Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bud’e yace “How old is she? Hudan?” “Close to 18” ya bashi amsa ba tare da ya fahimci inda tambayoyinshi suka dosa ba. “Kwanaki kace min a gidan Mijin Mamanta take, and ba suyi maka maganar Dad d’inta ba ko?” Cewar Aslam. “Aslam what are u getting out of this ne wai??” Arshaad yayi mishi tambayar. Da d’an fad’a yace mishi “Just answer me!!” Shiruuu, yad’an yi sai kuma yace “Tun farko…da na fara zuwa gidansu ta ce mini ‘Basu ma da number d’insa’ (her Dad) Uncle d’inta kuma yace “families d’inne suka samu matsala shiyasa but ana hoping resolving in shaa Allah.” Aslam, Tafin hannayensa duka biyun aslam ya saka yayi cupping iya daidai hancinshi da bakinshi ya fitar da wani Hucin da sai da na kusa dashi ya juyo yana kallonshi! Tukunna ya cire hannun ya dafa Arshaad kanshi tsaye yace “Hudan is our sister!! Daughter d’in Abba ce, bani da tantanma.” Da kyar Arshaad ya daidaita kanshi daga shock d’in daya shiga, kafin yace “How???” Aslam ya bud’e baki da niyyar bashi amsa kenan! Ya hango shigowar Abba!. Kusan a tare suka ga juna don shima Abban yana shigowa idanunsa suka sauk’a akan Aslam d’in. Da sauri ya k’araso yana cewa “Aslam mai ya faru? kace In baro komai in zo asibiti emergency, duk na rikice, waye ba lafiy........” Maganarshice ta mak’ale sakamokon idanuwanshi da suka sauk’a akan Hudan wadda taketa faman kuka har yanzu….. Shi dai Abba bai san ya akayi ba dan kawai tsintar kanshi yayi a gabanta a tsaye! Ana cewa yana kama da su Aslam da Yaya amman tunda yake bai tab’a ganin kamanninshi da wani mahaluk’i kamar na wannan matashiyar budurwar ba! Dukda fuskarta a yanayin kuka take hakan bai b’oye tsananin kamannin da suke yi da juna ba! Ita kam Huda yanayin tashin hankalin da take ciki ne bai bata daman fahimtar kallon fuskar mutumin ba, amman tabbas tun lokacin da yazo gabanta ya tsaya taji wani bak’on al’amari ya shige ta! Tsintar kanta tayi da mik’ewa tana goge hawayen ta sannan ta shiga gaidashi……. Aslam bai bashi damar amsawa ba yace “ya biyo shi, yana so zai nuna mishi Mahaifiyar Yarinyar daga nan sai ya yanke hukunci da kanshi.” Haka nan kawai Abba ya bi bayan Aslam kamar rak’umi da akala! Bayan aslam d’in ya cewa Huda itama ta biyosu! Arshadd ka bashi da wani zab’in da ya wuce ya bisu. A haka suka d’unguma Inda aka kwantar da Mama ake duba ta…suka tsaya suna jiran fitowar Doctor! Kusan wajen 29 minutes ba wanda yace komai kowa ka gani da abunda yake yawo a kanshi… Suna a haka Doctor ya fito! Kallonsu yayi one by one kafin ya k’arasa inda Aslam yake tukunna ya fara magana “Alhamdulillah An ci sa a ta farfad’o! Za ku iya shiga ku ganta amman dan Allah kar kuyi hayaniya kuma kuyi k’ok’arin kwantar mata da hankali saboda jininta ba k’aramin hawa yayi ba!.” Yana gama fad’an haka ya mik’awa Hudan takardun hannunshi ya wuce. Abba bai san daliliba bai kuma san wacece a kwance a d’akin ba, amman yadda zuciyarshi take bugawa da kuma kalar karkarwa da jikinshi ya d’auka lokaci guda ne ya sake d’aure mishi kai! Dan tabbas ya san in da ace za a auna jininshi a yanzu To da za aga yafi na mara lafiyar da ake cewa su taru sun kwantarwa da hankali hawa… Muryar Aslam ce ta katse mishi tunani jin yana cewa “Muje Abba. Bismillah.” D’aga kai kawai yayi alamar ‘to’ sannan ya