Chapter 36
Chapter 36
alak’a da shi ba? Eh? Kika barni a duhu?” Cikin rashin fahimta tace “Wallahi ni ban gane komai ba! Dan Allah ka fahimci ni”. Shiruuu, Auwal yayi yana d’an nazartarta yana kallonta.. Chaaan! Kuma yayi tsaki kafin yace “kije ki tattaro kayan ki, ki wuce wajen Gwaggo Asabe, i’ll get back to you, idan kuma zaki zauna anan d’in ne to zan iya barinki but ki tuna abunda na fad’a miki d’azu!”. Da sauri ta nufi d’akin ta na sama, kafin minti goma ta tattaro komai… Auwal ji yake kamar ya shak’e ta yayi ta dukanta! Kawai dai ya barta ne ya samu ta rabu dashi for now dan bayaso Daddy yazo kiranshi da kansa! Amman tabbas sai ya koya mata hankali, dukda ya fahimci kamar jahilcinta da dak’ik’ancinta ne ya janyo komai.................. A gate d’in estate ta had’u da su duk sun fito har Gramma wadda ta kawo su Shuraim don tun jiya da suka k’i bacci da safe kuma suka dinga yiwa Abba kuka akan suna son Ummi ta dawo, ya kaisu wajenta. Da kyar ta lallab’asu bayan tace musu “Ummin tayi y’ar tafiya ne amman soon za su dawo, suyi hak’uri.” Hudan tana k’arasowa Gramma ta kamo ta, tace “Ki kwantar da hankalinki Ki bisu kinji, na san kina kewar Maman ki, amman na san Abba da kansa zai kaiki idan komai ya gama daidaituwa, kinji y’ar albarka?”. Anhankali ta d’aga mata kai tanajin k’aunar matar da girman ta suna ratsa zuciyarta. Dad shima abunda ya fad’a mata kenan sannan yace “duk abinda take buk’ata idan sunje ta rubuta ta bawa Arshaad ya kawo mishi,,already anyi mata d’an siyayyan abubuwan da zata buk’ata for now suna cikin mota.” Da “to” da kuma godiya shima ta amsa mishi. Auwal yana fitowa daga mik’a Jalila wajen Gwaggo Asabe suka fara shirin tafiya… Abba ne ya bud’e mata gaban wata mota yace ta shiga, tana shirin shiga dai dai nan Gwaggo Asabe wadda ta fito yanzu ta k’araso taja Hudan tayi hugging d’inta, ji suke kamar kar su rabu dan har sun saba a cikin y’an wuni biyun da suka yi tare. Auwal yana gefe in banda tab’e baki babu abunda yake yi, ji yake kamar yaje ya shak’e ta! Shi fa ya tsani yaga ana fifita wani, kuma ya lura kamar hakan a jinin y’an gidan yake! k’iri k’iri sun iya nuna banbanci…..gashi yanzu ma akan y’ar k’ank’anuwar Yarinya an kwashe Surukan gida kaf! An kai cell, an bar mahaukaciya!…. Ya ja tsaki yafi a k’irga k’arshema mota ya shige yana ta mita a ranshi yana cewa “Kamar duk ba a tsatso d’aya muka fito ba!” Mu an maida mu kamar wani bole especially ma ni….kowa idan ya tashi k’orafi sai kaji yace ‘Auwal’.” Shi kad’ai haka yayi ta mita yana ta faman kumbure kumbure.. Su kam bama su san yana yi ba. Sallama suka yiwa juna kafin Gramma ta ruk’o hannunta (Hudan) da kanta ta saka ta a mota ta juyo. Daurewa kawai take yi, amman Abba yana zuwa da yayi hugging d’inta sai ta kasa ci gaba da daurewa ta fara hawaye. Da kyar suka lallasheta sannan suka maidata gida, suka fito, suka kama hanya ba dan ransu yanaso ba, suka fice a estate d’in suna masu jin dumbin kewar gida cike a zuk’atansu. Suna fita suka had’u da motar Kaka da Madu, horn suka d’anyi musu don haka suka dakata! Dan shi Abba bai ma gane su ba. A D’an gaba kad’an suka yi parkin, dan haka suma su Kaka suka juyo da akalar motar tasu suka isa inda suke suka yi parking…. Suna fitowa Abba ya ganesu dan haka ya k’arasa ya cewa su Aslam su zauna a motar, shi da Dad kuma suka fita suka samesu. Suna wucewa itama Hudan ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar amman sai ta jita a rufe! Cikin d’an tsare gida tace “zan je wajen Kakannina!” A k’ufule yace “Baza ki ba!” Wani takaicine ya rufe ta taji kamar ta rufeshi da duka, taya ga su Kaka tana kallo suna kallonta, amman ace ba zata je wajensu ba? Inaaa, ba zai yiu ba! Dan haka ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar ta k’arfi! Tun k’arfinta. Ta gefen ido yake kallonta, tanata dambe da handle d’in motar, tun k’arfin ta. Ta fi minti biyar tana fama ganin ta kasa yasa ta juyo da d’an ladabi tace “Ya Aslam dan Allah ka bud’e inje wajen su mana.” Ta bashi dariya sosai amman ya danne, still amsar d’azu ya sake maimaita mata babu alamun wasa a fuskarshi “Baza ki ba!” Wani k’ululun takaici ne ya tokare mak’ogwaronta, dama ga haushin Arshaad da take ji tun d’azu! (Don Abba har yana shirin shiga motar da take amman ya janyeshi yace “yazo zai tuk’a shi”) Yanzu gashi ya had’ata da wannan boss d’in! Shi bai bari ta tafi da Abba ba kuma shi ma ya kasa shigowa su tafi tare ko dayake ta san saboda yana jin kunyar had’a ido da ita ne shiyasa! Kuma ya san koda ya shigo d’in ma fita zata yi ta bar mishi motar dan haka d’in ta gama shiryawa a ranta. Amman kuma at least ai da ya gwada Insted yana kallonta amman ya shige motar Abba yaja suka tafi da shi da su Shuraim.. .....Abunda Huda bata sani ba shi kuwa Arshaad fushi ya d’auka da ita bana wasa ba ata dalilin zargin da tayi mishi!. Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba! A tunanin ta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi. Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da yayi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo waenda suka tsaye a setin su.. Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a! Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.” A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba! Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?” Abba ya k’ule! A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!. Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan bayason yayi musu rashin kunya. Daddy ne ya tabbatar musu da “sunje har unguwar da Hudan ta taso kuma sunji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu saniba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!” Yace musu “Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96