Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 92

Chapter 92

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

duba,idan lafiya lau shikenan babu buqatar sake damuwa ko saka ido. Zai fita ita kuma zata shigo,kusan lokaci daya suka murda handle din,baya tadanja kadan bayan ta dubeshi ta dauke idanunta,sai taga kaman ya fada kadan daga jiya zuwa yau da kuma fitar daya sakeyi da dawowarsa,ganin alamun fita zaiyi sallah saita juya ta soma sauka tana cewa "Sannu da zuwa" "Yauwa" ya amsa yana tsaye cak yana dubanta sanda take sauka din,yanajin kaman ya rintse ido ya bude yaga duk abinda ya farun da wanda ke faruwa a mafarkine,bai taba kwana ya kwatanta a ranshi ko sau daya rayuwar zata iya zuwa musu da wannan salon ba,dai gashi lokaci daya komai ya canza,komai ya tabarbare,komai yazo da cikin wani bahagon yanayi. Karon farko tun bayan rabuwarsu dayaji wani abu mai kama da tausayi tausayi akanta saboda tuna cewa nan gaba kadan nafisa xata shigo gidan a matsayin kishiya a wajenya,ya tuna yadda mata ke komawa duk sanda zance makamancin haka ya shiga kunnensu yatuna yadda nafisa ta birkice a sanda labarin wanzuwarta qarqashin inuwa guda ya shiga kunnenta,a sannanma bata zama qarqashin ikonsa na,basu taba kwana qasan rufi guda ba,inaga ita?,duk da bashi da tabbacin cewa zataji wani abu ko zata damu,saboda dukkan dalilin dake sawa mace tayi hakan babushi tattare da ita. "Kidan samu kifi ki dafaminshi idan ba damuwa,zanje sallah na dawo" ya fada cikin laushin murya wanda har hakan yaso bata mamaki,saita juyo tana kallonshi,suka hada idanu ta sake dauke kai ganin yadda ya kafa mata idanu,taji kallon nata har cikin jikinta,sai taba baiken kanta data sanya kaya irin wannan ta zauna haka ko mayafi babu bare hijabi,amsa masa tayi da to tana ci gaba da sauka daga benan,har sai dayaga bacewarta sannan ya sauko shima yawuce masallacin. Sai data soma shiga daki ta samu dan qaramin hijabi ta saka sannnan ta wuce kitchen din har yanzu tana mamakin irin salon da yayi mata magana dashi,ta ciro kifi ta gyarashi,ta kauda wancan tunanin na farko ta fada tunanin yadda zata sarrafashi ta yadda zai dace da yanayinsa,wani gashi ta tuno mai kama da romo romo da takanga anty xubaida bayi,ba bata lokaci ta soma hadashi,wanda cikin mintuna qalilan ta kammala,qamshi kuwa ya cika gidan ko ina,ta gyara komai a kitchen din ta gogeshi sosai yadda ta saba sannan ta fito don barin kitchen din. Tunda ya dawo yana falon a zaune yana shaqar qamshin kifin har cikin zuciyarsa,da mamaki tadan dubi sashen da yake din,don iya zamanta a gidan batace ga sanda ta ganshi zaune haka sosao cikin falon ba,kamar yasan da tsaiwarta shima ya waiwaya yana dubanta,yabi hijabin jikinta da kallo,shima hakan yayi masa don tamkar gata tayi masa,baisan me yasa takeson ta zame masa tamkar wani maganadisu ba ko mayen qarfe aduk sanda ya ganta?,baisan me yakeson sauyashi haka ba,bayan a baya yasan bai damu da dukka shigarta ba,amma cikin abinda bai gaza sati biyu ba yanason sauyawa gaba daya?. *Alqawarin Allah* 44 Komawa tayi da baya kitchen din ta shirya komai ta dauko kan tray sannan ta sake fitowa "A'ina za'a aje maka?" Nuni yayi kata da gabanshi,ta qaraso nan ta aje ta shirya komai ta dauko sauran na wajen dining shima ta shirya masa,tayi sarving dinsa sannan ta yunqura zata miqe saiya dakatar da ita yace ta zauna,ba musu ta koma ta zauna din,saidai duka bata jinta dai dai,baiyi magana ba harya qare cin abincin sannan ya soma da cewa "Da can kafin aurenki ina tare da wata yarinya nafisa wadda har an saka mana rana lokacin biki ya rage saura sati uku,to wasu abubuwa suka biyo baya wanda ya zama silar fasa auren namu a wancan lokacin,a