Chapter 80
Chapter 80
ba,abinda ya debe mata kewa kenan har wata washegarin,saidai randa ta cika kwana na hudu dif kakeji,duk sai taji gidan babu dadi,haka ta wuni ita kadai,daga kwanciya sai kallo sai latse latsen waya,har zuwa dare data kammala abinda take tayi shigewarta daki. Tunda ta gama yin baqi bai kuma sakata a idanunsa ba,kafin magariba ta gama komai tayi shigewarta daki,bata fitowa sai washegari shima idan ya fita a gidan,zatayi abincin safe haka na dare ta aje masa,saidai shima bai bata taba abincin ba,yadda ta jera haka zata kwashe abinta,kusan hakan na faruwa ne saboda ya koma aikinsa gadan gadan,bai samun damar dawowa gidan dawuri,hakanan da wuri yake fita. Sati biyu cur aka suka kwashe a haka,idan ya dawo bai ganinta,hakanan idan zai fita ma haka. Zaman taji ya isheta,kadaicin ya mata yawa,tayi kallo har ta gaji,tayi chart ya isheta,saita yanke shawarar ta sameshi tayi masa magana kan komawarta office don tana da buqatar hakan. Sai data idar da sallar magariba yau sannan ta shiga tayi wanka,ta shirya cikin wani cotton material baqi da aka yiwa adon purple wanda yadan ciza,ta gyara gyara gashinta sannan ta feshe jikinta da turaruka yadda ta saba,duk da ko batasaka turaren ba qamshi kayan suke bayarwa na turaren wutar da take turare kayan nata dashi,nan bakin window din dakinta dake fuskantar harabar gidan ta tsaya,ta yaye labulen tana kallon harabar gidan kawai,duk da babu kowa sai mai gadi dake zaune can bakin qofar gidan,amma ko ina gauraye yake da haske tarwai kaman rana,haka gidan yake da wuta 24hrs. Ta jima tsaye tana saqo tana warwara,har ta soma gajiya da tsaiwar ta saki labulen da niyyar komawa ta zauna taji horn,saita tsaya tana ci gaba da kallon qofa sanda baaba ya tura gate din anwar ya sako motarsa cikin gidan,tabi motar da kallo har zuwa harabar da yake ajesu,tana kallo baban ya qarasa bakin motar bayan ya maida qofar ya rufe,ya tsaya daga bakin window din da alama magana suke sannan ya juya ya tafi. Tayi zaton bazai fito daga motar ba jin shuru na wasu mintuna,kana daga bisani taga ya bude murfin motar ya fito,sanye da mens blazzer ruwan blueblack da baqin takalmi sau ciki,yanayin takunsa kawai zai gaya maka a gajiye yake,idanunta akanshi har ya bacewa ganinta sannan ta saki labulen tana sauke ajiyar zuciya,hannunta saman kanta tana son tuna wani abu tana tursasa zuciyarta kan kada ta tuna mata. A qalla sai data bada minti talatin kyawawa sannan ta yafa mayafinta ta fito,sam bata ko sha'awar hawa samansa amma dole ce xata kaita,taso ace yana zama a falo ta cimmasa a can. Yauma da zata gota table din sai data kalla,komai yana nan akai kamar yadda ta dora,saita tabe baki tayi gaba cikin zuciyarta tana cewa "Kai ka jiyo,nidai na sauke haqqina ko". Yana zaune saman kujera one sitter,sanye da boxer da short sleeve shirt farare qal,fitowarsa kenan daga wanka,yayi relaxing bayansa a makarin kujerar,idanunsa na lumshe ya hada yatsun hannanunshi cikin na juna,haka kawai yakejin gidan ya masa shuru tamkar shi kadaine a cikin gidan,yunwa da gajiya suna damunsa,yana buqatar abubuwa da yawa amma ya rasa wanne zai fara tunawa cikin zuciyarsa,cikin haka yaji kaman an buda qofar falonsa,da mamaki ya ware idanunshi da suka dan kada saboda yadda ya jima da rufesu yana kallon qofar,qwarai yayi mamakin ganinta,amma ya shanye mamakin yana ci gaba da dubanta sanda take takowa ciki,bazaiyi qarya ba ta masa kyai cikin yadin jikinta,saiyaji wani bangare daya cunkushe a zuciyarsa yana budewa,tunanin da yakeson yi ya soma dawowa,kwanaki yau kusan goma sha uku kenan bai sanyata a idanunsa ba,ko motsinta bazai