Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai kuma ya fashe da wani irin kuka.. Ba abunda idanunsa suke hararo masa sai irin yanda yaga Mama tana ta k’arewa gidan Abban kallo! Tayaya? How? A haka shi zatayi appreciating d’inshi!? He has been trying his best ya goge Abba a ranta, amman abun yak’i yuwuwa sam ya kasa cireshi a ranta, in dai abu da Abba a ciki to ba zata iya hak’ura ba Duba fa yanda ta shirya mishi k’arya yau ta tafi gidanshi…… Yana wannan tunanin shed’an kuma yana sake rura mishi wutar zarginsu d’in da yake yi ita da Abban A ranshi yake aiyyana “to in ba hakaba in dai ba suna tare ne ba tayaya za su dinga bawa juna mahimmanci haka?” Ya lura da yanda ran Abba ya b’aci matuk’a ranar da yaje gidanshi da y’an sanda a lokacin da ya aibanta Maryam d’in a gaban kowa, aiban ta tan da yayi ne ma Ummul abaisin dalilin da yasanya Abban ya kulle shi…… Ya jima ya na kuka kamar k’aramin Yaro, zuciyar shi ce ta bashi shawarar gwara ya karyar mata zuciya ta hanyar nuna mata Abba fa yayi mata nisa ba zai tab’a dawowa ba! Amman ta yanda zuciyartata za tafi karyewa ta hak’ura shine idan ta saka rai sannan ta samu full hope akan zata samu Abban for the second time sai hakan yak’i yiwuwa ta sake rasa shi! In ta samu wannan disappointment d’in ya san zata ji zafi zuciyarta zata karye kuma tabbas zata cire rai ta hak’ura da Abba ta rungume shi (Baba) a matsayin Masoyi. Da wannan tunanin ya mik’e ya fara dube dube.. Da kyar ya samo takarda, ya yi rubutu ya d’aura mata akan k’irjinta, ya juya ya bud’e k’ofar ya fice ya barta kwance cikin jini cikin mawuyacin hali. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 47 Tun bayan sallar la’asar su Hudan suka fara neman layukan su Mama domin su ji ya suka isa gida. Ummu dai ta d’auka amma Mama har bayan Maghrib bata d’aga ba. Tun suna ganin abun kamar wasa har bayan sallar Isha shiru dan haka Ummu ta yanke shawarar zuwa domin taga ko lafiya saboda Mama ko 2 misscalls bata bari ayi mata take amsa waya........ A hankali take bud’e idanuwanta….dishi dishi ta fara gani kafin ta samu ta d’an fara gani. Gefen fuskar Hudan wadda ke zaune a gefenta ta fara gani ta sharkaf da hawaye, sai kuma cikin fad’a sosai taji Kaka yana cewa “Wallahi tallahi Talatu zan yi mugun b’ata miki rai! Wannan wanne irin rashin tunani ne da son kai? Mutumin da yayi wannan b’arnar shi kike cewa a saka? Reputation d’in yaci k’aniyar sa! Ai babu wani maganar image da reputation shi da kansa ya riga ya lalata kayanshi…” Tana k’ok’arin yin magana ta fara ganin dishi dishi still.. Har ta koma ta sake sumewa babu wanda ma ya san ta farka! Bata farfad’o ba sai washegari da safe, d’akin daga Ummu sai Hudan, Arshaad da Sakina. Sakina ce ta fara lura da ta farka dan haka ta k’arasa da sauri tana cewa “Ummu kinga ta bud’e ido yanzun nan kuma ta sake rufewa”. “Alhamdulillah” Ummun tace sannan ta fita dan zuwa ta kira Likita saboda yace tana farkawa a kirasa. Bayan y’an dube dube ya k’ara mata wasu allurai ta drip sannan yace “su yi k’ok’ari su bata abinci mai kyau, ta ci.” Yana fita Hudan ta k’araso, duk yadda taso ta rik’e hawayenta kasawa tayi dan haka ta fashe da kuka Sakina ma haka, haka itama Ummu wadda ke tsaye a gefe. Arshaad ne yayi k’arfin halin lallashinsu