yanzu maganar ta dawo wanda ina tunanin duka ba za'a wuce sati uku ba nan gaba" bata taba tunanin zataji irin abinda taji a zuciyarta ba'a yanzu,tunda ya ambaci sunan zuciyarta da idanunta suka haska mata ita,saita dinga binsa da kallo kawai sanda yake bayanansa,gaba daya saita daina fahimtarsa,duka bayanan da yake kawai tana ganin yana yine saboda radin kanshi,yarinyar daya aiko mata da hotunanta sanda take tsaka da radadin rashin mahaifinta?,yarinyar daya turo mata da fuskarta sanda take tsaka da jimami da alhinin rabuwa dashi?,yarinyar daya kawo mata hotonta ta gani cewa ya samu wadda ta fita?,ya sauya wata a madadinta,a yanzu ita zai aura ya kawo gidan?,shine yake wani rufa rufa dason yiwa zancan kwaskwarima?,tana ganin abu mafi sauqi kawai ya fito ya gaya mata zai cika muradi da burinsa ne,yanzune manufar da yasa ya aureta zai bayyan muraran baro baro,me yayi saura?,me xata xauna taji daga bakinsa,ai komai ya qare hakanan komai ya fito fili,sai kawai ta miqe sanda yake tsaka da bayanin nashi,binta yayi da kallo ganin ta soma tafiya zuwa hanyar dakinta ba tare data ko waiwayeshi ba,kiran sunanta ya soma yi abinda ya jima rabonshi dayin hakan,saidai ko daya bata saurareshi ba bare taji me yake fada,da hanzari ya miqe ya bi baya,taji takun tafiyarsa,saboda haka tana shiga dakin ta saka key,ta samu gefan gadonta ta xauna ba tare datasan me zata tuna ba,wani kuka ne mai sautu ya qwace mata wanda ta kasa tsaidashi,hannunsa saman kanshi yana yamutsawa jin sautin kukanta dake ratso har inda yake tsaye "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta yana kallon qofar dakin da yayi juyin duniya ta bude taqi,bai taba xato ko tunanin xata damu ba ko sau daya,me yasa ta damu?,me yasa ranta yw baci?,bayan ta gaya mishi cewa bata qaunarshi ko kadan?. "Me yasa kike kuka shahida?,kukan me kike?,kins kukane saboda mutumin da kika dainaso xai qara aure?,ko kina kuka ne saboda mutumin daya daina sonki xai auro wadda yakeso?,muradin zuciyarsa?,haske rayuwarshi?,meye abun damuwa a ciki shahida?,har yanzu anwar na cikin zuciyarki ko kuwa?" Tambayoyin da zuciyarta ta dinga mata kenan wanda yasa ta soma tuhumar kanta da kanta. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Duban nafisan mima takeyi sosai da wani irin banzan kallo,cikin ranta ji take kaman ta tashi ta shaqe nafisan,cikin ranta tana ala wadai da sakacin da tayi har ta bari tunanin nafisa yakai gata nemi anwar karo na biyu,tabbas da tasan da irin wannan ranar da tunu ta saka almakashi ta datse alaqar da tayi saura tsakanin anwar din da nafisan,koda yake a yanzu ma bata baci ba,saidai kuma ba haka taso ba,dole ya saka taka tsantsan da nutsuwa dinta wargaza tsakaninsu,don a yanzu bata da burin daya wuce ta ganta itama gidan anwar din a matsayin matarsa,sake duban nafisan tayi a karo na biyu yadda taketa faman fara'a,bakinta kamar zai hade da kunnenta,irin kallon da miman ke mata yasanya jikinta yadan soma sanyi "Ko bayi dai dai bane hajjaju?,bafa zan iya haqura da anwar ba matuqar ina raye shima yana raye" baki miman ta tabe tana ci gaba da dubanta "Dama aida kin jira ni nidin xan miki wannan aikin,abinda yasa kika ji shuru ba'a kai gabar bane,naso mu gasashine harsai ya kawo kanshi da kanshi ta yadda koda kin shiga saikinfi daraja da qima a idanunsa,amma a yanzun yadda kikayi wallahi qimarki ta zube qasa warwas,kuma haki da wata fuffuka da xakiyi idan kin shiga gidan,hasalima ba baiyi matsuwar shigowarki gidan ba kinga baki da abun cewa sawa ko hanawa koda kin shiga gidan" sai jikinta ya danyi sanyi,taji maganar mima tabbas tana kan hanya,shigen maganar da mummynta

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});