Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,302 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dama bayan cin abincin dare yana zama ne cikin yaran nashi su taba hira kafin ya tattara ya wuce dakinshi. "Rahama,meye ya faru ranar hutun noor international?" Tambayar da abbun ya jefo mata kenan bayan ta gama dubawa su farouq haddarsu da wajibul manzil da aka basu kan tajwidi,a hankali ta dago idanunta ta dubi abbun,daita sunkui da kanta qasa,tana tuna duk wani cin fuska da anwar yayi mata,tanq tuna kalamanshi akanta daya bayan daya,wani daci na tasowa daga qirjinta zuwa harshenta,saidai ta dake zuciyarta,batason ko daya ta sake zubda qwalla a rayuwarta saboda anwar "Uhmmm..." Abbu ya sake bata dama ganin tayi shuru "Abbu sun koreni ne" "Kora kaman yaya?,me kika musu?,wannan wanne irin cin fuska ne?" Anty zubaida ta fada a hasale,yayin da abbu yayi shuru har sai da anty xubaida takai aya "Dazu gamayyar malaman makarantarku sun sameni har wajen aikina,sun bani haquri kan abinda ya faru,na gaya musu banda masaniyar abinda yafarun,sun bayyanamin cewa mai makarantar ne gaba daya ya sallameki,dukkansu basu da masaniyar ainihn dalilin daya sanya ya koreki ba,duk da kina daya daga cikin haziqan malaman da suke alfahari dasu,idan don kamarace bake daya kika makara a ranar ba,amma suna so na baki haquri in sha Allahu zasu magana dashi master din,kuma sunsan yana da sauqi zai fahimta,to,duka dai sun gama bayanansu,na kuma ari bakinki naci musu albasa cewa kema ba zaki koma ba,idan baki manta ba dama kan yarjejeniya na barki koyarwa a makarantar,yanzu kuma abinda muka gina yarjejeniyar akai ya afku,saboda haka yanxu kinga nayi winning,dole ki karbi duk aikin dana samo miki kenan" ya qarshe yana murmushi,don bashi da ra'ayin tursasa dan adam ne,amma dama tun asali ta yaya shahida me matakin karatun irin wannan zata tsaya koyarwa a primary?,wanne irin maida kai baya ne "In sha Allahu abbu,nima bani da sha'awar komawar har abada" "Shikenam faduwa tazo daidai da zama,Allah yasa hakan shine yafi alkhairi" "Amin abbu na gode" ta furta idanunta har yanzu na kallon qasa,nan ta yimusu saida safe da zummar zata sha magani ta kwanta. Sai data raba dare tana gayawa kanta ya kamata ta motsa gaba,ta watsar da komai,ta ciyar da rayuwarta gaba,ya kamata ta shafe komai kaman yadda take gayawa kanta a 'yan kwanakin nan,idan bata manta ba,idan kuma zata iya tunawa,anwar din data gani dazu da anwar din data gani satin daya gabata ba shine anwar din data sani shekaru goma baya ba,lallai ba shakka bashi bane,ya kamata aga wata shahidan ta daban ba wannan ba "Yes!" Ta fada tana baiwa kanta qwarin gwiwa da tabbacin zata sauya komai. Washe gari da qwarin gwiwarta ta fito,hakanan tayi yaqin maida murmushi da fara'arta gaba daya,koda bata samu duka ba taji a jikinta ta maida kaso hamsin cikin dari,wanka ta soma yi sa'annan ta fito ta shirya cikin kwalliya madaidaiciya a riga da skert na atamfa don kusan tafi son atamfa saboda tana son kaya cottoon kasancewarta mutum da batason zafi,feshe jikinta tayi da turarenta na din din din,ta tsaya gaban mudubi tana kalli kanta,ita kanta tasan tayi kyau,kwalliyar data jima bata bari ta rabi koda fuskarta ba,murmushi ta sakarwa kanta da kanta tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai taji gaba daya hankalinta ya karkata ga aikin da abbun yace zai sama mata,batason ci gaba da zama haka "I need to make my self busy,so i can forget dat am deeply hurt and broke" ta qarshe maganar tana juyawa cikin hanzari ta dauki wayarta ta fice daga dakin. A tunanin anty zubaida zata ganta sukuku ko cikin damuwa saboda maganar jiya amma sai