Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 95

Chapter 95

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

riga ka nuna musu bani da mutunci bani da daraja a idanunka! To Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!” Murmushin takaici Dad yayi kafin yace “Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya! Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba, ko kin gaida ni tunda na shigo?” Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace “Kaga Arshaad wuce mu tafi! Zan ga wanda zai hanaka fita yau” Mammy ya kalla, suna had’a ido tace “In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba! Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan to ban yafe maka ba!” Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi. A zafafe Dad ya yunk’ura zai yi magana da sauri Daddy ya katseshi ta hanyar cewa “Dan Allah dan Annabi ka kyaleta, Uwa ba abar wasa bace ba! Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta Dole.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace “Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata tasoba. Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki sannan da ita kanta Hudan, babufa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace kamar azo aurenta a fasa!..” Cikin katseshi Mammy tace “Yi mini shiru Yusuf!” Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yanda ta kirashi . Bata damuba taci gaba “Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu! Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!” Cikin tsiwa da masifa tace “Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita! Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.” A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi. Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi. Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan yace “Rukayya bani da ishashshen lokaci! Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.” Cikin katseshi ido cikin ido ta kalleshi kafin tace “Yahaya! Ko da ace ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa “ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya. Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu. Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito “Wuce mu tafi masallacin” Haka kawai Dad yace mishi daganan kowa ya shiga motarshi sukai gaba. Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace! Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity. Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in. Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in….. A hankali yake driving, babu nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin. Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin! Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce? Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo.. Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu cikin tsananin farin ciki da nishad’i. Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa Kwata kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in! Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace “Aslam dan Allah idan sun zo kace......” “Ku wuce muje mana! Ya naga kun tsaya anan?” Muryar Dad ta katsesu. Kallon Auwal d’in yayi ya kalli Dad sannan yace “Ok” Kawai, ya juya ya yi gaba…. Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarinshine! Tabbas badaban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan! Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma furr! Ta ki yarda, ta nace ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan! He might look calm but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba! Wannan wacce iriyar k’addara ce? Mai yasa yake jin hakan har yanzu? Mai yasa yake jin haka? Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi…..? A hankali yaji Abba yace “Aslam” Firgigit! Haka yayi hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe, da sauri ya ja burki! Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai. A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe.. Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana “Watak’il yau in yi maka laifi! Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido” Da mamaki yake kallonshi zuciyarshi tana dukan uku uku! Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi daga jin furucin Abba na yanzun! Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi. Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga” Yana gama fad’in haka ya wuce ciki. Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal. Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata! Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi amman kuma ba a d’auka! A fili sannan da k’arfi yace “damn it!!” Sannan yayi jifa da wayar tashi wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi…. Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara. A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace “Sorry”. Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!. Ba musu ya mik’a mishi shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure…….. Auwal k’ok’ari

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});