Chapter 38
Chapter 38
hannunta tana share hawayen duka biyu. Kallonta yayi tukunna yaci gaba “Amman idan kinje, inaso ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan jiraki a mota! Ku gaisa ki dubata daganan kice musu kina zuwa, in kin fito sai mu dawo. And karkice musu ni na kawoki”. Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace “To ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.” Mik’ewa yayi kafin yace “Shine ni kuma zaki yaudareni ki tafi kik’i dawowa ko?” Kuka ta fashe da shi….saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!. A hankali yace “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman inaso ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waenda sukayi nasarar raba ni dake!. Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani. Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamaki, amman Hudan ba zan sake bari kiyi nesa dani ba.. I want to take care of you Make it up to you Make you forget all the sufferings that you go through. Amman hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yanda kike yi mini ba kwata kwata Huda, it’s like kamar ma bakya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki! Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba! Yanzu ma kalli yadda kike yi min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’innan?” Ya k’arashe maganar a hankali. Gaba d’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi, tabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita…. Tunaninta ne ya katse jin yana cewa “I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.” Shiruu, d’akin ya d’auka kafin yaji tace “Tam”. Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita. Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata.. Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping… Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye. Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban yace mata. Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in wajen kala nawa.. Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates. Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci… Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su.. Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka nan suka shigo abunsu ana d’an tab’a hira kowa yana fara’a banda shi. Suna shigowa da Daddy suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu. A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin inda taga sun nufa kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen, Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita. Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku” Aslam ne kawai ya amsa mata, a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma! Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!” A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata. Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace, “Sorry dota mun barki ke kad’ai ko? Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba bazaki ji dad’in zaman ba kwata kwata tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.” Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace “ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take! Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.” Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in! Yana mamakin Auwal!! Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana….. Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa “Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyaleshi.” Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!. Cikin fushi Daddy yace “Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are? Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!” Cikin katseshi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyaleshi kawai! Dan Allah” Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.” A fusace Auwal ya kalleshi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace “Get out akace!! Stupid boy kawai!!!” Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama. Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so ace a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiyasanya yakejin kanshi a sama kamar yafi kowa!. To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i,,kowa da abunda yake damun ranshi. Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala, kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96