da kyar suka samu suka yi shiru, sannan suka shiga tambayar ta “ya jiki” Fahimtar da Arshaad d’in yayi suna buk’atar space ne ya sa shi yi musu sallama sannan yace “zuwa anjima zai dawo ya tafi dasu, akwai abunda ake buk’ata?” Da “Babu” suka amsa sannan Ummu ta sake yi mishi godiya, ya fita. Yana fita Ummu ta juyo tana kallonta kafin tace “shi ya kawomu nan shekaran jiya.” Da mamaki Mama tace “Shekaran jiya?” Da kyar. Shiruu, Ummu tayi kafin tace “eh! Kwanan ki biyu a nan. A yanayin dana ganki na yi tunanin na rasa ki ne Mama” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka sannan cikin kukan tace “Ban yi tunanin kina da ragowar rayuwa a gaba ba, sannan na san muddin Abba ko Hajiya wani ya ganki a yadda na ganki to ba lalle su iya jura ba tsaf za su iya yanke jiki su fad’i dan ni kaina sai da na zube a wajen, da na ganki. Gashi Baban Sakina baya gari, shiyasa na kira Arshaad wanda shi kuma ashe a lokacin ma su Hudan sun d’agawa Abbansu hankali akan suna so su zo su ganki dan sunyi ta kira bakya d’auka, gashi kuma nima a lokacin sunata sake kirana amma ban d’auka ba! Dan haka suka taho. Banyi 20 minutes da kiransu ba, suka k’araso duk su ukun a hargitse dan a yanda sukaji muryata (lokacin da na kira Arshaad) sun san ba lafiya ba. Shigowar da suka yi ya sanya maimakon a d’auki mara lafiya d’aya sai kuka zama ku biyu! Dan itama Hudan suma tayi, Arshaad ya d’auketa a hanyar fitar da ita suka had’u da Baba! Yana ganin fitarshi ya datsa sakata wai Namiji ba zai sake shigar mishi gida ba! Kuma muka ce masa ya taimaka mu fitar dake ya k’i!. Ba yadda na iya sai su Abba Madun muka kira, abunda muke gudun kuwa sai da ya faru don yanzu haka shima yana kwance tunda ya ganki jininshi ya hau sosai! Don shima yayi tunanin mutuwa kika yi. Amman abu d’aya wanda aka yi yayi mini mugun dad’i shine ‘bayan an kawoki an tabbatar da kina da rai da Kaka da Abba Madu suka je dakansu suka yi arresting Baba! Kuma sun ce basu ga ranar fito da shi ba’.” Cikin kuka Mama tace “ki kira min su Kaka, ina da buk’atar magana da su, Bilkisu na gama auren Ya Usman, wallahi.” Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin ta zaro wata takarda a cikin jakarta, ta mik’a mata...... Wani sanyi ne ya lullub’e Mama, atake taji kamar an yi mata bushara da gidan aljannah! Saki d’aya tak! taga yayi mata “Alhamdulillah” ta hau jerowa wasu hawaye suna gangaro mata….. A hankali Ummu ta dawo ta zauna kusa da ita kafin tace “A ta sanadiyyar dukan da yayi miki! Cikin da ke kanki na san baki san kina d’auke da shi ba ya zube jiya, har an yi miki wankan ciki!”. Mama bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba............. Ta d’an ci abincin kuwa ba laifi. Zazzab’i da zafin ciwukan jikinta especially karayar k’afarta ne suka sanya aka yi mata allurar bacci dan ta samu sa’ida. Sai dare Arshaad yazo, ga mamakin Sakina har da Auwal… Tana d’an murmushi suka shigo amman tunda suka yi ido biyu da Auwal ta had’e rai ta turb’une fuska! Dariya ta bawa Arshaad dan haka suna had’a ido ya hau yi mata dariyar tsokana ai kuwa ta chuno baki gaba ta sake kumbura jira kawai take a tab’ata ta fashe. Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya durk’usa

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});