Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

So Da Buri Book 2 Complete Hausa Novel – The Secret That Changed Everything 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya shagala da kallonta, har wani lumshe ido yake yi yana bud’ewa. Jikinta ne ya bata kamar ana kallonta, sai kuma mayen k’amshin turarenshi da ta fara ji a jikin shi tun ranar farko ya daki hancinta! Dan haka da sauri ta d’ago ta kalli dining d’in.. Suna had’a ido yayi saurin rintse idanuwanshi kafin a hankali ya bud’e su a kanta! Doguwar riga ce a jikinta Ashape y’ar kanti bak’a mai ratsi ratsin sky blue sai d’ankwalinta wanda tayi simple d’auri da shi.. Rigar bata wani kamata ba, amman kasancewarta mai garin jiki yasa ta d’an fiddo mata surar jikinta kad’an!. Ranta ne ya b’aci ganin yanda yake wani rufe ido yana sake bud’ewa yana k’are mata kallo! Da sauri ta sa hannu ta warware d’ankwalinta ta yafa a jikinta sannan ta doka wani uban tsaki, wanda yayi sanadiyyar dawo dashi cikin parlourn. Har ga Allah abinda take tunani ma shi Allah bai bashi ikon lura da nan d’in ba, kawai shi dai yasan ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki da shauk’i na daban, sannan yanda ta yi d’aurin ya sake fito da ainahin kyauwun fuskarta dan yawanci cikin hijabi yake ganinta, ga wani lallausan saje dake shirin had’ewa da gashin girarta, na gefen kunnenta ma ya sauk’a sosai kamar zai had’e da gashin k’eyarta, sannan tunda yake bai tab’a ganinta tana murmushi irin yau ba! Bai ida dawowa dede ba yaga ta juya da sauri zata bar wajen. Da sauri ya mik’e ya k’arasa ya sha gabanta kafin yace “Sakina, please, listen to me dan Allah.” Wani kallon tsana tayi masa kafin tace “mallan dalla matsa In wuce” Tayi maganar babu alamun wasa a tare da ita…. Zagayeshi take k’ok’arin yi amman yak’i ya bata damar yin hakan, da alamun ma in ta biyeshi to a yadda yakesa hannayenshi wajen k’ok’arin kareta daga wucewa tsaf zai tab’ata! Don haka ta tsaya ta fara aika mishi da harara kafin tace “Malan ni ba Jalila bace ba! Ka bar ganin wai a gidanku nake wallahi Idan baka bani hanya na wuce ba, zan zabga maka mari!” Ga mamakinta sai taga yana dariya, sai da yayi mai isarshi sannan yace “Na yarda! But duk mari d’aya zaki bani 10 minutes d’inki, kawai ko d’an hira ne muyi…..tbh i can do anything to get your attention” Ya k’are maganan yana kallonta da murmushi akan fuskanshi sannan ya d’anyi k’asa da kanshi….. Yanayin zanen flower d’in da aka yi na sky blue akan kayan jikinta yayi mishi kyau sosai! Zanen ya bi da kallo, har ya sauk’e idanunsa akan yatsun k’afarta! , Gaba d’aya ya shagala da kallo yaga ta janye da sauri cikin b’acin rai tace “D’an iska kawai!!” k’asa k’asa, ita kanta bata yi tunanin zai ji ba, sannan tayi sauri ta nufi d’akin da ke kusa kusa, tana shiga ta datse k’ofar ganin yana shirin biyo ta. Tunda Auwal yake a rayuwar shi, har snake friends d’insa wani lokacin suke kiranshi da shi, ko master, ko danger sunaye dai na rashin d’a’a kala kala but bai tab’a jin ba dad’i ba! Amman yau da Sakina tayi mishi wannan kallon har ta furta, gaba d’aya duk sai yaji babu dad’i! He hates it. Kasa ci gaba da lunch d’inma yayi don haka ya mi’ke ya fita ya koma office da tunani barkatai a ranshi! He just wants to talk to her, yana so ya sake ganin smile d’in nan nata! D’an 5 minutes d’in da suka yi shi da ita d’azu tare zai iya cewa ‘it one of the best moment of his life.......’ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 46 BAYAN WASU Y’AN KWANAKI. Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram!Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi. Gaba d’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip. Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci. Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yanda bata iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gaba daya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii! Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya. A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani. Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance! Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace “Ta tsaneshi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba! Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi….” To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba. Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu..gaba d’aya duk ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi….. Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau through out batayi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”. Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi, dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai! A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa. Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!. A chan suka tarar da Aslam da Arshaad… Basu samu Daddy a wajen dining d’inba amman an kammala jera komai. Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimakeshi babu kowa a wajen. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman…. Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda itafa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal! Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings.. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo yaci” Murmushi Aslam yayi, Abba kuma yace “gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});