallami wadanda suke sayen ribbom ta koma ciki inda take wankin kan. Daya daga cikin kujerun dake wajen shahida ta zauna,ta aje jakarta gefe daya sannan ta cire glass dinta da take amfani dashi lokaci zuwa lokaci saboda ado ta dorashi saman jakartata ta bude magazine din ta soma dubawa. Hayaniya da hirar dake tasowa daga ciki ta cika mata kunne har tasa ta daina fahimtar abinda take dubawar,sai kawai ta rufe magazine din ta riqeta a hannu,hirar yammatan dake ciki na shiga cikin kunnenta "Ya hadu iya haduwa,daa wlh ni bai dameni ba saboda a sannan baida wani abun burgewa,amma yanzu har wani kishi kishinta nakejin yana kamani wallahi,anya nan gaba kuwa ba za'ayi juyin mulki ba kuwa?" Dariya suka kece dashi "Mima baki da kyau,daga daukanki sojan haya saiki fadi haka?" "Ke qyale shegiya,shekara nawa ina mata bauta?,don tana biya na aiba halitta ta tayi ba" hirar sam bata wa shahida ma'ana ba,saboda haka ta zaro wayarta kawai tayi kiran ummanta,bayan sun gaisa tace "Umma don Allah ki saka mubina ta soyamin wainar fulawa ina nan zuwa,na tsaya yin kitso ne,ta saka min albasa da yawa,ta manja nakeso" "Toh shikenan,amma saita saukemin tuwona" "Eh kafin sannan ma na qaraso" "Allah ya kawoki lafiya" "Ameen umma" bayan ta kashe kiran noradden ya shigo,ba yabo ba fallasa ta daga "Yallabiya kin hanani sukuni sai naji muryarki" murmushi ne ya subuce mata ba tare data sani ba,ita mamaki ke kamata idan nura na nuna yadda yake tsananin qaunarta "Dariya ma na baki?,don bakiga yadda na gaji tubus ba saboda tunaninki,shahida har yau kina daukan son da nake miki da sauqi" "Ba haka bane,kawai dai haka kai ka fahimta" "Koma yaya ne dai yanzu kin wuni lafiya?" "Lafiya qalau,kaifa?" Sosai yaji dadin yadda ta tambayeshin,daga haka ya shiga janta da hira,ta biye mishi kodan ta ragewa kanta lokacin zaman jiran da takeyi. Minti ashirin 'yammatan da akewa wankin kan daya ta soma daga labulen ta fito,tana sanye da riga dinkin straight gown wadda tafitar da duk wata sura tata,shahidan na shirin dauke kai dayar ta biyo bayanta,itama sak irin dinkin dayar ne a jikinta,har shahida ta dauke kai yadda taga ta zuba mata ido ya sanya itama ta maida idanunta kanta,da sauri taga ta juya ta koma ciki tana cewa "Au...madam na manta qawata tace muyi jiranta a nan" "Ohkey to babu damuwa" ta bata amsa sanda shahida tayi sallama da nooradden ta maida wayar jakarta sannan ta cire rolling din kanta,ta zare ribbom dinta ta soma taje kanta. A gaggauce nafisa tayi parking na motarta a qofar shagon,cikin hanzari da sassarfa ta nufi qofar shiga wajen kai tsaye. A sannan anyi rabin kitson da akewa shahida,labulen kawo sukaga an bankado hakan ya sanya shahida daga kanta ita da madam tawakkaltu dake mata kitson gaba daya,idanunta ne ya sauka cikin na shahida tana mata kallon fes,itama shahidan kallonta take,tasan fuskar,fuskace da ba zata taba manceta ba,fuska ce da anwar ya turo mata da hotunansu a tare yana bayyana mata ita a matsayin masoyiya a gareshi,ta yaya zata manta wannan fuskar,amma saita dauke idonta ta maida kanta qasa tana ci gaba da danne danne a wayarta,saidai wani abu yazo ya tsaya mata cak a qahon zuciyarta. Madam tawakkaltu ce ta amsa mata tana ci gaba da yiwa shahida kitson,saidai