nufi inda yaga su Hudan da Arshaad sun shiga, Aslam ya mara mishi baya…. ...Shekaru goma sha takwas rabon shi da ita, amman ba a yanayin rashin lafiya ba ko a garin makafi idan ya had’u da Maryam ya shafa yaji to sai ya gane ta! Lokaci guda yayi baya luu!! Ba daban Aslam yayi saurin taro shi ba tabbas da sai ya zube a k’asa! A b’angaren Mama kuwa! Da farko da ya shigo ta ganshi ta d’auka gizo yake yi mata, sai da taga har Aslam ya taro shi yana cewa “Be careful” tukunna ta tabbatar da cewa shi d’in ne! “Mai ya kawo shi? Me yake nema? Me zai ce mata?” Sune tambayoyin da suka taru suka had’e da al’ajabi suka fara k’ok’arin tarwatsa mata zuciya! Da kyar ta k’ok’arta ta tashi ta zauna sai kuma ta fara k’ok’arin tsayuwa. Da kyar ya iya dedeta kanshi sannan ya sake sauk’e idanuwanshi a kanta… Babu abunda ta k’ara ko ta rage, tananan kamar yadda ya santa 18 years ago! fatarta ce kawai ta d’anyi duhu amma kyawunta da yanayin jikinta ba abunda ya ragu ko ya k’aru! “Astaghfirullah!!” Yayi saurin furta hakan, sakamokon tunawa da yayi ita d’in a yanzu mallakin wani ce! Sai kuma lokaci guda ya fara ganin duhu duhu sakamokon kishin da ya turnuk’e sa! Bai tashi dawowa dai dai ba sai da yaji Hudan da Arshaad suna tambayar ta “Ina zata je?” Ba tare da ta kalle su ba tace “Gida!!” Sannan ta sa hannu d’ayan hannunta ta cisge cannular k’arin ruwan da aka d’aura mata a d’ayan hannu nata, tayi hanyar fita (inda su Abba suke tsaye!). Da sauri ya tsaya a gabanta ya fara magana “M mm Maryam Doc ya c ce jji kin kk ki ba kwari kark.......” Mahaukacin Marin data d’auke sa da shi ne ya sanya hatta su Aslam sai da suka d’auke wuta na y’an sakanni! Cikin b’acin rai tace “That’s for Huda!! Na duk wani kuka da bak’in cikin da ta fuskanta ata dalilin hukunci daka yanke tun kafin rayuwarta ta soma!” Bana so ta san ka! Bana so taji komai!! Bana so ta san komai!!! Ba ma buk’atar ka!!!! na rok’eka da girman Allah ka bar nan tun kafin raina ya k’arasa baci!” Ta k’arashe maganar cikin b’acin rai da k’unar zuciya, wasu zafafan hawaye suna zubo mata. Idan lissafinshi ya bashi dai dai to maganganun Maryam suna nuni ne da irin kalaman da ya kamata a yiwa uban da ya gudu ya bar y’arsa…… Bai damu ba sam! Dan bata k’umbiya k’umbiyar magana yake ba a halin yanzu…shi daman ko da ace ya tambaya ance mishi Yarinyar ba y’arsa bace ba to fa ba zai tab’a yarda ba!! Ballantana kuma yanzu da maganganun Maryam suka sake tabbatar mishi da ‘y’ar’ tasu ce!. Hakan yasa ba tare da yabi takan Mama wadda Aslam yake ta rok’o ta koma a saka mata cannula tak’i ba! (Ta nace akan sai dai Abba ya fita ko kuma ita a tafi) Ya nufi inda y’arsa take tsaye! Yana zuwa bai yi wata wata ba kawai ya rungume ta sai kuma ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro. Ita dai Hudan zuwa yanzu ta koma mutum mutumi! Dan kwakwalwarta ta kasa aminta da amsar da kalaman Mama da kuma reaction d’in wannan bawan Allah suke bata. Shigowar Likita ce ya juyo da hankalin su gaba d’aya, dan hayaniyar su ta fara damun ragowan patients d’in da suke gefen su… Dukda inda suke an yankashi da girma sosai dan yayi biyun ragowar inda patients d’in suke amman dole in sunyi magana za a jisu kasancewar labulaye ne kawai ake sakawa a tsakani. Da mamaki

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});