taga sabanin hakan,itama hakan yayi mata dadi sosai,ranar alhamis ce babu islamiyya,haka ta sake sosai cikinsu huda sukayita buga games bayan sun gama karatu,ta kira mutanen data jima bata kirasu ba,ta kira zunnurarta sun jima suna hira,har ita kanta ta dinga tambayarta yau da alama ranar ta musamman ce. Koda noradden yazo shima yazo yau a sa'a,ta tanqwara zuciyarta ta fita ta saurareshi ba tare da wani dogon turanci ba,ba laifi kuma ta dan jima wajensa,don ta dauki mintuna aqalla ashirin abinda bai taba faruwa ba a tarihin zamantakewarsu,ita kanta yau taji zuciyarta sakayau kaman ta rage mata nauyi daga cikin nauye nauyen dake takure da ita. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *ga mai buqatar littafina da zanyi bayan kammala alqawarin Allah,yaje youtube yayi searching SAUTIN HIKIMA,zaiga SUBSCRIBE da jan rubutu ya dannan zai koma black,yayi screenshoot ya turo zuwa ga number da zatazo a qasa,zan sakashi group din da yardar Allah SUBSCRIBW KYAUTA NE BA'A DAUKAN KO SISI* 07038670166 *Alqawarin Allah* 2️⃣0️⃣ Zaune yake shi daya cikin dan qaramkn garden din dake bangare raban na gidan nashi,wanda yasa aka masa shi sannan aka qawata masa,yakan yawaita zama lokaci zuwa lokaci musamman a sanda yake buqatar kebewa ko yin wani gagarumin aiki da bai buqatar surutu ko takura,snye yake da t.shirt mai gajeran hannu gami da trouser light and dark brown,tray ne dan qarami aje a ganshi da butar shayi hadi da qananun kofuna guda biyu akai,daya kofin yana hannunsa,idanunsa zube kan laptop din dake kunne gabanshi tana aiki yana kallon wani aiki daya soma tsarawa,inda yake fidda duk wajajen dake da kura kurai,yayi. Da wani sashen kuma ranshi ke a bace saboda sanarwar da nafisa ta fitar a fashion tv,baisan ya akayi ba sai saqonnin taya murna ya tashi dashi fal email dinshi,watsapp dinshi da twitter,angage din ma da ba'akai ga tabbatar dashi ba. Qarar bude gate din gidan da mai gadi yayi ya shiga kunnuwansa,sai yayi tsai yana sauraro,iyakar saninsa yasan dai ya gaya masa kar yabar kowa ya shigo masa gida idan ba muhsin ba,saboda yana son ya hada hankulanshi waje daya,zuciya da qwaqwalwarsa ta samu cikakken hutu. Ba'a wuce minti biyar cikakke da budewar ba ya juyo taku,kamn ya juya saiya basar yaci gaba da abinda yake,don qamshin turarenta daya rigashi isowa ya gaya mishi ko wacece. Ta dauki minti biyar tana tsaye a bayanshi,hannayenta harde a qirji tana qare masa kalla,ba shakka ta jarabtu da son anwar irin soyayyar da bata tsammaceta ba,har kwanan gobe kuma bata ji a jikinta zahiri da badini ta samu irin soyayyar da take kwadayi daga gareshi,haka ta gaji ta saki hannayenta tana fidda ajiyar zuciya ta taka har inda yake,gabanshi ta zagayo ta tsaya tana dubanshi,fuskarta a narke haka ta karyar da wuyanta,sai daya mula don kanshi sannan ya dago ya mata kallo daya,haka kawai yakeji wasu abubuwa marasa dadi akanta,har yanzu baisan a wanne aji zai sanya nafisan ba,ta kuma qi ta gane taqi ta fuskanceshi "Baki iya sallama ba?" Sai tadan sassauta kwabw fuskar da tayi,tana son ta koyi sallama duk sanda ta iskoshi kaman yadda ta fahimci tsarinsa ne amma takan yawaita mantawa,kuma mima ta gaya mata dole ta siffantu da duk wani yanayi da tasan yana so yana kuma cikin tsarinsa "To salamu alaikum" amsa mata yayi duk da har yanzu bai daga kai ya sake dubanta ba "Ba zakace na xauna ba?" Ta fada cikin shagwaba,ture kofin dake gabansa yayi "Sai nace ma?,ai ga kujera nan kina gani ko?" Kai ta gyada a hankali taja kujarar dake fuskantarsa ta zauna. Hannayenta ta hade waje guda,ta sake sassauta murya "Dear...don Allah

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});