idanunta na akanta tana neman jin abinda ya kawota wajen,don bata santa ba "Amm,akwai friend dita mima da tazo wankin kai nan ko?" Nafisa tayi qarfin halin furtawa,ranta da zuciyarta gaba daya a jagule "Eh sunaa ciki aeke sukee jira" ta amsa mata cikin gurbatacciyar hausa,kafin takai ga isa wajen mima ta fito da qawarta lima "Gani...mu wuce ko?" Ta fada tana karantar fuskar nafisan,kaita jinjina yanayin fuskarta na sake sauyawa yana nuna rudani a ciki qarara,har sukaje bakin qofar da zasu fita tana duban shahida wadda bata ma san tanayi ba,saidai jikinta ya bata hakan "Madam ko kinsansu ne?" Tawakkaltu ta tambayeta ganin yadda suke kallonta "Ba wadda na sani a cikinsu" ta amsa mata a taqaice "Allaho ya kyauta" ta fada tana mamakin irin kallon da sukewa shahidan su duka. Duka sai komai ya tsayawa shahidan cak,ba bacin rai takeji ba amma ranta da jikinta sam babu dadi,wayar ta maida cikin jaka ta ciro carbinta ta maqala a yatsanta ta soma jan HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL,wansa babu jimawa taji komai na koma mata dai dai. Dukan sitiyarin motar tayi da qarfin gaske har lima na zaro ido kada fa kan motar ya lalace "Ba haka nakeso na ganta ba mima,ya akayi na ganta a cikin kyakkyawan yanayi?,so nake ta dilmiya ta lalace,so nake tayi nisa cikin shan kayan maye karta waiwayo komai nisan kiran da za'a mata,kudin dana biyaki bai kamata wasan ya tsaya iya nan ba,ya akayi haka?" Ran mima yadan sosu kadan sabida yadda nafisan koda yaushe taqamarta nakan kudin data bata,amma abinka da bariki saita danne "Abinda ya bani mamaki ya girgizani kenan yasa har nayi kiranki" shuru ne ya ratsa motar abun na kaiwa nafisa ko ina,maganar mima ta katse mata zaren tunaninta Ba wannan nakeson jiba,meye mafita?" Ajiyar zuciya mima ta sauke "Toh....a yanzu dai babu batun saka wani kota bar wani ya shiga jikinta,na tabbatar ba zata sake barin haka ta faru ba a gareta...amma dai duk da haka,ba'a rasa nono a riga,ki fidda kudi,zansan aikin daya dace muyi a kanta,amma....kece zakiyi rabin aikin,ke kike tare da anwar kuma zakici gaba da kasancewa tare dashi,dole ki sake cusa masa tsana da qinta cikin zuciyarsa,kisan yadda zaki ki mamaye tunaninsa ki shiga lungu da saqo" "Kudi ba damuwa bace,successful aiki shine damuwata" "Karki samu damuwa,kinsan wace ni,nayi kin gani ai" locker motarta ta bude ta ciro kudi ta irga ta miqa mata,tasa hannu ta cafesu tana sakin murmushi "Koma sit dina ki jamu,don bazan iya driving ba a yanzu" "Ohkey" miman ta fadi,sukayi musanyan seat ta kunna motar ta figeta,wata ta sanya musu nafisa taja tsaki "Ina cikin irin wannan mode din zaki kunnan waqa,kashe malama ki barni nayi tunani da kyau" "Daqiqiya wanne tunani gareki?,bayan duk wani tunaninki nice nake miki" ta fada a zuciyarta tana cire waqar,yayin da a fili tace "Am sorry,komai fa zai dai daita". Qarfe shida ta shiga soron gidansu bakinta dauke da sallama,tsakar gidan nasu babu kowa sai mubina dake zaune saga qofar kitchen tana suyar wainar fulawarta,fes gidan yake kamar kullum,cikin gajiya ta qarasa inda mubina ke zaune "Sannu da zuwa yayaa" "Yauwa mubi...ashe kin soma?" Tayi maganar sanda take duqawa ta

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});