Chapter 4
Chapter 4
kika yi ta aika mishi da threats kala kala ba?” Shigowar Doc ce ta katsewa Arshaad maganar da yake shirin yiwa Aslam akan attitude d’inshi towards Mama!! He’s is not like this kwata kwata, he wonders why yake yiwa Maman haka. Ba tare da Likitan yace “k’ala ba ya juya ya fita, ko minti d’aya bai yi ba ya dawo da takardar sallama ya bawa Aslam sannan yace “Kuje gida kuyi solving issue d’inku, dan har ga Allah kun hana marasa lafiya sukuni!! Ba sai kun rufe file ba, zaku iya tafiya kawai…” Yana gama fad’an haka ya kama hannun Mama ya cire mata cannular yana cewa “kuna gama cases d’inku ki tafi asibiti, dan ina jin tsoron jikin nan naki a haka!.” Yana fita Mama wadda daman abunda takeso kenan, ta yafa mayafinta, sannan ta cewa Huda “wuce mu tafi!” ………. Kasa sauk’e kafarta data d’aga da niyyar tafiya tayi jin Abba yana cewa “Babu inda Huda zata bii ki!!” Da mamaki ta juyo tana kallon Abba kafin tace “Ban gane ba!” “Babu inda zata je, tare da ke!!” Abban ya fad’a yana mai k’arasowa inda take sannan ya zuba mata idanuwanshi da ta kasa jurewa kalla tayi saurin yin k’asa da kanta. Cikin tattaro dukkan ragowar k’arfin jiki kuzari da jarumtar ta, ta zagayeshi taje inda Hudan take ta fara k’ok’arin kama hannunta amman kafin tayi hakan tuni Aslam ya juyo da sauri ya rigata, sannan ya tura Hudan bayansa, shi ya zamana yana a gaban Maman!! Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi da ya runtse!! Tun lokacin da ya rik’e hannun Hudan ya zubasu a kan Mama! Cikin wata iriyar kasala data dirar masa lokaci guda yace “You have to pass through me first!” Arshaad kam zuwa yanzu ya zo wuya!!! Dan haka cikin fushi ya kalli Aslam d’in yace mishi “Let her go!!” “No” Yace ba tare da ya kalleshi ba! Sannan ya dakawa Hudan wadda take ta k’ok’arin kwace hannunta tana kuka tsawa “Ki nutsu!!”. Wani irin irin kuka Mama ta fashe da shi a take ta durk’ushe a wajen abin tausayi. Abba ne ya umarci Aslam da “Ya kai Hudan mota dan in dai yaci gaba da ganin Maryam a haka tou za a samu matsala!” Da sauri Arshaad yace “babu fa inda zata je ba tare da Mahaifiyarta ba!!! Haba Abba! Ka san kuwa shak’uwar dake a tsakanin y’a da uwa?? Ka san abubuwan da suka yi going through tare, lokaci d’aya kawai kazo kace zaka d’auketa haka nan? Why are you trying to be selfish???” Kallonshi Abban yayi da idanunsa da suka fara rinewa…. He‘s tired so tired of everything!! A yanzu yadda yake jin zuciyar shi tabbas idan ya tsaya kula Arshaad to zai iya yi mishi illa!! So yake yi kawai ya isa gida tare da Huda ya fuskanci kowa da komai! Masu laifi kuma ya hukuntasu dan bashi da tantamar cewa akwai waenda suka san da zaman Huda a dunyia a cikin estate d’in su… Apart from that ma inda ace ya san yanada y’a tun farko to da ko kwana d’aya ba zai barta tayi a gidan Usman ba which definitely ya san anan take da zama… Tabbas ya san bai kyautawa Maryam ba, but she’s not ready to listen!! Baya jin kuma zata yarda ta bashi Huda a cikin sauk’i! Shi kuma a halin yanzu ya kai peak!! Edge!!Limit!! Na tolerance… So yake kawai ya isa gida. Shiyasa cikin k’ok’arin danne zuciyar shi da yake ji tazo masa iya wuya!!! Ya cewa Aslam “Kai ta mota!! Idan tayi tirjiya ka d’auketa!” Yayi maganar ba tare da ya d’auke