iya fadin yaushe rabon daya ji ba,tana sake matsowa qamshin jikinta na shiga ta qofofin hancinsa,qamshin daya sanyashi lumshe idanunsa ya sake budesu a kanta sanda ta samu hannun daya daga cikin kujerun dake can nesa dashi ta dosana ta zauna kan wuta,shuru ya ratsa dakin bayan sallamar data yi na wasu daqiqu sannan tace "Inason magana dakai" idanunshi ya daga ya kalleta na wasu sakanni kafin ya janye duban nashi daga kanta ya maida idanun nasa ya rufe kaman yadda suke dazu,don shine mafita kawai a wajensa "Uhmmm" yace da ita a taqaice "Inason na koma aiki idan Allah ya kaimu ranar monday" da sauri ya bude idanun nasa ya zubesu fes a kanta,saitaji ya mata kwarjini saboda haka ta janye idanunta daga kanshi "Labari kike bani ko umarni?" Ya tambayeta kai tsaye,yanayin tambayar daya mata yasa dole ta kuma kallonshi,tadan sake tsuke fuska "Shaida maka nake"sai ya maida idanun nashi ya rufe sannan yace "Tunda ba umarni bane ba zaki koma ba,kin gama aiki a triple r gem,bama nan ba kawai,kin gama kowanne aiki ako ina idan ba cikin gidan nan ba" haushi takaici da baqinciki suka cikata,me yake nufi kenan?,yana nufin ya rabata da aikinta,cikin hasala tace "Me kakeso kace?,bayan duka qarfa qarfan daka yimin bai isheka ba har saika qara da wannan?,toni ban yarda ba in gaya maka gaskiya,ai bamuyi haka dakai ba" miqewa tayi tsaye ta soma tafiya "Dama na gaya maka ne donkar kazo ka tarar bana nan kace ban shaida maka ba". Tana dab da fita ta tsinceshi a gabanta,suna hada ido ta kauda kai saboda yadda qwayar idanunshi ta sauya launi "Bazan taba lamunta ki fita wani waje mahada jama'a maza da mata ba da sunan aiki,ki gogayya da maza kiyi magana dasu,ki fita da safe ki dawo da yammaci,idan na barki kika koma lallai na tabbata wawa,kuma abinda nayi baiyi riba ba,kina nufin komawa office din danaga wani ya kama yatsarki zai saka miki zobe?,Karki soma gigin aikata kuskure irin wannan,idan ba haka ba zaki gane baki da wayau,idan kuma baki yarda ba bismillah" daga haka ya kauce daga hanya ya bata waje yana komawa mazauninsa,da gudu gudu ta fice daga falon ta soma sauka qasa,tayi nasarar riqe kukanta batayi agabansa ba sai data danga da dakin gadonta,wani irin tuquqi takeji cikin qirjinta da zuciyarta,sam bazata yarda ba,ba zata lamunci ya sake cin galaba a kanta ba bayan wadda yaci,idan yayi haka aiya tauyeta da yawa,tayita zama kenan cikin wannan gidan da zaman cikinsa harya soma gundirarta,zaman da bai mata ma'ana ba sam?,gobe kam saidai ayi duk wadda za'ayi,idan yaso yace ta wuce gidansu. Iska yake furzarwa daga bakinsa mai dumi bayan fitarta yana murza tafin hannunshi kan hannun kujerar da yake kai,yanajin bacin rai nason taso masa yana danneshi,ta yaya zai barta ta koma aiki?,aikin da tun ranar daya ganta cikinsa bai sake samun nutsuwa ba sai daya tabbatar ta daina zuwa ta sanadin aurenshi,randa yaga nuradden din cikin office dinta da qyar ya samu ya saisaita kansa,ji ya dinga yi kaman hawan jininsa zai tashi,sannu sannu ya dinga ambaton sunan Allah har ya samu zafin da yakeji ya sauka,yunwar da yakeji ta dawo masa sabuwa fil,bashi da mafita illa slipper dinshi daya zira ya sauka zuwa qasan. Karon farko da zauna kan dining din,ya jawo warmers din ya soma budewa daya bayan daya,take qamshi ya cika wajen wanda ya qara qaimin yunwar tasa,tun kafin ya soma ci a ido abincin yayi masa,sanda ya soma ci kuwa saiya samu kansa da lumshe idanunsa,dadin girkinta ya ninka fiye da wanda ya sani a baya,a nutse yaci abincin,ya kuma yi qoshin daya manta rabonshi da yayi irinsa,baibat abincinba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96