idanunsa da suka koma tamkar garwashin wuta daga kan Arshaad ba! Yace masa “Do your best ka lallashi Maryam sannan ka maidata gida.” Yana gama fad’an haka ya juya ya bi bayan su Aslam da Huda wadda ta bisa salin alin dan , gani tayi ana cewa ‘ya d’auketa’ ya durk’usa ya fara k’ok’arin ciccib’arta…. Amman fa kukan da take yi still tana k’ok’arin zame hannunta ana Aslam ya sanya gaba d’aya hankalin duk mutanen da suka wuce ta gabansu ya dawo kansu, da yawa tunanin su rasuwa aka yi mata, shiyasa ba wanda yayi k’ok’arin tsaidasu! Sai dai ‘Allah ya ji k’an rai’ kawai da wasu mutanen suka dinga cewa Wasu kuma kallon tausayi suka bisu dashi. Aslam yana isa bakin motar yaiyi mata key ya bud’e ya dannata a ciki ya rufe sannan ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya bata wuta, ba tare da ya jira Abba ko Arshaad ba ya d’auki hanyar MT estate da ita........ Arshaad gaba d’aya ya tsorata da ganin yanayin Abba Dan tabbas bai tab’a ganinshi a irin wannan yanayin ba! Duk inda bacin rai ya kai b’acin rai to yau ya hango shi a kwayar idanun Abba! Shiyasa ya kasa tsaidashi. A hankali bayan fitar shi yaje inda Mama ke durk’ushe tanata faman kuka shima ya durk’usa gaba d’aya ranshi ba dad’i! A hankali yace “Mama dan Allah k.....” Kallon da ta d’ago tana yi mishi ne ya sa ya had’iye ragowar maganar sa! A hankali ta mik’e ta gyara mayafin jikinta sannan tace “Arshaad mai yasa kayi mana haka?” Da mamaki yake kallon ta kafin yace “Mama ni kuma mai nayi?” So da Buri Free Book 39 Da sauri Sakina tace “Mamaa” sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tattab’a ta, ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita! “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare, dan a yadda Sakina ta juyo da ita haka ta biyo hannun Sakinan ta taho yuuu ta zube wanwar kwanciyar rigingine. Ummu mutuwar tsaye tayi a wajen, so take ta k’arasa inda suke amman ta gagara sakamokon ganin y’ar uwartata da tayi kwance tamkar gawa! Ta kasa tab’uka komai banda hawaye ba abunda take yi. Sakina wadda ta rikice tanata tattab’a Maman ne ta juyo tace “Ummu ki zo ki kamata mu mik’ata emergency.. Mama ce amman bata numfashi.” Jin hakan ba k’aramin sake rikita Ummu yayi ba, ita dai kawai ta ganta a gabansu a tsaye amman bata san ya aka yi ta isa wajen ba. Matar nan ce ta matso itama ta hau jijjiga Mama tana cewa “kumafa yanzun nan muka gama magana da ita, tun jiya muke nan tare da ita. In banda kuka ba abunda take yi, nayi tambayar duniyar nan tak’i kulani… Sai dai kawai taje tayo alwala tazo tayi ta sallah. Sai d’azu ne da naga kamar batta lafiya nace ‘tazo muje in rakata taga Likita’, shine na samu ta d’an kulani ta inda take ce min ‘bara ta d’an yi bacci, idan ta farka sai muje’.” Ita dai Sakina cicib’arta ta fara k’ok’arin yi hakan yasa suma suka sa hannu suka taimaka mata suka yi waje da ita..... Su Madu suna tsaye a k’ofar shiga emergency.. Kana ganinsu ka san hankalinsu ba a jikinshi yake ba! Ga tsananin gajiyar da suke tare da ita Dan ma Allah ya taimaka Abokin Junaidu ne ya biya musu kud’in jirgi su kuma suka biyawa Baba Saboda yaga yanayin tsufansu gashi da ya kira Baban ma a hanya ya jisu suna dawowa daga wata tafiyar…. Ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96